LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?
Kafin zuwan musulunci a karni na 7, larabawa sun kasance a cikin
wani yanayi da aka lakabawa Jahiliyya. Dalili kuwa shine saboda rashin tsari na
zamantakewa cikin ilimi da kyautatawa. Kafin zuwan musulunci manya manyan
mafarautan dauloli irinsu Alexander the great sun mamayi duniyar wancan lokaci
amma basu kalli Arabia ba. Addinan Yahudanci, Kiristanci, Manikanci, Budanci da
Hindu duk sun kauce wa Arabia face mabiya kalilan daga yahudu da nasara da kan
zauna a garuruwa. Jahilcin larabawa ya kai cewa akan rakumi guda sai kabilu su
yi shekara da shekaru suna yakar juna, mata basu da wata kima domin babu wata
mu’amala da ake yi da su, kuma ana binne jarirai mata da ransu. Zuwan manzon
Allah cikin yan shekaru kalilan sai aka wayi gari kan larabawa ya hadu yadda
kafin shekara dari biyu bayan wafatinsa sun mamaye daulolin Syria, Egypt, Iran,
India, sassan China da gabashin duniya, haka nan har cikin gabashin Turai da
yammacin Afurka.
Daular musulunci tayi shekaru dari biyar tana jagoranci mulki da
ilimi a duniya amma kasancewar an yi watsi da koyarwar Qur’ani an shagala da
siyasa da jin dadi da tauye hakkoki na jama’a sai Allah ya kawo wasu kafirai
daga gabashin duniya, wato Mangoliyawa, karkashin Hulagu wanda ya kewaye garin
Bagadaza har tsawon shekara guda. Bayan ya kama garin, tarihi ya nuna cewa ya
kashe musulmi da ke cikin garin sama da 800,000 kuma suka yanka Khalifan wannan
lokaci, Al-Mustasim, tare da duk iyalansa.
Allah ya gargadi larabawa cikin suratul Muhammad
Q47:38 “Ga ku, ya ku wadannan (larabawa) ana kiranku domin ku
ciyar ga tafarkin Allah, sannan daga cikin ku akwai mai yin rowa. Kuma wanda ya
ke yin rowa, to yana yin rowar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadatacce alhali ku
fakirai ne. kuma idan kuka juya baya (daga yi masa da’a) zai musanya ku
da wadansu mutane, kuma ba za su zama irinku ba”
Fitowar manzon Allah cikin wannan kabila ya basu kima da basu
taba samu ba, amma kasancewar hakan sai su ke ganin a duniya babu kamarsu kuma
dole a yi musu biyayya. Larabawa sun cusa abubuwa na al’adunsu da yawa cikin
musulunci kuma saboda karancin bincike daga malamai ana kasa gane al’ada daga
addini. Ajamawa da yawa, basa son a fadi laifin larabawa sai su ga kamar an
soki manzo ne. A sani na ban ga wata kabila mai kabilanci da mugwayen halaye
kamar larabawa ba, domin a junansu ma yana tasiri. Allah da manzonsa sun
fahimci wannan hali nasu shi yasa suka karfafa yaki da kabilanci domin cikin
Qur’ani sai ya umarce mu
Q49:13 “Ya ku mutane, lallai ne mu mun halitta ku daga namiji da
mace, kuma muka sanya ku dangogi da kabilu, domin ku san juna. Lallai mafificin
daraja a wurin Allah shine wanda ya fi tsoron Allah”
Ko kafin wannan umarni da akai mana, Qur’ani ya bamu
tarihi cewa Annabi Nuhu sun yi hannun riga da dansa kuma Ibrahimu sunyi hannun
riga da mahaifinsa. Don haka fitowarka daga wani mafificin dangi ko kabila ba
zai sa ka fi kowa ba sai don tsoron Allan ka. Idan muka duba cikin tarihin
Annabi (SAW) zamu ga cewa a lokacin da ya shiga Madina kafin ma a gina
masallacinsa da inda zai zauna, mukami na jama’a (Public office) na farko, kuma
mafi muhimmanci wanda annabi (SAW) ya bayar shine na mai kiran sallah. Akwai
manyan sahabbai wadanda a matsayin dangi da kabila ba su da na biyu amma bai ba
kowanne ba sai ya ba Bilal (Bakin mutum kuma yantaccen bawa). Annabi (SAW) yayi
wannan ne domin ya tabbatar wa larabawa cewa lokacin kabilanci ya wuce kuma shi
yazo ne domin ya jaddada waccan aya da ubangiji ya saukar.
Larabawa, a da da yanzu, suna jin girman kai ganin annabi ya
fito cikinsu kuma an saukar da ayoyin Allah da yarensu, domin ba mu ‘yan baya
ba, hatta shi annabin akwai wadanda ke masa gorin wannan matsayin na su kamar
yadda Allah ya bamu labari cikin
Q49:17 “Su (larabawa) na yin gori a kanka (annabi) wai sun
musulunta. Ka ce “Kada ku yi gorin musulunta a kaina. A’a, Allah ne ke yi muku
gori domin ya shiryar da ku ga imani, idan kun kasance masu gaskiya”
Irin wannan gori da su ka yi wa fiyayyen halitta shine larabawa
na yanzu suka gada kuma suke wa ragowar musulmi. Allah ya ja musu kunne cikin
Q9:19 “Shin, kun dauka shayar da mahajjata da rayar da masallaci
mai alfarma kamar wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, kuma yayi jihadi a
cikin hanyar Allah? Ba su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah baya shiryar da
mutane azzalumai”
Kasancewar mutanen Saudia suke kula da haramai da dawainiyar
wuraren, kada su dauka cewa daidai yake da imani da Allah ko wani garanti ne a
bangarensu. Garantinsu guda shine bin abinda Allah ya umarta. Kuma Allah ya
sake tabbatar mana da halayyar larabawa tun fil azal wadda ita suka gada har
yau, shi yasa ya ce musu
Q49:14-15 “Larabawa suka ce “Mun yi imani” ka ce “Baku yi imani
ba, amma dai ku ce mun mika wuya” imani bai gama shiga a cikin zukatanku
ba…..Muminan gaskiya kawai su ne wadanda suka yi imani da Allah da manzonsa, sannan
ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihadi da dukiyarsu da kuma rayukansu cikin
tafarkin Allah. Wadannan sune masu gaskiya”
Tsarin kasar Saudia daga shekaru dari 250 da suka wuce zuwa
yanzu ya ta’allaka ne daga irin tunanin da Muhammad Ibn Abdulwahab da taimakon
Ibn Sa’ud (a 1774) ya gina kasar na bin addini da tsatstsauran ra’ayi.
Wahabiyanci ya karbu a kasar har da waje domin mayakan Abdulwahab sun karbe
Makka da Madina da Riyadh har ma da Karbala da ke cikin Iran, Kafin Sojojin
Turkiya karkashin sarki Mahmud II su cinye su da yaki. Abdul’Azizi Bn Sa’ud ya
sake yakin da ya kwato garuruwan daga hannun ottomans cikin shekarun 1920-26.
Tsanani irin na tsarin wahabiyanci ya haifar da mutane masu tsatstsauran ra’ayi
a zamaninmu irin su Osama Bn Laden, domin suna kallon addini ne ta mahangarsu
kadai.
Wannan ya kawo mu kan matsalar da mahajjatanmu na bana suka
fuskanta a kasar. An tsare mata sama da 1500 a cikin kunci da wulakanci kuma
daga baya aka dawo da su gida. Hujjar da suka bayar itace ta rashin muharramai.
Maganar muharrami Allah bai wajabta ta cikin Qur’ani ba amma Annabi (SAW) ya
bada ita cikin Hadisi. A malaman hadisi Bukhari ne kawai ya ruwaito hadisai
biyu (mujalladi na 3, littafi na 29 hadisai na 85 da na 87). Ina dalilin da
annabi (SAW) yace mata idan zasu yi tafiyar kwana biyu su tafi da muharram?
Saboda larabawa a wancan lokaci mace bata da wata kima don a cikin gidanta ma
sai a far mata balle ta yi tafiya. Domin kada mugwaye su far ma mace idan babu
mai tsaronta, shi yasa annabi (SAW) ya umarce su da tafiya da muharrami.
Sharadin muharram kuma kamar yadda rayuwar annabin ta nuna sai idan ita kadai
zata tafi amma idan a kungiyance ne ba’a bukatar kowacce sai da muharraminta
daban. Idan mata na gungu ne, ko na fatauci ko yaki ko aikin hajji basa bukatar
kowacce sai da muharraminta. A wannan tsari ne mutanen duniya kaf, ba na Nigeria
kadai ba suke yin aikin haji tsawon shekaru. Amma saboda wata manufa tasu sai
suka yi wannan kulli. Kuma sai da aka yi jirgi sha biyar kafin su fara tare
mata, sannan a cikin jirgi guda sai su ware mata masu kananan shekaru su bar
manya. Larabawa, musamman na Saudia suna ganin sune musulunci don haka duk
yadda suka so ko su ka fahimta dole haka za’a yi. Kuma wannan dabi’a sun gado
ta ne daga kakannisu domin Allah ya gaya mana cewa tun lokacin annabi larabawa
na shishshigi cikin lamarin addini
Q49”16 “Ka ce “kuna sanar da Allah ne game da addininku?”
Wato duk abinda tunaninsu ya dora su a kai sai su yi kokarin
tilasta shi ga sauran musulmi, kamar Allah bai bada hukunce-hukunce cikin
littafinsa ba. Idan har wannan hukunci da suka tilastawa matan Nigeria don
hakkin shari’a ne, to ya zama wajibi a dora kan kowacce mace yar Nigeria ba a
ware wasu ba. Haka nan wajibi ne a wajabta ga dukkan sauran matan kasashen
duniya, matukar za’a tabbatar da hukunci na shari’a bana son rai ko nuna isa
ba. Karancin bincike daga malamai ya saka abubuwa da yawa da muke dauka addini
ne sun yi kakagida cikin musulunci wadanda a zahiri ba fadar Allah ba ce face
al’adun larabawa. Misali idan ka dauki saka hijab da nikaf, wanda al’ada ce ba
ma ta larabawa kadai ba ta dukkan mutane ne dake zama cikin zafin Hamada
(Semitics). Idan kana lura zaka ga matan da ake kira da “Nuns” na kirista suna
yin hijabi irin na musulmi, haka ma matan yahudawa masu zaman saumomi. Amma a
zamaninmu babu abinda ya zama abin ja-in-ja da kasashe kamar shi. Bara, wani
malami balarabe daga jami’ar Azhar ya fito fili ya gaya wa larabawa cewa wannan
Magana ta nikaf al’ada ce. Me Allah ya gaya mata game da rufe jikinsu?
Q24”31 “Ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu, kuma su
tsare farjojinsu, kuma kada su bayyana kawarsu face abinda ya bayyana daga
gareta, kuma su yafa mayafansu a kan wuyan rigunansu”
Allah bai ce mata sai sun saka hijab daga kansu ko kuma su rufe
fuskarsu ba, su dai rufe kafadunsu da kirjinsu. Kuma ko cikin tafsirin Ibn
Kathir abinda ya fassara da dora mayafi kan “juyub” shine kafadu da hakarkari.
Amma tun kafin zuwan musulunci, saboda kariya daga zafin rairayi da kura,
larabawa (maza da mata) na lullube kansu da fuskokinsu. Idan da Allah ya karbi
tsohuwar al’adar larabawa ta rufe kai da fuska ai sai ya ce wa mata musulmi su
rufe kawuna da fuskokinsu. Larabawa suna da al’ada ta fada da kisa don haka
komai da bai yi musu daidai ba sai su suce kawai a kashe mutum, kuma da sunan
musulunci duk da cewa Allah bai fada ba kuma annabin bai aikata ba. Shi ko
kashe rai Allah kadai ke da hurumin ikonsa kamar yadda ya ce mana
Q17:33 “Kuma kada ku kashe rai wanda Allah ya haramta face da
hakki”
Amma larabawa saboda su na ganin kamar cewa addinin nasu ne,
kuma ba su dauki rai wata tsiya ba, kowanne laifi sai su ce a kashe, misali su
ce a kashe mai zagin manzo (SAW), a kashe wanda ya koma wani addini, musulmin
da ya ki yin sallah da sauransu duk da cewa Allah bai fada ba cikin Qur’ani.
Kuma duk wani abu da al’adarsu ta gada idan musulunci ya fada sai kaga sun fi
karbar sa sama da komai, misali kamar maganar baya ta Hijab da Nikaf ko maganar
cin alade, don haka da musulunci ya haramta sai suka rike shi fiye da duk wani
hukunci. Amma abinda basu gada ba misali
Q47:38 “Ga ku, ya ku wadannan (larabawa) ana kiranku domin ku
ciyar ga tafarkin Allah, sannan daga cikin ku akwai mai yin rowa. Kuma wanda ya
ke yin rowa, to yana yin rowar ne ga kansa”
Larabawa na da arzikin da ya fi na kowa a yanzu domin kasashen
larabawa sune ke da fiye da rabin man fetur a duniya kuma shine akalar tattalin
arzikin duniya amma daidai da rana daya baza su iya amfani da wannan damar
wajen tursasawa kasashen yamma da hana cin zarafin manzo (SAW) da musulmi ba
domin tsoron kada su rasa kudin shiga. Idan da gaske suke yi kamar yadda suke
yi wajen harkar fatawoyi ta cewa a kashe wannan da wancan to su yi amfani da
kudadensu wajen kwato mana hakkokin mu da na manzo (SAW) da aka sa a gaba mana.
Ina ganin ba zasu iya ba, kuma wannan hali nasu na son dukiyoyinsu fiye da
Allah da manzonsa shi yasa suka fada cikin bala’in da suke a yanzu. Saudia ce
kadai ta tsira a yanzu ba don komai ba sai don sanin kowa cewa algungumar
duniya, wato America, bata da wata kawa a waje sama da su, duk da cewa Allah ya
gargade mu da
Q5:51 “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku riki yahudu da
nasara a majibanta. Sashensu majibancin sashe. Kuma wanda ya jibance su daga
cikinku, to, lalle ne shi yana daga gare su. Lalle Allah baya
shiryar da mutane azzalumai”
A karshe ya kamata mu fahimta cewa tun fil azal Allah ya kasa
larabawa kashi uku, wato;
Q9:97 “Larabawa ne mafi tsananin kafirci da munafinci,
kuma su ne mafi kamanta ga rashin sanin haddodin abinda Allah ya
saukar a kan manzonsa”
Wadannan sune kafirai tsantsa kuma sun fi kowanne irin kafiri a
duniya kafirci. Sannan sai
Q9:98 “Kuma daga larabawa akwai wadanda su ke rikon abinda suke
ciyarwa a kan tara ce”
Wadannan sune wadanda gasu dai musulmi ne amma imani bai zauna
sosai cikin zuciyarsu ba (duba ayoyin sama Q49:14-15) domin halin kabilancinsu
na nan bai canza ba duk da umarnin Allah kuma basa ganin kowa da gashi tunda su
yan-na-gada ne kuma suna da izza a ransu ta ganin cewa duk abinda zasu yi wa
addini da dukiyoyinsu kamar tara ce. Sai kashi na karshe;
Q9:99 “Kuma daga larabawa akwai wadanda suke yin imani da Allah
da ranar lahira, kuma suna rikon abinda suke ciyarwa tamkar wadansu ibadodin
neman kusanta ne a wurin Allah da addu’o’in manzonsa…Allah zai shigar da su
cikin rahamarsa”
Wadannan sune wanda suka shiga musulci gaba daya kuma suka yarda
da cewa addini na Allah ne, kuma duk musulmi daya suke babu fifikon kabilanci,
sai dai wanda duk yafi wani tsoron Allah shine madaukaki. Don haka mu daina yi
wa larabawa kudin goro, mu ajiye su daidai da aikinsu cikin wadannan ajujuwa
guda uku da Allah ya fada mana. Duk balaraben da ke aiki da umarnin Allah da
manzonsa wannan abin tsarkakewa ne (daga fakon musulunci har tashin kiyama),
kamar yadda mu ka ga sahabbai da tabi’a da tabi’u tabi’in na kwarai sun yi,
amma wanda ke wa Allah shishshigi a addini ko gori ga annabi (SAW) da mabiyansa
kuma su ke kin yi hukunci da fadar Allah sai mu yi tir da su.
Comments
Post a Comment