ALAMUN TSINUWA...


Duba na nazari da lura ka iya nuna mana alamomin tsinuwa sun bayyana a cikin al’amuran mutanen Nigeria. Idan muka dauke su daya bayan daya zamu ga cewa, duk da dai samun al’umma wadda take da Musulmi da Kirista masu yawa cikinta da kullum ke kiran Allahu Akbar da Halleluya, kamar Nigeria na da wuya. Amma sai dai shi Allah baya jin wannan kiraye kiraye namu saboda iyakar sa a baki ne babu shi ko kadan a aikace. Allah da kansa ya kwatanta mutane wadanda su ka yi watsi da rahamominsa takar dabbobi, sai kuma ya ce kai! sun ma fi dabbobi.

Akwai wani ba indiye da muke hira wata rana sai yake bani wani labari kamar al’mara amma kuma idan aka kalle shi da idon basira za’a ga haka yake. Wato ya ce wai lokacin da Allah zai halicci duniya sai ya fara raba arziki ga kasashe, wasu ya basu kasar noma wasu ma’adinai, wasu albarkatun ruwa wasu yanayin damina ko sanyi ko Hamada. Da Allah ya zo kan Nigeria sai ya ce a debo kowanne irin abubuwan da ya raba wa sauran kasashe a saka a Nigeria. Nan da nan sai mutanen sauran kasashe suka fara korafi “Yaya za’a hada wa Nigeria komai?” Sai Allah yace “haba ku tsaya mana ku ga irin mutanen da zan zuba a cikin kasar mana”. Ganin irin mutane da Allah ya zuba (wato malalata masu son kai) sai sauran kasashe hankalin su ya kwanta domin ganin cewa wadannan mutane ba zasu tabuka komai ba.

Cikin satin da ya gabata an sako wasu mashahuran yan siyasa guda biyu daga gidan kurkuku sakamakon mashahuriyar zamba cikin aminci da rub-da-ciki da kudin jama’a na biliyoyin Naira. Wadannan yan siyasa daya daga kudu, Bode George da kuma dan arewa, Aminu Dabo. Amma saboda kasancewar alamomin tsinuwa sun tabbata a cikin wannan al’umma ta mu, sai ga shi manyan yan siyasa (harda tsohon shugaban kasa, Obasanjo, wani gwamna da ministoci da talakawa) sun yi dafifi wajen taron Bode George, kai har ma da bashi takardar yabo. Mutanen da kotu ta caja ta same su da laifi dumu dumu na cin dukiyar jama’a ta yanke musu hukunci dauri a gidan yari, amma maimakon a kyamace su don wasu su hankalta, sai ma karrama su aka yi. Don Allah ka gaya min dalilin da idan wasu ko su suka sake samun dama ba zasu sake aikata ta’asar da ta fi wannan ba? Kuma ka gaya mini ta yadda wadanda ke kan mulki za sa su ji tsoron cin amanar talakawa a nan gaba? Su kansu, maimakon a ce sun saci jiki wajen komawa gidajensu saboda jin kunyar an daure su saboda sata, sai ga su a bainar jama’a suna cewa “sata halas ce kuma wanda duk ke son jama’a su karrama shi to ya zama babban barawo”

A satin da aka saki wadannan mutane (a kasar da alamun tsinuwa ya hau kanta) amma a can kasar masu hankali (Turai) sai ga shi Ministan tsaron Jamus yayi murabus saboda an sami tabbacin cewa a cikin takardarsa ta digirin digirgir (PhD Thesis) Ya kwashi bayanai da bai nemi izni ba sakamakon haka dole ya bar mulki. Yan majalisar kasar da manyan masana sune kan gaba wajen neman ya ajiye aiki saboda wannan abin kunya da ya yi. Amma a nan Nigeria me kake tsammani da zarar wani ya taba yan majalisa? Na san ba ku manta da yadda aka yi ta yamadidi da Sunusi Lamido ba lokacin da ya fadi abinda yan majalisa ke samu a shekara.

Munga yadda rigima ta barke tsakanin Sola Saraki da dansa gwamna mai ci, Bukola saboda shi Sola yana son idan Bukola ya gama mulkinsa ya barwa kanwarsa, wadda take yar majalisar dattijai tazo ta gaje shi. Amma watakila kasancewar ba uwarsu daya ba sai ya kekasa kasa da hujjar cewa mulkin jihar ba gado ba ne yadda har suka sami sabani da mahaifinsa. Bayan ya koma bangaren Goodluck sai aka yi masa alkawarin kujerar sanata don haka duk da cewa mulki ba gado bane don ya hana kanwarsa ta gaje shi, sai gashi shi kuma ya na son ya gaje ta.

Muna gani yadda gwamnatin Ibrahim Shekarau ta zo da sharia ta kuma samo wani kafaffen mai zafin ra’ayin addini, wato Rabo, ta bashi hukumar kula da dab’i da tace fina-finai domin ya kawo gyara cikin al’amura. Ya kama yaki gadan-gadan da yan fim domin ya kori abinda ya kira “Badala”. Cikin lokaci kankane ya gurgunta wannan harka a Kano wadda ke samar wa dubban samari aiki, domin daga zarar marubucin fim ya dora bironsa a takarda an fara samun aikin yi ga samari ta hanyoyin irinsu matan aure da ke cikin gida su bada zannuwansu haya, masu yin abincin location, masu pure water da zobo. Abin bai tsaya nan ba domin yan kasuwa iri-iri kama daga masu saida kaset, masu bada hayar na’urori, masu bada gidaje da sauransu. Hatta ga yara masu share wuraren da ake daukar fim da masu motocin haya da otel-otel. Haka abin zai yi ta tafiya har aje ga yara masu daukar fina-finai suna yawo  a shataletale suna saidawa. Babu wanda zai zargi gwamnati idan ta nemi kawo gyara cikin al’amura amma ba wasu mutane da basu gama fahimtar addini ba, su rika neman cusa tunaninsu cikin al’amura. To in gajarce maka zance, sai aka wayi gari mai dokar barci ya bige da gyangyadi domin cikin Azumi da ya gabata sai ga kafofin yada labara sun kawo labarin an kama Rabo na kokarin lalata da wata yar karamar yarinya, wadda take karkashin kularsa. Amma sai gashi zancen yayi shiru, gwamnati ba ta sa an yi bincike ba kuma su yan sanda ba su kai abin kotu ba, kuma kowa ya yi shiru. Babban abin haushi, maimakon a ce gwamnati ta sauke shi ko kuma shi kansa ya yi murabus, sai gashi ya dawo yana shiga kafafen watsa labarai da sunan yana ci gaba da yaki da ”Badala”. Wannnan rashin kunya ta yi yawa, ko da yake dai ina ganin cewa tuni dama aka yi jana’izar Kunya a wannan kasa. Kwanan nan ne saboda zargin lalata (ba kamawa a cikin duhuwa ba) da aka yi wa Berlusconi, shugaban kasar Italiya, gwamnatin ke neman faduwa. Ya ilahi, wannan bai nuna cewa muna cikin tsinuwar Allah ba?

Rikicin Jos ya kai kimanin shekaru shida ya ki ci ya ki cinyewa kuma an kashe daruruwan mutane, amma muna gani saboda mutuwar mutum guda ya jawo faduwar gwamnati a Tunusia. Cikin yan kwanakin nan Goodluck ya je Jos kamfe amma har ya gama bai Ambato zancen rikicin ba. Wacce irin alumma ce wannan? Duk wanda ya kwana ya tashi a Jos (Kirista da Musulmi) babu abinda ke damunsa irin wannan rikici, amma ace shugaba mai ci ya kasa komai akan abin sannan kuma ya je kamfe, ai ko don yaudara ma ya tabo zancen. Su kuma wadanda su ka yi masa dafifi, babu wanda zai iya tambayarsa me ya sa bai yi komai ba kuma idan ya sami dama nan gaba me zai yi?

Mutanen da ke son su ga cewa an sami canji a wannan zaben sun fahimta sun kuma yarda cewa kawar da PDP shine kadai mafita, kuma sun yarda cewa idan za’a kauda PDP dole sai an yi hadin gwiwa amma sai gashi hadin gwiwar ya gagara. Yan Nigeria masu ra’ayin canji suna ganin cewa jam’iyyun adawa na CPC da ACN kadai ke iya kawo canji amma kuma an kasa fahimtar cewa wadanda suka kasa hadewa waje guda domin yakar PDP, me kuma zasu iya yi? Ribadu ya ce zai janyewa Buhari amma ACN ta bada sharadin sai dai dan takara ya fito a karkashin jam’iyyarta tunda su ke da gwamnoni amma Buhari yayi kunnen uwar shegu. Mutane masu neman canji a Nigeria ba za su gafartawa Buhari ba matukar PDP ta koma kan mulki domin shine ya kawo cikas. PDP ta gaza su kuma yan adawar su ma sun gaza, ba don komai ba sai saboda kowa ka gani a kasar nan (face kalilan) bukatarsa ita ce bukata ba wai ta mutane ba. Domin idan dai Buhari ba bukatar kansa ya sa a gaba ba don menene za’a bashi dama amma saboda jam’iyya kawai ya bari abin ya lalace? Shin ba ANPP ya bari ba wadda ta tsai da shi takara sau biyu? Kuma matukar aka yi hadakar aka kai gaci, idan har ya fuskanci abinda bai gamsu da shi ba a ACN yana iya ficewa kamar yadda ya fice daga ANPP. Duk da cewa sai da lokaci ya kure masa sannan ya fita? Domin Bafarawa a cikin hirarsa a wannan mujalla ya ce tun a 2003 ya ba Buhari shawarar ficewa daga ANPP amma ya ki. Shin Buhari na son ya maimaita irin wannan kuskure ne? Idan kuma a kan Tinubu ne ya nace sai an bashi mataimaki, shin yanzu tinubu ne mataimakin Ribadu? Akwai wanda ya yi min martini a kan rubutu na na baya cewar ko ina yaro ko bana kasar ne Buhari yayi mulki, alal hakika kamar yadda ya fadi shekarunsa ina ganin ba zai girme ni ba ko mu zama sa’anni domin ina aji hudu na sakandare Buhari yayi mulki. Kuma ba’a taba shugaban da nake so na kare kamarsa ba, amma lokaci yayi da zamu daina dora dukkan burikanmu da na yayanmu da jikoki a kansa kuma kafiyarsa ta yi ta jawo mana hasarori. Domin da ya bi shawarar Bafarawa sun kafa sabuwar siyasa tun 2003 me kake tsammani? yi la’akari da lokacin da aka kafa CPC (Dec. 2010) da kuma irin tasirin da tayi a fagen siyasa yanzu. Kuma abin dubawa shine, menene mafi illa tsakanin barin PDP ta ci gaba da mulki, ko kuma wata matsala ta jam’iyya da ake hasashe? Kana da matsala, ka kuma san yadda zaka yi maganin matsalar sannan kana da yadda zaka iya maganinta amma ka kasa bin hanyar a radin kan ka, shin akwai wani alamun tsinuwa ta hau kanmu a matsayin al’umma sama da wannan? Dabba kadai aka sani da halin kowa ya yi ta kansa amma duk lokacin da mutane su ka ce kowa zai yi ta kansa to kowa yana cikin bala’i.

Zan iya rantsuwa cewa babu wani mahaluki da ya kwana ya tashi a kasar nan da ya ke jin dadi, matukar ya san menene jin dadi. Gaba dayan mu mun raja’a  a kan cewa kowa sai ya sami kudi shine zai ji dadi. To bari na baku misalai; duk kudin ka a Nigeria idan wani mugun ciwo ya kama ka sai dai a kai ka kasar waje domin ka nemi magani(watakila ka mutu a cikin jirgi), kuma idan kana son danka yayi karatu mai inganci irin wanda ka yi a makarantar gwamnati, a kuma aljihun gwamnati kana yaro sai dai ka tura shi waje. Sannan kana zaune a falon ka kana kallon labarai sai wuta ta dauke dole sai an tashi generator ya dame ka da kara kuma zuciyar ka na tunanin kudinka ka ke Konawa. Idan ka hawo motarka ta miliyan biyar sai dan Acaba ya zo ya fasa ma Danja kuma mutane su yi ca a kanka suna baka hakuri dole ka hakura, idan bah aka ba a zage ka da cewa baka da mutunci. Idan dan hiace yayi maka mummunan overtaking, ka na yin magana sai ya zage ka kuma babu yadda zaka yi.

Idan kuma kana takamar cewa mulkin da kake yi akwai jin dadi cikinsa, dubi yadda ka zama duk inda kake kana cikin fargaba ta cewa saura kwana kaza ka sauka. Ka hana kanka barci kana kamfe, mutanen da kake rainawa sune abokan yawonka dare da rana. Idan ka ci zabe, bukatun abokan ka da suka cicciba ka sun yi yawa ka rasa yadda zaka biya su, a karshe wasu su koma abokan gabar ka. A gida kana cikin karbar bukatu na yayanka da matanka da yanuwansu da abokai na kusa. A ofis ma haka, a hanya ma haka. Duk inda kake mutane ke kokarin amfani da kai don cin ma burukansu, kuma wanda duk ka hana wata dama sai ya daura gaba da kai. Wanda kuma ka yi wa yanzu, anjima kadan ya dawo da sabuwa. Da zarar ka zo sauka sai kaga an fara watsewa, kana sauka sai ka wayi gari kaga cewa babu kowa tare da kai, idan ka yi sata da yawa ka sami dan abin yi, idan ko baka saci komai ba sai kai ma ka koma bara wajen masu shi.

Shi kuwa talaka dama zancen jin dadi bai sanshi ba, domin bala’in tuwo da ya sa shi a gaba kadai ya ishe shi. Don haka bai san kansa ba balle ya san abinda ya kamace shi. Ya zama kamar mahaukaci a kan titi baya ji baya gani, don haka dokar titi ma baya binta, sassauci da sanin ya kamata babu shi tsakaninsa da dan uwansa talaka. Idan ya koma gida ko kula matarsa baya iyawa saboda gajiya da bacin rai. Amma dai duk da haka yana da damar da zai iya amfani da kuri’arsa domin ya kawo wa kansa canji amma…kash, sai dai kuma karancin masu kawo canjin.

A ganina babu wata kasa da Allah yayi wa albarka irin Nigeria (idan mu ka yi la’akari da arzikin ciki da yawan mutanenta) saboda ya bamu kasar noma wadda ita kadai ta ishe mu idan da mun inganta ta. Idan ka je Zimbabwe, kafin Mugabe ya haukace, zaka sami gona wadda tsawonta ya kai daga kano zuwa kwanar dangora ta mutum guda da ma’aikatansa. Muna da ma’adinai kusan kowanne iri, akwai koramu da rafuka. Ga wuraren yawon bude ido da albarkatu iri iri amma a banza saboda, kamar yadda abokina dan indiya ya ce, malalatan mutane masu son kai ne cike da kasar. Da ana ba Allah shawara da na ce masa ya canza mutanen ciki, domin duk wasu alamu na tsinuwarsa ta hau kanmu, idan ya so ya dauke albarkatun. Domin akwai mutane masu kwazo da kishi wadanda kasashensu basu da komai amma sun kai gaci...ganiya.

 

 

Comments

Popular posts from this blog

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

SARKIN KANO DA GWANINTAR IYA SUKA