MATASALAR ALMAJIRANCI: MENENE MAFITA (Kashi na biyu)

 


Almajiranci kamar yadda na fada a baya ya lalace sakamakon shigowar bara cikinsa bayan turawa sun rushe daular usmaniyya. A yanzu ka na iya ganin yaro dan shekaru 3-4 a titi yana yawon bara a matsayin almajiri. Hakika tsananin rashin tausayi da tsagwaron rashin imani ne zai sa mutum ya jefo dansa mai karancin shekaru irin haka kan titi ba tare da sani ina ya kwana ya tashi ba, ballantana harkar abincinsa ko lafiyarsa balle uwa uba tarbiyarsa. Binciken kimiyya, musamman wanda mashahurin manazarcin dabi’a Sigmund Freud ya kira “Psychodynamic Perspective” da kuma aikin August Aichorn na “Latent Delinquency” sun nuna cewa akwai alaka mai karfi tsakanin shekarun yarinta (1-10) wadda ba’a sami cikakkiyar mu’amala ta yau da gobe tsakanin yara da iyayensu ba, wajen haifar da halayen  rashin tausayi da imani, zafin rai da kuma rashin nadama a halayyar irin wadannan yara idan sun balaga. Idan muka duba masifun Boko Haram da ta’addanci da satar mutane, ya isa ya tabbatar mana da wancan binciken kimiyya cewa mafiya yawan wadanda ke ta’asar irin wadancan yara ne da su ka taso ba su sami soyayya da shakuwa ta iyayensu da al’umma ba.

Cin hanci da rashawa wanda ya yi mana katutu ya bada gudunmuwa mai yawan gaske wajen lalata al’umma saboda gwamnatoci sun kasa samar da ababen more rayuwa da ayyukan yi ga dimbin matasa, musamman a harkar noma wadda za ta iya rage yawan kaura daga kauyuka zuwa birane. Yawan haife-haifenmu ba tare da samar da tsarin kula da karuwar jama’a ba, yafi hadarin yaki domin nan da shekaru talatin zamu zama kasa ta uku mafi yawan al’umma a doron kasa. Alkalumma na kwanan nan sun nuna cewa muna da yara kimanin miliyan 13.5, yawancinsu almajirai, wadanda ba sa zuwa makaranta sai dai gararamba a tituna. Illar da almajiranci ke haifar mana wajen asarar basira, saka yaran cikin masifun yanayin talauci tare da asarar samun kulawa ta iyaye zai iya tarwatsa zamantekawar mu nan da yan shekaru idan ba’a magance matsalar ba. Amma akwai hanyoyi da dama wadanda idan an bi su za’a iya maida harkar almajiranci ta zama mafita ga wasu matsaloli namu. Amma hakan ba zai yiwu ba sai kowa ya tashi tsaye ya bada tasa gudunmuwar tsakani da Allah.

MAFITA

Kashe almajiranci rana guda, abu ne wanda ba mai yiwu ba, domin duk abinda al’umma ta ginu a kansa kuma wasu ke cin moriyarsa sai an bi a hankali wajen magance shi. Kamar yadda a tarihi mun ga yadda zuwan musulunci bai hana bauta nan take ba, domin Allah ya rika saukar da hukunce-hukunce daki-daki domin dakile tsarin. Da farko Allah ya umarci annabi cewa ba sauran kamen bayi sai an ci abokan gaba da yaki, kuma wadanda aka kama ko dai a sake su bayan fansa ko fi sabilillah abinda ya datse babbar hanyar samar da bayi matuka. Haka nan abubuwa na shari’a irinsu rantsuwa, karya azumi da kaffarori daban daban aka alakanta su da sakin bayi. Dalilin bin wannan tsari shine domin a karni na 7 idan aka hana bauta nan take, tattalin arzikin larabawa wanda ya ginu a kan bayi da bauta zai rushe nan take. Don haka almajiranci kansa ya na bukatar bin tsari daki-daki domin a canza shi daga yadda yake a yanzu ya koma yadda zai taimaki kowa, kuma wannan shine babban kalubalen mu a yau.

SHARI’A

Hanya ta farko da ya kamata a duba shine ta fannin sharia. Wajibi majalisun dokoki na jihohinmu su yi kuduri na hana bara kowacce iri sannan kuma a kayyade iya shekarun da Uba zai iya tura dansa makarantar allo, kuma ya kasance kada a tura wani yaro wata jiha sai dai a iya karamar hukumarsa. Babban abinda ya ta’azzara bara shine kasancewar a baya da wahala ka ga almajiri wanda ya gaza shekaru goma amma yanzu dan shekaru 3-4 za ka gani ya na bara. Wannan dabi’a ta samo asali saboda yadda iyaye ke hayayyafa amma ba sa son kula da dawainiyar yayansu. Don haka da zarar yaro ya fara tafiya Allah-Allah a ke a tura shi almajirci domin a sauke nauyin kula da ciyar da shi. Wajibi a hana iyaye watsowa al’umma irin wadannan yara wadanda idan sun taso a haka su kan kasance ba sa tausayin kowa domin su na ganin ba wanda ya tausaya musu. Ba sa son kowa domin ba su tsosi soyayya daga wajen iyayensu ba balle su nuna wa wani. Wannan ita ce babbar hanya ta dakile almajiranci.

TSANGAYU

A tarihin almajiranci a Nigeriya ba wani shugaban kasa da ya yi hobbasa wajen kawo canji a tsarin almajirci kamar Jonathan domin a mulkinsa ya yi kokarin gina makarantun tsangayu 157 a fadin kasar nan. Matsalar da wannan tsari nasa ya samu ita ce kasancewar an yi da zummar siyasa ne kawai kuma ba’a tsara shi yadda ya kamata ba. Wajibi a farfado da wadannan makarantu na tsangaya kuma a fadada su yadda kowacce karamar hukuma ta sami nata. Alfanun makarantu tsangaya irin wadannan zai fito fili idan aka yi la’akari da tsangayar Malam Muhammadu Basakkwace wadda ke garin Gombe. Wannan malami ya ci gajiyar wancan tsari na Jonathan, amma duk da cewa ginin makarantar kawai aka mallaka masa, ya nemo sauran mutanen unguwa sun hada kai wajen kawo nagartaccen tsari domin ganin wannan makaranta ta dore. Sun fadada yawan almajirai yadda ba kawai almajirai ake koyarwa ba har da yaran unguwa kuma duk almajirin da ke makarantar ba ya fita bara domin ana dafa musu abinci sau uku a rana. Sannan akwai wajen wanka da bahaya kuma an saka cikin manhajar karatunsu nazarin turanci da lissafi. Baya ga haka a wannan makaranta akwai tsarin koyon sana’o’i kama daga yin sabulu, man shafawa, dinki da sauran sana’o’in hannu. A hira da BBC malamin ya tabbatar da cewa a wannan sabon tsari yaransa sun fi saurin haddace Qur’ani fiye da yadda ya ke a baya. Kuma cikin dalibansa wanda aka yaye, ya gaya wa BBC cewa a wannan shekarar ya dinkawa mutane sama da hamsin kayan sallah, sannan ya zama mai koyar da yara yadda a ke dinki a wannan makaranta ana bashi alawus.

Wannan tsari na tsangaya idan aka zurfafa tunani da tallafi watarana zai iya kasancewa hanya mafi girma a arewacin Nigeriya wajen samar da kayayyakin bukatu na yau da kullum tare da samar da ayyukan yi ga yaran mu sama da miliyan 13.5 da basa zuwa makarantar boko. Irin wannan tsari na samar da gungu-gungun ma’aikata masu sana’ar hannu ita ce ta zama ginshikin juya akalar tattalin arzikin kasar China a shekarun baya. Mu na da mutane sama da miliyan dari a arewacin Nijeriya wadanda ke bukatar abubuwa wadanda sai mun jira an kawo mana su daga China. Shin idan aka inganta makarantun tsangayu yadda zasu iya yin sabulu/mai/hula da sauransu wadanda za’a siyar a yankin nan, miliyan nawa za’a samar?

 

SAMAR DA KUDADE

Babu wata al’umma a duniya da za ta zauna lafiya idan mutanenta ba sa taimakon junansu. Shi kuma yawan jama’a alheri ne ga duk al’umma mai taimakon junanta. Kungiyoyinmu da ke yaki a kan maganar almajiranci wajibi su dunkule waje guda a samar da kwamitin tsangayu a kowacce jiha wanda zai kunshi limaman masallatai da sarakuna da yan boko domin samar da gidauniyar tsangayu wadda a duk sati zata rika tattara kudade a masallatan jummu’a domin tallafawa tsangayu. Sannan a hura wuta yadda kowacce jiha zata ware ko da kashi 2% ne a duk wata domin tallafawa wannan gidauniya. Ayyukan wannan gidauniya zai kasance na samar da hanyoyin sana’o’i a tsangayu, wato bangaren koyarwa da kuma samar da kayayyaki.

GWAMNATIN TARAYYA

Yunkurin Jonathan wajen samar da kudaden yin wadancan tsangayu ya kamata a ce ya bude idanuwanmu mu gane cewa ashe dai dokar Ilimin Bai daya ta kasa (Ubec Act 2004) ta bada damar samar da kudade wajen tallafawa almajirci. Dole kwamishinonin ilimi na jihohin arewa su dunkule wajen fitar da ingantaccen tsari yadda a duk kasafin kudi na Ubec kason tsangayu zai dinga tafiya kai tsaye jihohi ko da karkashin Subeb ne domin raya makarantun tsangayu.

NOMA

Dole jihohi su dawo da hankulansu wajen saka kudade domin farfado da noma ya zama sana’a ta kasuwanci. A arewa mu na da dama-damai wadanda ke zaune a banza ba’a morarsu. Ya kamata a yi makarantun tsagayu duk inda ake da Dam yadda dalibai za su rika yin noma da kiwo wanda zai samar da kudaden shiga da ayyukan yi ba ga almajirai kadai ba har da gwamnatoci. Yan majalisunmu na tarayya maimakon su rika siyen Babura su na rabawa ya kamata su karkatar da irin wadannan kudade da na ayyukan mazaba wajen ganin an samar da kwami-kwami na noma a duk bakin kogunanmu da rafuka da dama-damai wanda zai bunkasa harkokin noma da kawar da talauci. Ya kamata mu gane cewa arewa ba ta da wata hanya da za ta iya maganin talaucinta irin ta hanyar farfado da noma. Noma zai iya samarwa arewa ninkin kudaden mai da yankin ya dogara da shi. Idan gwamnatocin jihohi su ka saka jari a harkar noma da kiwo, hakan zai yaki masifun da mu ke fuskanta a yau na makiyaya da ta’addanci da sace-sacen jama’a.

A karshe ina ganin cewa idan muka hada karfi-da-karfe mu ka tashi tsaye, hakika muna iya juya akalar matsalar almajirai ta zamar mana mafita wajen samar da miliyoyin ayyukan yi tare da inganta tattalin arzikin arewa, wanda ita ce hanya tilo wadda za ta yi maganin matsalolin rashin tsaro da muke fuskanta. Wajibi a rarraba arziki kamar yadda addininmu ya koyar mana ta hanyar zakka da sadaka, ko kuma rowarmu da halin babakeren arzikinmu a hannu yan kalilan ya zama ajalinmu a matsayin al’umma.

Comments