PDP: SHEGIYAR UWA


2012

Mafi yawancin lokuta an fi samun shegen da fiye da shegiyar uwa, amma duk inda aka sami shegiyar uwa ka tabbatar ‘ya’ya da jikoki, da ‘yan uwa da surukai da makwabta, kai har ma da mutanen gari sun shiga uku. Hakika idan mutum yayi cikakken nazari na al’ummomin Nigeria da halayyarsu zai ce lallai mun yi babban dace da uwa.

A wannan lokaci da PDP ta cika shekaru 14 a duniya, idan muka bibiyi tarihinta zmu ci karo da gagaruman abubuwa da ta kawo ko kuma ta jaddada a wannan kasa tamu. Munafinci da son kais hi ya auro mana wannan uwa tamu. Domin dai manyan mutanen kasar da magoya bayansu ne suka yi gangami wajen daurin auren a matsayin waliyyanta. A matsayinsa na tsohon soja mai fada a ji, kuma mai tanadi da ganin cewa ya sake dare kujerar mulkin a karo na biyu, Janar Babangida, yayi wuf ya kawo Obasanjo domin ya zamar mata dan takara. Wannan yunkuri yana da manufa mai harshen damo; wato a rage wa Yarbawa radadin June 12, sannan a share masa fagen cimma wancan burin a dawowa (tunda dama da ya sauka cewa yayi, ya dan matsa gefe).

Obasanjo na hawa mulki sai yayi kokarin zazzage shugabancin PDP ya kawo ‘yan barandansa. Kafin ka ce kwabo, wannan jam’iyya ta zama wani gungu (cartel) irin na masu fataucin kwayo ko na ‘yan mafiya. Domin manufa guda aka sa a gaba: wato habaka tattalin mambobi ta kowane hli da kare muradunsu, sannan a kawar da duk wanda yayi kokarin kawo cikas. Na san dai bamu manta da irinsu Harry Marshall da Bola Ige da Chuba Okadigbo ba.

Daga 2011, bayan harin 9/11 a Amurka, sai mai yayi tashin gwaron zabi inda kasar ta fara samun mahaukatan daloli (wanda har yanzu ake samu). A kullum Nigeria na hakar gangar mai miliyan biyu da rabi wadda ake sayarwa a kan dalar Amurka 113, wato muna samun dala miliyan 282 a kullum. Kaga a duk wata muna samun dala biliyan 8.475 wato a shekara zai zama dala biliyan 101.7 kenan. Wannan daloli idan ka canza su zuwa naira zai baka Naira tiriliyon 16.272. Kada mu manta cewa kasafin kudi na 2012 Naira tiriliyon 4.5 ne kacal, wato kaso ¼ na kudin da aka samu na mai. Ya ilahi ina kashi ¾ na kudin da muke samu suke shiga? Haka nan a cikin kudaden kasafin kudin kansu, da kyar rabi zai isa ga talakawa. Abin takaici kuma sai talauci, rashin wuta lantarki, magani har ma da uwa uba, tsaro, suka kai matsayin da basu taba kaiwa ba a wannan lokaci. Shekaru 14 na PDP sun tabbatar da Nigeria a matayin kasar da aka fi zubar da jini duk da cewa ba cikin yaki take ba. Rayuka a kasar nan sun zama kamar na kiyashi, domin raina da naka da na dan majalisa ko minister bashi da wata kima domin duk wanda aka kasha babu abinda zai faru. Manyan barayi  kasar nan ‘yan PDP, mun ga yadda bayan kotu ta kama su da laifi ta tsare amma an yi gangamin tarbarsu tamkar jaruman yaki.

Duk wanda yayi wani namijin kokari don kawo canji ko yin gaskiya a PDP sai an yi waje da shi. A yau ina mazaje irinsu Sunday Awoniyi, Senator Matori, Isyaku Ibrahim, Abubakar Rimi, Nuhu Ribadu, El-Rufai da sauransu?

Kusan kowa ya yarda cewa Yar ‘Adua mutumin kirki ne kuma yayi iyakar kokarinsa, amma kasancewar dama an dora shi da masaniyar yana da ciwon da ba zai dade yana rayuwa ba shi ya sa aka bashi mulkin tare da tarnakin Jonathan. Kafin rasuwarsa yayi yunkurin ganin cewa ya mika mulki ga nagari daga arewa domin rade-radi sun nuna cewa ya kira Abubakar Rimi ya gaya masa cewar ya fara kanfen zai sauka ya bashi takara a PDP. Watakila tsoron faruwar hakan ya sa wasu suka saka ‘yan fashi suka tare Rimi a tsakanin Bauchi da Jigawa. Kanin Abubakar Rimi da direbansa da ke tare da shi, sun tabbatar ba a daki Rimin ba amma dai an caje jikinsa kuma daga nan ya fara tari wanda kafin a zo Kano ya cika. Duk da cewa ba a binciki gawar Rimi ba (wato autopsy) alamu na nuna cewar an shafa guba (radioactive poison) a fatarsa wadda tayi ajalinsa.

A yanzu matsalar Boko Haram ta yi mana katutu, kuma wannan matsala bata rasa nasaba da laifin da PDP tayi mafi muni. Wato kowa ya san kasar nan ta dade a dunkule ne sakamakon yarjeniyoyi da ba rubutattu ba. PDP karkashin jagorancin Obasanjo ta zuga Jonathan yayi watsi da tsarin karba-karba wanda hakan ya jawo abubuwan da suka faru bayan zabe 2011 har zuwa yanzu.

Ya kamata ‘yan Nigeria su tambayi kansu ina dalilin da duk sanda muka sami shugaba na kwarai baya tasiri? Murtala yayi wata shida, Buhari shekaru biyu da watanni, Yar’Adua shi ma shekaru biyu da watanni? Duk da cewa tun kafin a kafa PDP muke a lalace amma illar PDP ita ce ta zo assasa da karkafa da kuma tabbatar da dorewarmu a lalace. Kamar yadda wani gagarumin shugaban PDP ya ce zasu shekara sittin suna mulki, wallahi idan ba mu tashi tsaye ba sai sun yi dari. Duk kasashen duniya a yau ko dai sun ci gaba ko kuma sun kama hanya amma banda mu. Nijar dinnan da Ghana duk sun zarce mu a yau, haka nan kasashen larabawa, wadanda suka fi kowa tsoron hukuma, a yau sun zubar da jinni don kwato yancin su. Babban abin bakin ciki shine dama ta zo mana a 2011 yadda zamu yi namu juyin-juya-hali ba tare da ko lakuce hanci ba, wato ta hanyar zabe amma sai gashi an bi hanyar da aka saba ta kabilanci wajen raba kawunanmu. PDP ta sake darewa mulki, amma miliyoyin talakawan da suka rungumi kabilanci suka zabe su, kudu da arewa, a yau tare da kowa suke dandana azabar PDP. Wajibi ne mu gane cewa Allah ya bamu damar mu canza makomar mu ta hanyar zabo managartan cikinmu don su mulke mu ba tare da zubar da jini ko tashin hankali ba. Duk al’ummar da ta kasa zabo nagarinta don mulkarta, sai a ce Allah wadaran wannan al’umma.

A karshe, kasancewar yau shekaru 14 kenan muke kwankwadar azabobin PDP me ya kamata mu yi? Mu taya PDP murna ne ko kuma mu yi mata tir da ature?

·                     



 

Comments

Popular posts from this blog

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

ALAMUN TSINUWA...

SARKIN KANO DA GWANINTAR IYA SUKA