ALAKAR KWARONA DA ZANGA-ZANGA
Shekarar 2020 ta shiga tarihi a matsayin wadda ta fi muni a tarihin da
kimanin mutane kusan biliyan takwas da ke wannan duniya ba su taba ganin irinta
ba. Ba tare da harba bindiga ko tura sojoji ba, akasarin mutanen duniya, walau
masu mulki ko talakawa, matalauta da mawadata tamkar akuyoyi an tura mu cikin
gidajenmu na zama tamkar a kurkuku tsawon watanni. Hakika na yi imanin cewa wannan
annoba ta kwarona wata hanya ce da Allah ya nuna karfin ikonsa, ko mutanen
duniya za su saduda su rage dagawa da girman kai da kuma wa’aztuwa. Amma da alamu
duk darasin da cutar ta zo da shi ban ga alamun mun koye shi ba. A halin yanzu
bazuwar annobar kwarona a karo na biyu na ci kamar wutar daji a kasashen turai
da amurka, amma cikin ikon Allah ya kare mu yan Afirka, yadda yayin da kasashe
a Turai ke kokarin sake kulle kawunansu a gidaje, mu muna ta harkokin mu tamkar
babu ciwon. Idan ba Allah ba wa zai iya kare Afirka, nahiya mafi talauci da
rashin tsari na shugabanci mai adalci, daga wannan masifa?
A nan Najeriya ko a karon farko na
bazuwar wannan annoba ba ciwon ne ya fi yi mana illa ba irin yunwar da ta
haddasa. Yayin da kasashe ke fitar da tallafi iri-iri domin tallafawa mafiya
rauni a kasashensu ta hanyoyi daban daban, mu a nan Najeriya ba wanda ya kula
da talaka. Gwamnati ta garkame mutane ba tare da wani kyaykyawan tsari ba amma
kuma mawadatanmu sun rika mikawa gwamnati tallafin kudade maimakon su taimaki
mutanensu da abubuwan masarufi. A Kano, biyu cikin mafiya arziki a jihar sun
samar da cibiyoyin killace masu cutar kwarona maimakon su taimakawa talakawa da
abinci. A tsakiyar kullen yayin da matasa a wasu sassa na birnin Kano su ka
fara tare motocin abinci su na kwacewa, ni da kaina na yi wani sakon murya da
aka turawa matar shugaban kasa Aisha Buhari wanda bayan ta saurara a kasa da
sa’o’i 48 ta tura da kayan tallafin abinci na miliyoyin nairori birnin Kano,
kuma ba ta mika shi ga gwamnati ba, sai ta saka mutanenta su ka raba ga
talakawa kai tsaye. Amma tallafin da gwamnatin tarayya ta tura jihar Kano akwai
wadanda aka bari a waje har ruwan sama ya lalata wasu sannan kuma wasu aka boye
su a rumbunan ajiya.
Da langa, kuma a firgice talakawan
kasar nan su ka fito daga cikin kullen kwarona saboda tsananin wahalar da su ka
sha, amma cikin nutusuwa su ka koma kan ayyukansu domin neman abin sakawa a
bakin salati. Katsam a wannan yanayi na kokarin murmurewa yayinda wasu ma sun
rasa hanyoyin cin abincin su sai kuma gwamnati, a cikin sa’o’i 24 su ka sanar
da karin kudin man fetur da wutar lantarki. Tun da aka kafa kasar nan ba’a taba
ganin rashin tausayi da rashin imani da kuma nuna halin ko-in-kula daga
mahukunta irin wannan ba. Mutane sun yi watanni cikin masifu da matsi ba tare
da wani tallafi ba amma daga fitowa a sake matse su haka? Kuma a karshe zaka ga
cewa duk abinda za’a tatsi talaka zai bige ne wajen ci gaba da kasha dawainiyar
almubazzaranci mahukunta. A wannan gwamnati ne kasar nan ta karbi kofin zama
kasa wadda ta fi kowacce kasa a doron duniya yawan matalauta (kimanin mutane
miliyan 89 kafin annobar kwarona inda muka buge kasar India daga matsayin na
daya). Yanzu Allah kadai ya san yawan mutanen da su ka karu cikin wancan jeri
sakamakon yadda kwarona ta rusa ayyukan mutane da dama. Ana tsakiyar kwarona
gwamnati ta sake duba kasafin kudi na 2020 inda, maimakon ta rage shi sakamakon
kudaden shiga sun ragu, sai ta sake kara shi sama kuma mun san cewa a duk
shekara akasarin kason wannan kasafi na tafiya ne ga mahukunta da ma’aikatan
gwamnati inda kaso 40% ke zama kudaden gudanarwa na yau da kullum sannan kashi
25% ke tafiya wajen biyan basuka, sannan sauran kaso 35% din kansa ake yi kashe
mu raba da mahukunta da yan ayyukan da a ka ware na raya kasa. Wannan dalili ya
sa duk shekara ba’a ganin wani canji a rayuwar talaka bayan kasafin kudin domin
ba wajensu ya ke tafiya ba.
Idan za mu gaya wa kanmu gaskiya,
kowa ya san cewa ba wai fushin hukumar SARS ne kawai ya tunzura yan Najeriya
wajen yin zanga-zanga ba illa dai azabar matse tattalin arzikin talakawa da
hukumomi ke yi ce a gaba wajen wannan tunzuri. Koda yake dai akwai makiyan
gwamnati wadanda su ka so yin amfani da zanga-zangar domin kawowa gwamnatin
Buhari cikas. Amma daga gwamnatin har makiyan na ta basu fuskanci zanga-zangar
yadda ya kamata ba, domin sun raina irin matsi da fushin da matasa ke da shi.
Duk wanda ke hakilon juyin-juya-hali ta karfi tsiya a Nijeriya hakika ya manta
yadda kasar ta ke domin hakan ba zai haifar da komai ba illa rugujewar kasar
gaba daya domin babu fahimtar juna da hadin kai da za’a iya yin haka
salun-alun. Mu dubi kasar da ba ta da banbance-bance irin namu, wato Libya,
amma ta wargaje yayin da ta yi kokarin juyi da karfin tsiya. A lokacin da
matasan kuduncin kasar suka fito zanga-zangar matasan na arewa ba wanda ya
fito, ina dalili? Shin matasan arewa ba su fi na kudi zama cikin kunci ba? Duk
mai hankali zai gane cewa an yi amfani da bangaranci da addini abinda ya sa yan
arewa su ka ki shiga, musamman yadda aka rika nuna bidiyoyin Kanu da zantukan
inyamurai. Irin wannan dalili shine ya faru a shekarar 2011 yayin da yan arewa
su ka fito kone-kone bayan faduwar Buhari amma yan uwansu na kudu ba wanda ya
fita. Wallahi mu kiyayi duk ranar da yaran arewa za su yi zanga-zanga tasu ta
kansu, domin idan su ka yi ba wanda zai tsira saboda matsin da su ke ciki na
rashin ayyuka, shan kwayoyi da kuma fushi da mahukunta.
Ina ganin gwamnati da gangan ta ki
kallon hakikar matsalar da matasa ke ciki idan mu ka yi la’akari da jawabin
shugaban kasa bayan tarzomar matasa a kudu. Maimakon shugaban kasa ya lallashi
matasa ya amsa gazawar gwamnati na kula da halin da su ke ciki sai ya bige da
kurin cewa ba wata gwamnati a tarihi da ta fito da hanyoyin tallafawa matasa
kamar tasa. Hakika wannan gwamnati ta fito da tsare-tsare na tallafawa matasa
fiye da na baya amma magana ta gaskiya a suna su ke kawai domin ba sa kaiwa ga
hakikar wadanda aka nufa. Domin bayan jawabin shugaban kasa kadan sai ga matasa
a arewa (Kaduna, Jos, Tarab da Adamawa) su na ta balle rumbunan ajiyar kayan
abinci suna wawaso. Ya kamata shugaban kasa ya san cewa hakika akwai tsaruka
masu ma’ana irinsu na NIRSAL da gwamnatinsa ta samar amma a takarda su ke
kawai. Wannan tsari na NIRSAL shi kadai da ya na aiki wallahi sai an ga
tasirinsa domin tsari ne wanda zai samar da kudade ga matasa masu kwazo cikin
sauki yadda zasu iya kafa sana’o’i da masana’antu, amma akalla kimanin mutane
dubu dari shida ake tsammanin sun nema amma idan banda yan tsiraru kuma
shafaffu da mai kadai su ka samu. Shi kansa tsarin Ancho borrower ta bayyana
karara cewa asara ce ga gwamnati domin akasari ba hakikanin manoma ake baiwa ba
shi yasa kudaden basa iya dawowa. Don haka ya kamata gwamnati ta soke shi ta
kawo tsarin tallafin noma kai tsaye yadda manoma kadai ke iya cin moriya (samar
da iri, filin noma da taki a saukake). Tsarin tallafawa manoma ta hanyar daukar
hoton gonakinsu da aka yi a farkon wannan damina ga shi har daminar ta wuce ba
abinda aka yi. Kudaden trader-moni sun yi kadan yadda ba za su iya tallafar
sana’o’i ba(an ce da ka baiwa mutum kifi gara ka koya masa kamun kifin). Wato
duk da yawan tsare-tsare a gaskiya basa aiki kuma abinda zai kawar da matsalar
matasa shine a tabbatar da cewa ire-iren wadannan tsaruka dole a yi su a bude
yadda duk wani dan kasa da ya cancanta zai iya cin moriyarsu ba sai wadanda ke
kusa da yan siyasa ba. Ba wata kasa da za ta kai gaci idan kananan sana’o’inta
da masana’antunta basa samun hanyar samar da jari. Gwamnati ya kamata ta
tursasa bankuna su rika ba matasan da su ka cancanta basuka ba kawai su rika
jibge kudaden da aka sace ba, ba tare juya su ba.
Wasu na ta kokarin kare shugaban
kasa da cewa ba laifinsa ba ne laifin wadanda ya baiwa amana ne, duk wanda ya
fadi haka ya manta da cewa yan kasa ne su ka ba shi amana kuma ya zabi mutane
wadanda ya nuna cewa ya yarda da su dari-bisa-dari domin ba yadda ba a yi ba a
baya ya canza shugabannin hukumomin tsaro amma ya yi kemudugus. Don haka ko a
gaban Allah idan gwamnati ta yi nasara ko akasarin haka ba wanda za’a dorawa
face shi.
Kada mu manta da yan majalisunmu
wadanda sun kasance kadangaren bakin tulu domin duk da cewa kasafin kudinsu ya
ninka na fadar shugaban kasa kuma ba wanda ya san yadda su ke juya kasafin
nasu, amma duk da haka bayan sun lakume nasu kasafin idanuwansu kuma na kan sauran
hukumomin gwamnati. Mun ga yadda su ka yi watsi da binciken NDDC lokacin da aka
tasarwa tona musu asiri wajen badakalar kwangiloli. Haka nan da yadda su ka
kama fada da minister kan ayyuka da za’a ba matasa a kananan hukumomi 774. Daga
dukkan alamu mun baiwa kura ajiyar nama ne kawai.
Shawarata ga mahukunta da yan
siyasa shine su rage hadama da handama da babakere su karkata wani kaso daga
cikin arzikin kasar nan ga matasa, domin wallahi ita ce kadai hanyar da za ta
hana yin fito-na-fito da matasan nan ko ba-dade-ko-ba-jima. Duk wata
kwaskwarima sabanin hakan sai dai ya jinkirta zuwan wannan rana amma ba ya hana
ta zuwa ba. Wannan zanga-zanga da matasan kudu su ka yi kararrawa cewa a gare
su, duk ranar da yaran arewa su ka fito irin haka, zai wahala Najeriya ba ta
ruguje ba idan mu ka yi la’akari da yadda su ka yi a dalili na siyasa a 2011,
ba a dalilin yunwar cikinsu ba. Duk wanda ka kai bango ba shi da zabi illa ya
turo ka baya. Allah ya bamu ikon ceton kan mu da kanmu kafin lokaci ya kure.
Comments
Post a Comment