Posts

DUK WANDA YA SAYI RARIYA

Image
Ina zaton idan na yi ta mahaukaci nace duk duniya babu wata kasa ko al’umma wadda ba ta dauki ran dan adam a bakin komai ba kamar Nigeria za’a iya yarda da ni ko da ban bada wata hujja ba. Amma dai ya kamata komai zaka fada ka kawo hujjoji. A tunani na, babban dalilin da ya sa kasar nan take cikin bala’in da take ciki shine jinin mutane da ake zubdawa ba tare da cewa yan kasar ko hukumominta su damu ba. Duk wata al’umma da ta san abinda ta ke yi hatta dabbobi ta na tashi tsayin daka wajen ganin ta kare rayukansu. Amma mu a Nigeria babu wani rai da yake da cikakken tsaro kuma idan aka kashe shi an kashe banza ko wanene don babu abinda za’a yi. Kwarai kuwa domin a kasar nan ne a bainar jama’a aka yi sanadiyar daya daga cikin gwarazan yan siyasa da basa tsoron kowa, wato Chuba Okadigbo amma babu abinda aka yi. Sannan an kashe ministan shari’a Bola Ige, kuma wanda ake zargi da hannu, Omisore, yana kurkuku aka zabe shi zuwa majilisar dattawa. Don Allah a wace kasar duniya ce za’a zabi wanda

Dabara Ta Rage Wa Mai Shiga Rijiya…

Image
To, an dai gama zabubbukan cikin gida na jam’iyyu kuma kowa ya ga abubuwan da suka faru, amma ban sani ba, ko kowan ya fahimci abubuwan da ya kamata a ce mun fahimta. Na farko dai muna iya fahimtar cewa idan ka dubi dukkan jam’iyyu zaka gane cewa babu wani mahimmin banbanci a tsakaninsu yadda aka gudanar da zabubbukan fitar da ‘yan takara, domin dai idan ka cire takarar shugaban kasa a ACN da CPC, zaka fahimci cewa kudi ne yayi aiki ko karfin mulki wajen fitar da su, ba cancanta ba. Kuma ko a cikin ACN da CPC a zabubbukan gwamnoni da majalisu, kudin ya yi tasiri. Don haka me ka ke tsammani ga wadanda su ka ci takara kuma suka kai ga madafun iko? Abubuwa da dama sun taimaka wajen tallafawa siyasar kudi, na farko a ganina muna iya zargar mutum biyu wajen haddasa wannan yanayi, wato Marigayi Janar Yar Adua da Janar Babangida. Dalili na shine, Babangida shine shugaba na farko da ya rika dunkule makudan kudade yana baiwa yan takara a jamhuriya ta uku domin su ci zabe. Sannan ya kafa jam’iyy

INA MA DAI…

Image
Hankalin yan Nigeria da ma na kasashen duniya ya koma kan zaben watan afrilu saboda mahimmancinsa ga kasar da ma duniya gaba daya. Dalilai da dama sun saka wannan zabe ya fi kowanne mahimmancin a tarihin wannan dimokuradiya tun daga 1999. Da farko dai kowa ya ga irin guguwar Canji da take kadawa a kasashen arewacin afurka saboda talakawa sun fara gajiya da irin mulkin kama-karya da shugabanni ke yi. Zaben 2007 ya zama matattara ta magudi, sannan mutuwar Yar Adua ta kawo wani yanayi mai wahala kan tsarin bangaren da ya cancanci mulki. Idan muka kalli wadannan matsaloli, zamu fahimci cewa kamar yan uwanmu na arewawacin afurka, duk da cewa basu da matsalar rashin wutar lantarki, asibitoci, makarantu ko abinci, mun fi su cancantar muyi bore, saboda shekaru 12 na PDP, maimakon kawo ci gaba cikin al’amuran kasa sai koma baya. Idan muka kalli alkaluma na samar da man fetur, aikin yi, asibitoci, cin jarrabawar dalibai, tsaro da tulin abubuwa zamu fahimci cewa 1999 ta fi 2011 ta kowacce fuska.

ALAMUN TSINUWA...

Image
Duba na nazari da lura ka iya nuna mana alamomin tsinuwa sun bayyana a cikin al’amuran mutanen Nigeria. Idan muka dauke su daya bayan daya zamu ga cewa, duk da dai samun al’umma wadda take da Musulmi da Kirista masu yawa cikinta da kullum ke kiran Allahu Akbar da Halleluya, kamar Nigeria na da wuya. Amma sai dai shi Allah baya jin wannan kiraye kiraye namu saboda iyakar sa a baki ne babu shi ko kadan a aikace. Allah da kansa ya kwatanta mutane wadanda su ka yi watsi da rahamominsa takar dabbobi, sai kuma ya ce kai! sun ma fi dabbobi. Akwai wani ba indiye da muke hira wata rana sai yake bani wani labari kamar al’mara amma kuma idan aka kalle shi da idon basira za’a ga haka yake. Wato ya ce wai lokacin da Allah zai halicci duniya sai ya fara raba arziki ga kasashe, wasu ya basu kasar noma wasu ma’adinai, wasu albarkatun ruwa wasu yanayin damina ko sanyi ko Hamada. Da Allah ya zo kan Nigeria sai ya ce a debo kowanne irin abubuwan da ya raba wa sauran kasashe a saka a Nigeria. Nan da n

TSINUWA TA TABBATA A KAN MU…?

Image
An yi zabe an gama, duk da dai cewa rigingimu sun biyo bayan zaben, kuma an tabbatar da cewa shugaba Goodluck shine ya cinye zaben da gagarumin rinjaye. Kafin a yi wannan zaben marubuta iri-iri sun yi sharhi kuma ina daya daga cikinsu, cikin wani sharhi da na yi, na zargi Muhammadu Buhari da yin taurin kai wanda zai iya sa kasar ta kasa samun canji, kuma hakan ya faru a yau. Babu yadda za’a yi ka ci mulkin Nigeria ba tare da kana da kyakkyawan kawance da yarbawa da inyamurai ba, kuma jam’iyya ke cin zabe na kasa ba mutum ba. Muna gani Buhari ya ci jihohi sha biyu amma da kyar ya sami kason 25 a cikin 16. A yanzu muna gani Kano, Bauchi, Katsina, Kaduna da su ka bashi kuri’a sama da Miliyan dai dai, sai ga shi Duk wadannan jihohi sun zabi gwamnonin PDP. Domin kamar yadda n ace, hakika ba mutum guda ke cin zabe ba sai jam’iyya. Mutane da dama sun harzuka da irin bayanai na tare da maida min martini ta hanyoyi daban-daban, amma na san yanzu zasu iya fahimtar dalilan da muka zargi Buhari

PDP: SHEGIYAR UWA

Image
2012 Mafi yawancin lokuta an fi samun shegen da fiye da shegiyar uwa, amma duk inda aka sami shegiyar uwa ka tabbatar ‘ya’ya da jikoki, da ‘yan uwa da surukai da makwabta, kai har ma da mutanen gari sun shiga uku. Hakika idan mutum yayi cikakken nazari na al’ummomin Nigeria da halayyarsu zai ce lallai mun yi babban dace da uwa. A wannan lokaci da PDP ta cika shekaru 14 a duniya, idan muka bibiyi tarihinta zmu ci karo da gagaruman abubuwa da ta kawo ko kuma ta jaddada a wannan kasa tamu. Munafinci da son kais hi ya auro mana wannan uwa tamu. Domin dai manyan mutanen kasar da magoya bayansu ne suka yi gangami wajen daurin auren a matsayin waliyyanta. A matsayinsa na tsohon soja mai fada a ji, kuma mai tanadi da ganin cewa ya sake dare kujerar mulkin a karo na biyu, Janar Babangida, yayi wuf ya kawo Obasanjo domin ya zamar mata dan takara. Wannan yunkuri yana da manufa mai harshen damo; wato a rage wa Yarbawa radadin June 12, sannan a share masa fagen cimma wancan burin a dawowa (tunda

SARKIN KANO DA GWANINTAR IYA SUKA

Image
Duk wanda ya sami tattaunnawa da Sarki Kano, babu makawa zai sami kansa cike da mamaki na irin basira, ilimi da iya Maganarsa. Ba zan manta da samun kaina a a irin wannan yanayi ba, wasu shekaru a baya, da muka sami zama da shi, mu ka yi doguwar tattaunawa a gidansa na Gandun Albasa tun kafin ya zama sarkin Kano. Duk da cewa abubuwa biyu da muka tattauna a wannan rana, wato maganar jefe mazinata wadda a  lokacin su ka yi ta takaddama da marigayi Sheik Jafar, sannan da maganar cire kakansa Sunusi Murabus wanda Sardauna ya yi, na sami karuwa ta ilimi sosai a kan wandannan maudu’ai da muka tattauna. Na kasance a wannan lokaci ina yin bincike domin wallafa littafi na a kan jefewa sannan kuma kasancewar babban yayana, ya na auren yar sarki Sunusi wato goggon Sunusi Lamido, wadda na taso a gidansu, labarin wahalar da iyalan sarki Sunusi su ka fuskanta ba sabon abu bane a wajena, amma dai na karu da wasu abubuwan da ban taba ji ba a lokacin. Sunusi Lamido bai taba boye burinsa na gadar kakans