Dabara Ta Rage Wa Mai Shiga Rijiya…

To, an dai gama zabubbukan cikin gida na jam’iyyu kuma kowa ya ga abubuwan da suka faru, amma ban sani ba, ko kowan ya fahimci abubuwan da ya kamata a ce mun fahimta. Na farko dai muna iya fahimtar cewa idan ka dubi dukkan jam’iyyu zaka gane cewa babu wani mahimmin banbanci a tsakaninsu yadda aka gudanar da zabubbukan fitar da ‘yan takara, domin dai idan ka cire takarar shugaban kasa a ACN da CPC, zaka fahimci cewa kudi ne yayi aiki ko karfin mulki wajen fitar da su, ba cancanta ba. Kuma ko a cikin ACN da CPC a zabubbukan gwamnoni da majalisu, kudin ya yi tasiri. Don haka me ka ke tsammani ga wadanda su ka ci takara kuma suka kai ga madafun iko?

Abubuwa da dama sun taimaka wajen tallafawa siyasar kudi, na farko a ganina muna iya zargar mutum biyu wajen haddasa wannan yanayi, wato Marigayi Janar Yar Adua da Janar Babangida. Dalili na shine, Babangida shine shugaba na farko da ya rika dunkule makudan kudade yana baiwa yan takara a jamhuriya ta uku domin su ci zabe. Sannan ya kafa jam’iyyu masu karfi ya tula musu kudade makudai. Shi kuma Janar ‘Yar Adua ganin cewa Babangida na nema ya yi kaka-gida cikin al’amuran siyasar kasar sai ya shiga debo kudi kamar kasa yana watsawa ‘yan siyasa, wanda hakan ya bashi damar kasancewa dan siyasa na farko, wanda ba bayarabe ba ne, da ya kame jihohin kudu maso yamma, Haka kuma ya kama kuri’u daga kowanne sashe na kasar nan. Wannan shine mabudin ido wanda ya  baiwa yan siyasa hasken cewa idan dai kudi zai sa wani dan arewa ya kwashe kuri’a daga yammaci da kudancin kasar nan, to, kowa idan yana da kudi zai iya. Wannan ya ba Abiola damar maimaita abinda Janar Yar Adua ya yi. Wannan shine ya haifar da siyasar kudi a kasar nan kuma ya ke ta habaka kawo yau. Cikin satin nan mun ga yadda Jonathan Goodluck ya yi gagarumar nasara wajen cinye zaben fitar da gwani na PDP. Farkon hawan Jonathan mulki, ina daga cikin mutane da su ka yi masa kyakkyawan zaton, ba don komai ba sai domin kasancewarsa wanda ba nema yayi ba kai tsaye, dora shi a ka yi, sannan kuma ya kasance matashi domin mun gaji da kewaya tsofaffin mutane a mulkin Nigeria wadanda basu da kishin kasa. Amma cikin lokaci kankane na sami canjin ra’ayi. Abu na farko da ya sa na dawo rakiyar jonathans shi ne matsalar Niger Delta, domin dai kowa ya ga yadda shugaban kasa ‘Yar Adua ya kwashe shekarunsa wajen kokarin afuwa da tattatunawa tsakanin yan ta’adda da gwamnati, yadda ta sa da dama suka aje makamai kuma matatun mai suka koma fitar da kusan ganga 500,000 wadda take salwanta sakamakon rikicin da yan ta’addar Niger Delta ke yi. Jonathan ya yi watsi da wannan wanda ya sa suka dawo da hare-harensu. Abu na biyu mun ga yadda zancen wutar lantarki ya zama kwata-kwata wannan gwamnati ta Jonathan ta yi watsi da shi. Babu wani wanda ke maganar farfado da lantarki a cikin wannan gwamnati. Ku duba yadda rikicin Jos ke ta muzanta, amma sai aka wayi gari cewa adadin yan sanda raguwa yake a garin maimakon a ce shine garin da ya fi kowanne a Nigeria yawan yan sanda.. Muna gani, yadda a farkon mulkin Jonathan aka sami gwamnoni na arewa wanda su ka yi zumbur wajen kalubalantar tsayawarsa takara. Cikin wadannan gwamnoni babu wanda ya yi azarbabi kamar Sule Lamido. Bana mantawa, mutane da dama sun yo ca wajen yabon gwamna Sule da wannan kokari nasa, ko da yake akwai wadanda na kwaba da saurin yin wannan azarbabi saboda sanin gwamna Lamido da na yi. Amma a yau sai ga shi har wasu malamai na zargin kalamansa da cewa ya yi ridda wajen fadar cewa gara Jonathan (Kirista) da Atiku (Musulmi)(Koda yake a matsayi na na malami ina ganin sun zafafa). Amma abin lura a nan shine mutane irinsu Sule Lamido da sauran gwamnonin arewa ba sa tunanin talakawa da makomar su face bukatunsu da na yayansu. Idan muka koma baya za mu iya gane dalilin da ya sa shi Sule ya fara adawa da gwamnatin Jonathan. Wannan adawa ta samo asali daga lokacin da Jonathan ya ki daukarsa a matsayin mataimakinsa ya zabi Namadi Sambo. Sule Lamido, ya dade ya na renon burinsa na zama mataimakin shugaban kasa, domin a lokacin Obasanjo su ne suka yi ta hura wutar gaba tsakanin Obasanjon da Atiku da tunanin cewa idan an tsige Atikun shi za’a ba mataimaki. Kwanan nan Sule ya shiga gidan rediyon Freedom a Kano inda aka tambaye shi saboda zargin ya na fifita ‘yayansa wajen bada kwangiloli a jihar Jigawa, ya kada baki inda ya ke gayawa duniya cewa “bashi da wani abu da ya wuce kyautatawa yayansa” kuma baya jin kunya a ce shi yana kare yayansa a gaban kowa. Kuma da alamu cewa irin wannan soyayya ce, ta sa aka tankwara shi ta amfani da yayansa, wato ta hanyar cuna musu EFCC har suka gano wasu kwangiloli da a ka yi ba daidai ba, kuma aka yi amfani da ita domin tursasa shi ya karyo daga adawa da Jonathan. Kwatsam sai aka wayi gari daga mafi adawa da Jonathan, ya koma na gaba wajen ganin cewa ya sami takara. Jama’a, wadannan fa su ne ake cewa shugannin alummar arewa? Idan har shugaba zai iya fitowa duniya ya yi adawa don son ransa, sanna cikin lokaci kankane ya koma kare abinda ya ke adawa da shi, kana zaton zai kare hakkokin al’ummarsa? Ko kuma ya cancanci a ci gaba da bashi amana? Duniya ta san cewa marigayi Abubakar Rimi shine ginshikin habakar siyasar Sule Lamido domin shine ya bada sunansa aka bashi bankin raya manoma lokacin Babangida, ya saka shi ya zama dan takarar gwamnan tsohiwar jihar kano sannan daga bisani ya sa aka ba shi sakataren jam’iyyar SDP na kasa. Amma a 1999 bayan kafa PDP, Rimi ya tsaya takara da Obasanjo amma Sule Lamido shine ja gaba wajen yakar takarar da marawa Obasanjo baya. A kurkusan nan mun ga yadda yayi ta fadanci wajen Saminu Turaki domin ya zama gwamna, amma yana bashi hadin kai daga baya sai da ya kori Saminu daga jam’iyyar. A zamanin mu, ba wani dan siyasa da ya dade yana neman ya zama gwamna kamar Sule Lamido (daga 1990-2007) amma da Allah ya cika masa buri me ya yi wa talakawan? Mutane na yaudarar kansu da cewa yana aiki, sun kasa fahimtar cewa Saminu yayi shekaru takwas bai yi wani aiki ba don haka ko me Sule yayi duk kankantarsa sai an ganshi.

Idan mu ka dawo kan Jonathan, duk wanda ya ga jawabinsa na bude jefa kuri’a, zai tabbatar da cewa ba shi da wani tsari don cetar kasar nan amma kamar yadda ya kwashe kuri’ar PDP don zama dan takarar ta, idan ba ‘a yi hattar ba wallahi zai maimaita a zabe shugaban kasa. Matukar wannan ta faru, to duk wanda ya kwana ya tashi a kasar nan sai yayi da-na-sani. Kuma ina tabbatarwa da shugabanninmu cewa da su zai fara. Domin ina kyautata zaton kasancewar Jonathan shugaban kasa na wasu shekaru, zai iya tabbatar da hasashen da ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta yi a 2005 wanda ke nuna wargajewar Nigeria daga nan zuwa 2015. Duk wanda ke nazarin siyasar kasar nan ya san cewa tun bayan yakin basasa bamu taba fuskantar kalubale irin na yanzu ba domin an farfado da kabilanci: muna ganin yadda ake raba sakon text cewa gwamnonin mu kamar kirista su ke saboda zabar Jonathan don haka a zabi Buhari. A daya bangaren kuma ana raba takarda cewa CAN tana kiran kiristoci da kada su zabi musulmi, da kuma wani na Dokubo Asari shima yana cewa karshen ‘yan arewa ya zo. Wannan abu yana da mummunan hadari domin zai iya wargaza kasar, ya kamata ‘yan Nigeria a wannan zabe mu daina duba banbance-banbancen mu na kabila da addini, mu duba abubuwan da suka hada mu waje daya na talauci, jahilci da zama karkashin mutanen da basu damu da ci gaban kasa ba sai nasu da na ‘yayansu.

Ina mafita? Mafitar ta dogara ga shugabanni da talakawa: shugabanni su tabbatar da cewa sun yi watsi da raben-raben su na jam’iyyu inda muke da mutane masu ra’ayin canji irinsu Pat Utomi, Buhari da Ribadu. Dole sai sun yarda su mara wa mutum guda a cikinsu tare da gagarumin taimako daga Babangida, Atiku, Gusau, da sauransu. Sanna su kuma talakawa su tabbatar da fitowa daga kowanne sashe na kasar nan su yi zabe ba don kabilanci ko addinin ba sai don su kori PDP daga mulki. Matukar PDP na mulki, zan iya rantsuwa cewa kasar nan ba zata sami ci gaba ba, kuma shekaru 12 da suka wuce sun tabbatar da haka. Duk gwamnatin da tayi shekaru 12 amma babu ci gaba sai dai ci baya, wallahi idan muka sake bari ta hau mulki to kada mu zargi kowa sai kan mu. Mu lura da cewa gwamnonin arewa Musulmi da na kudu kirista su suka yi tsaye wajen ganin Jonathan ya ci zaben fitar da gwani, don me a PDP babu kabilancin addini ko kabila? Domin bakin su daya wajen tauye talakawa musulmi da kirista. Wajibi ne talakawa su koyi yadda Kano, Lagos da Bauchi su ka yi a zabubbukan baya, wato na a tsare, a raka a tabbatar. Wallahi wannan zabe shine wanda zai tabbatar mana da canji ko kuma zama tsawon rayuwar mu a bauta tare da tara wa yayanmu matsalolin da ba zasu yafe mana ba. A karshe ya kamata mu lura da misalin Tunisia: Ni na zauna a kasar larabawa shekara guda kuma babu wanda ya fi balarabe tsoron mahukuntansa amma sai gashi an wayi gari sun fito, saboda kawai rashi aiki yi, sun kori Ben Ali daga kasar. Kada ku manta a Tunusia talaka yana cin abinci kamar yadda Gwamna zai ci a Nigeria, yana da asibiti, makarantu, sufuri ingantacce, wutar lantarki da abinci. Dabara dai ta rage wa mai shiga rijiya.

 

Comments

Popular posts from this blog

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

ALAMUN TSINUWA...

SARKIN KANO DA GWANINTAR IYA SUKA