DUK WANDA YA SAYI RARIYA

Ina zaton idan na yi ta mahaukaci nace duk duniya babu wata kasa ko al’umma wadda ba ta dauki ran dan adam a bakin komai ba kamar Nigeria za’a iya yarda da ni ko da ban bada wata hujja ba. Amma dai ya kamata komai zaka fada ka kawo hujjoji.

A tunani na, babban dalilin da ya sa kasar nan take cikin bala’in da take ciki shine jinin mutane da ake zubdawa ba tare da cewa yan kasar ko hukumominta su damu ba. Duk wata al’umma da ta san abinda ta ke yi hatta dabbobi ta na tashi tsayin daka wajen ganin ta kare rayukansu. Amma mu a Nigeria babu wani rai da yake da cikakken tsaro kuma idan aka kashe shi an kashe banza ko wanene don babu abinda za’a yi. Kwarai kuwa domin a kasar nan ne a bainar jama’a aka yi sanadiyar daya daga cikin gwarazan yan siyasa da basa tsoron kowa, wato Chuba Okadigbo amma babu abinda aka yi. Sannan an kashe ministan shari’a Bola Ige, kuma wanda ake zargi da hannu, Omisore, yana kurkuku aka zabe shi zuwa majilisar dattawa. Don Allah a wace kasar duniya ce za’a zabi wanda yake tsare a kurkuku kan tuhumar kisa?

A baya bayan nan, saboda ya fara yawo yana gaya wa mutane zai tsaya takarar shugaban kasa kuma yana da goyon bayan tsohon shugaban kasa  marigayi Yar Adua, an kai wa Abubakar Rimi hari ta hanyar shafa masa guba yayin da maharansa a sigar yan fashi su ka yi, wadda ta yi sanadiyyar rasuwarsa. Makiyan kasar sun tabbatar da goyon bayan yar Adua babu abinda zai hana Rimi darewa shugabancin kasar nan kuma hakan babbar barazana ce gare su don haka suka hallaka shi.

A yan kwanankin nan mun ga yadda yan Boko Haram ke kashe-kashe kuma har ta kai ita kanta hukumar tsaron yan sanda da za ta kare mutane ba ta tsira ba, domin bayan far ma police stations har ita hedikwatar yan sandan aka hara da mummunan bom.

Tambaya ta a nan ita ce, idan har Chuba Okadigbo, Bola Ige da Abubakar Rimi za’a iya kashe su kuma babu abinda ya biyo bayan kisan nasu, sannan kuma su masu alhakin kare rayuka da dukiyoyi, wato yan sanda basu tsira ba, don Allah ran waye zai iya tsira? Kwanan nan shugaban kasa Jonathan ya bamu amsa inda ya ke cewa babu wadda yake da cikakken tsaro a kasar nan.

Abinda ya jawo wannan hali da muke ciki baka iya kauce dora laifin a kan tsoffin shugabannin kasar nan, wato Obasanjo da yar Adua. Dalilina shine daga hawan Obasanjo an kashe yan kasa dubbai a rikice-rikice daban daban amma babu wani mutum guda da aka kama aka hukunta. Shi kuma Yar’adua a lokacinsa aka yi wa yan boko haram kisan gilla kuma duk mai imani idan ya ga yadda akai kashe-kashen dole hankalinsa ya tashi. Kasashen duniya sun yi ta maganganu amma babu abinda wannan gwamnati ta yi. Marubuta daga kowanne sashe na kasar nan ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba sun yi ta cece-kuce da Allah wadai amma hukumomi su ka yi biris. Sakamakon wannan biris shi ya haifar da fitinar Boko Haram a yau.

A gaskiya kasancewar zukatanmu sun gama gurbacewa babu wanda yake damuwa da ran wani, idan har shi ya tsira, kuma hakan ya sa duk wata albarka da Allah yayi mana mun kasa mora sai bala’o’i da muke ta tura kanmu a ciki. Ran mutum ya fi kowanne abu daraja, kuma ko wanne irin mutum ba sai dan kabilarka ko addininka ba, matukar bamu dauki wannnan mun cusa cikin rayuwarmu ba, wallahi ba zamu sami sauki ba.

Wani sabon bala’in da ke neman kunno kai shine maganar da Gwamnoni suka yi a taron su na makon da ya gabata, wato suna kiran gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur domin su sami sukunin biyan mafi karancin albashi na dubu goma sha takwas. Ya ilahi wace irin kasa ce wannan? Mutanen da talakawa suka zaba domin su kyautata rayuwarsu, amma tashin farko shine su lalubo hanya da zata gallaza wa wadannan da suka zabe su. Kada Gwamnoni su manta cewa Nigeria na da mutane kimanin miliyan 120 wanda a cikinsu, kasa da kashi 7 ne kacal ke aikin gwamnati. Idan domin suna neman kudin da zasu biya bukatun kasha 7 cikin dari na mutanen kasar nan, sauran kasha 93 ba yan Ngeria ba ne?

Kafin a yi zabe, marubuta iri na mun yi ta kai gwauro da mari wajen nuna way an Nigeria, musamman yan adawa da su dinke waje guda domin ganin a kori annobar PDP daga mulki amma su ka yi biris, su kuma talakawa saboda rashin sanin me ke masu ciwo su ka sake zabar wa kansu azabar PDP. A nan kana iya cewa Allah ya kara, ko kuwa?

Kowa ya kwana da sanin cewa Gwamnoni da sauran mahukunta babu maganar kyautatawa talaka cikin ajandojinsu domin idan bah aka yaya ma zasu nemi a cire tallafi a wannan lokaci. Hikimar su it ace, tunda dai majalisa ta tabbatar da kudurin mafi karancin albashia dubu 18 kuma shugaban kasa ya saka hannu babu yadda za’a yi su ki biya. Mafi yawancin jihohin ko in ce dukkan jihohi banda Lagos babu wadda zata iya biyan albashin ma’aikatanta daga kudin shiga da take samar wa kanta. Alal misali ka dauki Jihar Kano wadda take bin Lagos a harkokin cinikayya bata iya tara abinda ya kai Biliyan daya a wata (Lagos na samar da kimanin Biliyan 7 duk wata banda tallafin tarayya). Don haka jihohin mu basu da wani banbanci da almajirai da muke da su a kasar nan suna barace-barace. Idan basu nemi kari kudi ta wannan hanya ba, ina zasu sami kudaden da za’a sace? Ayyuka dai dama ba yin su ake ba. Sabon gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya sanar cewa a cikin shekaru 2 kacal, ofishin mai ba gwamna shekarau shawara a kan ayyuka na musamman ya karbi biliyan 6. Don Allah ka gaya min wata hukuma a jiha wadda za’a bata wadannan kudade bata cimma murdun ayyukan da take so aiwatarwa ba a shekara biyu.

A takaice dai wannan hanya da gwamnoni suka dauka wallahi zata haifar da bala’in da sai ya cisu. Domin muna gani yadda talauci yayi kamari a kasar nan musamman a yankinnan na arewa, idan ya ta’azzara za’a bude wata kofa wadda yan boko haram zasu sami sabbin sojoji.

Ina mafita? Gwamnoni su sani cewa sun a da mafita. Bari na bada missali da Kano; a yanzu muna da yan acaba kimanin miliyan biyu a fadin jihar kano banda yan bus da yan tasi. Idan kamar yadda sabuwar gwamnati ke shiri ya tabbata suka saka musu haraji na naira 20 kacal wanda kowa zai iya biya ba tare da matsuwa ba, za’a rika tara Naira miliyan 40 a kowacce rana, wato kimanin Biliyan daya da digo biyu duk wata. Sannan akwai masu kananan sana’o’i sama da miliyan uku, idan ka saka musu naira goma a kullum zasu samar da kimanin miliyan 900. A wannan bangare kawai an samar da biliyan biyu, wato fiye da rabin albashin ma’aikatan jihar Kano. A kwai manyan yan kasuwa da kamfanoni, akwai tasoshi, akwai hanyoyin haraji na karya dokokin hanya da aje ababen hawa. Idan ka dauki manyan titunan kano ka bawa masu lura da titunan kuma suna karbar harajin karya dokoki, miliyan nawa zaka samu.

Gwamnati na iya samar da kudaden rance ga manoma su sayi iri da taki su yi noma, amma maimakon su biya da kudi sai gwamnati ta karbi amfanin gonar don adanawa ko sayar wa a kasashen waje. Wannan hanya ba karamin samar da guraben ayyuka zata yi ba da habaka tattalin arziki.

Idan gwamnoni da gaske su ke yi, me zai hana su fara daga kansu. Nawa suke karba a kullum wajen tafiye-tafiye, abinci da abin shaye shaye? Ba wani gwamna talaka, don me zai daka wa kudin talakawa wawa? A kano an kashe naira biliyan hudu wajen saukar baki a gwamnatin shekarau, don me ba za’a kashe miliyan dari biyar a yi wajen saukar baki na gwamnati ba wanda zai zama dindindin?

A karshe ina kira don Allah gwamnoni su tashi tsaye wajen kawo canji a kasar nan, domin babu wanda zai iya yin haka kamar su saboda sun fi kowa karfi kuma su ne kai tsaye kan rayuwar jama’a. Idan kuma sun ki, to sai ince yan Nigeria su suka jawa kansu domin wanda duk ya sayi rariya…ya san zata zubar da ruwa.

Comments

Popular posts from this blog

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

ALAMUN TSINUWA...

SARKIN KANO DA GWANINTAR IYA SUKA