BADAKALAR GANDUJE

                                  

tarihin badakalolin cin hanci a Nigeria tun daga lokacin turawan mulkin mallaka, kama daga badakalar Firayin Ministan jihar gabas, Dr. Nnamdi Azikwe, ta Bankin ACB a shekarar 1957, ko kuma ta rahoton Kwamitin Coker a shekarar 1962 wadda ta kama tsohon Firayin Ministan jihar yamma, Obafemi Awolowo, da hannu a badakalar cin hanci, kai hatta ta shekarar 1975 lokacin da Murtala ya kama gwamnoni goma da hannun a cin hanci, ba na tsammanin muninsu ya kai na kwanan nan wanda aka dauki hoton bidiyon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya na cusa daloli a babbar rigarsa. Ganduje ya lakabawa kansa suna “Khadimul Islam” wato jagoran hidimtawa addinin musulunci amma duk da haka bai iya yin murabus daga mukaminsa a mutunce ba sakamakon badakalar. Wannan abin kunya da ya yi, ba kansa kadai ya tsaya ba, abu ne wanda ya taba kimar musulmi da musulunci da al’ummar jihar Kano. Amma abin takaici, a garin da ke ikirarin addini sai ga shi banda malami guda da ya zama zakka, wato Sheikh Ibrahim Daurawa babu wanda ya iya fitowa ya nu na ba daidai ba ne. Shi ma da ya yi kiran ayi bincike tsakani da Allah, sai ga shi an yi masa ca a kafafen sadarwa da watsa labarai kamar za’a cinye shi danye.

Tsit ka ke ji daga yan siyasa, sarakuna, attajirai, yan boko da malamai game da wannan badakala. Wani Babban abin kunyar ma shine yadda wani gungu na malaman Izala karkashin jagorancin shugabansu na Kano Abdullahi Pakistan, su ka yi takanas-ta-Kano su ka yi wa gwamna mubayi’a ta goyon baya game da karbar cin hancin. Shin wai kuwa Kanon da na taso ce a ciki wadda ake wa ikirarin “Ko da me kazo an fika?”. Ban jin mun cancanci ci gaba da karbar wannan take a yanzu.

A lokacin da Jafar Jafar ya saki wadannan faya-fayen bidiyon, sai majalisar jihar Kano, kamar gaske, ta kafa kwamitin bincike inda ta fara da kiran dan jarida Jafar Jafar, wanda ya rankayo zuwa birnin Dabo rataye da Quraninsa a kafada domin ya bada shaida. Kwamitin ya gayyaci Ganduje ya zo domin shi ma ya kare kansa, amma saboda alamu na rashin gaskiya sai gwamnan ya kauracewa gayyatar sannan ya garzaya kotu da neman ta hana majalisa ci gaba da binciken gaba daya. Hausawa dai na cewa “Ciki da gaskiya, wuka ba ta huda shi”. Amma abinda mutane ba su gane ba shine cewar ita kanta majalisar da ma ba da gaske ta ke yi ba. Domin dai na farko sun san cewa za’a iya amfani da kotu a hana su bincike, kuma hakan ne ya faru. Sannan da majalisar da gaske ta ke, su na da hanya da tsarin mulki ya ba su dama wadda ba wata kotu a Nigeria da zata iya karo da wannan tanadi. Karbar cin hanci na cikin manyan laifuka da majalisa na iya amfani da sashen tsige masu mulki bi sa aikata laifi. Me ya hana majalisar fara shirin tsige gwamna, tsarin da doka ta ba su dama wanda zai basu damar saka Babban jojin jiha ya kafa kwamiti na mutane 7, wadanda fitattu ne ma su kima a al’umma kuma wadanda ba su fito daga bangarori na siyasa, ko na gwamnati ko kuma majalisa ba, wato yan baruwanmu. Wannan kwamiti idan an kafa shi babu wata kotu da ta isa ta soke shi saboda hurumin kundin tsarin mulki ne ya ba majalisa wannan dama. Kwamitin zai yi aikinsa ya mikawa majalisa wadda zata karasa aikinta ta yadda ko dai ta tabbatar da laifi ta tsige gwamna ko akasain haka sakamakon kuri’a da yayanta za su jefa. Maimakon haka sai majalisar ta dauki waccan hanya wadda aikin yan sanda ne ko hukumar EFCC, da sanin cewa kotu na iya dakatar da su.

Sakacin Buhari shi ma ya yi tasiri sosai wajen shashantar da wannan badakala saboda kasancewar ya ki saka hannu ko ya tilasta jam’iyya ta shigo ciki. Amma a fili ya ke cewa lokacin yakin neman zaben APC a Kano, ka na kallo Buhari ka san cewa ya saka kansa a tsaka mai wuya domin dai a karshe cewa ya yi da mutanen Kano “Ga Gandujenku” wato a fakaice ya na nuna cewar ya rage ga masu jefa kuri’a su zabi Ganduje ko su kore shi daga kujerar. Hakan ya dada fitowa karara saboda bayan kwana daya da barin Buhari Kano, sai ga shi hukumar EFCC ta saki rahoton cewa ta gama bincikenta kuma ta tabbatar da cewar Bidiyon Gandujen na gaske ne ba harhadawa a ka yi ba.

Ofishin shugaban kasa da na jam’iyyar APC sun gaza daukar mataki a kan Ganduje saboda tsoron kada su rasa kuri’a a zaben shugaban kasa. Amma kuskuren lissafin da su ka yi shine cewa, da sun dauki mataki a kan Ganduje da lallai ne sun tabbatar wa da duniya cewar yaki da cin hancin da gaske su ke, ba kamar yadda yan adawa ke ikirarin cewa sai a kan su ya ke aiki ba. Sanna za su iya tilatawa Ganduje ya yi murabus su ba mataimakinsa Nasiru Gawuna takarar, wanda ta haka zai kara wa gwamnatin tarayya farin jini kuma kowa ya san cewa ba wanda ya wuce doka. Yin haka zai kara musu farin jini da samun kuri’a a Kano. Mulki ba don mutum guda a ke yin sa ba, kuma babu wanda ya wuce doka.

Magana ta gaskiya, laifukan Ganduje sun wuce maganar cin hanci kawai, Kano ba ta taba samun Gwamna koma baya kamarsa ba. Zan bada hujjoji. Na farko mulkin Kwankwaso a karo na biyu, ya nuna wa kowa cewa hakika gwamnoninmu idan al’umma su ke so su na da hanyar kudade da za su iya yin ayyukan raya kasa masu mahimmanci. Ba wanda ya taba zaton kudaden da ake samu za’a iya yin ayyukan da Kwankwaso ya yi a shekaru hudu. Duk da cewa shi kuma kwankwason ya yi ayyukan ne domin kawai ya na neman takarar shugaban kasa. Sannan kamar yadda Obasanjo ya kakaba mana Jonathan haka Kwankwaso ya kakaba wa Kanawa Ganduje saboda gudun kada ya rasa kuri’ar delegates din Kano a fidda yan takara tsakaninsa da Buhari a 2015. Ya fi kowa sanin Ganduje da barnar da zai iya aikatawa.

Ganduje bai yi kasa a gwiwa ba saboda maimakon ya na hawa mulki, ya yi kokarin samar da kujeru da tebura da kayan karatu a sabbin azuzuwa sama da 800 na makarantun firamare da Kwankwaso ya gina sai ya yi watsi da su. Duk da cewa Kwankwaso ya kirkiro makarantun koyar da sana’o’i sama da ashirin, ya kamata a ce Ganduje ya zabi a kalla wasu daga ciki ya tabbabtar da su saboda al’umma na matukar bukatarsu, kamar makarantar fim ta Bagauda, da ta koyar da aikin tsaro, da na unguwar zoma da ire-irensu. Kwankwaso ya tura dalibai kasashen waje wadanda wasu a lokacin da Ganduje ya zo saura shekara guda su kammala karatunsu, amma sai gashi gwamnati ta ki biya musu kudaden jarrabawa da na rike kai. Ya ilahi ya gwamnati zata kashe kudade tsawon shekaru uku a kan dalibai a bari karatunsu ya lalace a shekarar karshe? Ai ko bashi a ci. Mun ga yadda Ganduje ya yaudari kanawa wajen yin zaben fid-da-gani nay an takarkarun APC, ya zabi tsarin kato baya kato amma ya zauna a gidan gwamnati ya na cewa yan takara ga wanda su ka zaba.

Tashin farko, Ganduje, saboda raina tunanin mutanen Kano sai ya ke tsammanin cewa idan ya rike Buhari sau da kafa, sannan ya yi mana Gadojin mota shikenan ya siye mu. Ya na karbar mulki ba abinda ya mai da hankali irin aikin gada. Sannan wani abin takaici, sakamakon badakalar daloli wai har a yawon kamfen sai a ce “Baba ka ci bulus” sai ya daga hannu. Ban taba ganin inda dan siyasa ya ci zarafin al’umma irin wannan ba. Laifi ya zama abin kamfe? Wace irin al’umma ce wannan?

Duk wanda ke bibiyar tarihin siyasar Ganduje ya san ya yi abinda a ke cewa “Mage mai kwanciyar daukan rai”. Tun a shekarar 1999, bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati Ganduje ya faso fagen siyasa da mahaukatan kudade. Ya shiga takarar gwamna ba a sanshi ba sai ga shi ya zama kadangaren bakin tulu, saboda watsi da kudi da ya rika yi a tsakankanin delegates da shugabannin jam’iyyar PDP na wancan lokaci. Kafin ka ce me, ya hargitsa takarar yadda ba shiri a ka yi yarjejeniyar a ba shi mataimakin gwamna a bar Kwankwaso ya yi gwamna saboda ya fishi gogewa da kuma sanin mutane a siyasa. Wannan abin da Ganduje ya yi shine ya fara saka dan ba a fagen siyen delegates da mai da siyasa ta kudi a jihar Kano, domin da kudinsa ya sayi kujerar mataimaki.

Ganduje cikakken dan jari hujja ne, kuma shekarunsa 15 yana burin Allah “Ya kai damo ga harawa”, wato kujerar gwamnan Kano. Babu irin wulakanci da bai jura a wajen Kwankwaso ba, amma ya hadiye har ya cimma burinsa. Kamar yadda abubuwa su ka nuna, Babban burin Ganduje shine cika aljihunsa kamar yadda hotunan bidiyo su ka nuna. Sannan ya na hawa ya jajubo aikin jirgin kasa daga Bata zuwa Dawanau wanda zai lakume dala biliyan $1.2 (sama da naira biliyan 400) a lokacin da babu isasshen ruwa sha a cikin birnin Kano. Sukar wannan aiki da Sarkin Kano Sunusi Lamido ya yi a gaban manyan arewa a taron kasuwanci na Kaduna, ya yi matukar tasiri wajen kashe wannan aiki yadda ya nuna al’umma ba ta bukatar wannan aiki. Mutuwar aikin ya janyo wa Ganduje asara ta kimanin naira biliyan 300, wato kimanin kashi 25% da yan kwangila ke ikirarin ya kan karba na cin hanci kafin bada aiki. Ganduje ya juyar da fushinsa ga Sarkin Kano yadda ba don shiga tsakanin wasu gaggan yan Arewa ba, da tuni tarihi ya maimaita kansa a masaurata, wajen tilasta shi murabus kamar kakansa. Ganduje ya samar da kamfunan karbar haraji da suka addabi masu sana’o’i cikin birnin banda yanka duk wani dan fili da za’a iya yin shaguna da ke kwaryar birnin Kano. Hatta filin idi bai tsira ba an maida bangarorinsa shagunan kasuwa. Sauran makonni da zabe Ganduje ya sake fito da wani tsarin na yin wata gadar da zai lakume naira biliyan 15 (25% kuma ya shiga babbar riga), saboda a tunaninsa rike hannun Buhari da yiwa Kanawa gada kadai zai ba shi zabe. A tarihin mulkin a Kano ba’a taba samun wanda ya bar matarsa ta shiga harkokin mulki kai tsaye kamar Ganduje ba, yadda hatta Kwamishinoni, yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati ke kai mata caffa kafin wani abu ya faru yadda su ke so. A matsayin Khadimul Islam yar sa ta keta haddin addini da na al’ada wajen daukar hotuna na batsa kafin aure amma ko gezau bai yi ba balle nuna nadama. Duk abubuwa na amfani da addini da cutar da jama’a irin wadda gwamnatin Shekarau ta yi na bawa malamai (musamman na Izala) da masaurata kudade na cin hanci domin toshe bakinsa shi a ke yi a yanzu.

Hakika, alamu sun tabbatar da cewa Ganduje ya raina siyasar Kano da masu jefa kuria. Amma ina son tunatar da mutane cewa siyasar Kano ta wuce yadda a ke zaton ta domin a baya mun ga yadda aka kwace mulki daga hannun gwamnoni biyu da su ka fi kowa farin jinin jama’a a lokacin su na kan kujerar mulki. A shekarar 1983, gwamnan da ya fi kowa farin jini wato Abubakar Rimi, saura wata uku zabe ya mika wa mataimakinsa kujera ya fita kamfe amma sai ga shi Sabo Bakin Zuwo ya kayar da shi a zaben. Sannan Kwankwaso a shekarar 2003, duk da cewa yana kan kujera ga kuma karfin gwamnatin tarayya amma sai ga shi wani wanda ba’a sani ba a siyasa, wato Malam Ibrahim Shekarau, ya kayar da shi. Idan mu ka koma can baya a shekarar 1990, duk da cewa SDP ke da rinjaye a jihar Kano, kuma Magaji Abdullahi ne dan siyasa mafi farin jini a wannan lokac,i sai ga wani sabon dan siyasar a jam’iyyar adawa, Kabiru Gaya, ya dare kujerar gwamna. Babban abin burgewa a dimokuradiya shine damar da masu jefa kuri’a ke da ita wajen korar duk wani shugaba da basa so, kuma tarihi ya nuna cewa Kanawa sun goge a baya da yin amfani da damar su. Idan mu ka sake mu ka yi watsi da wannan dama hakika siyasar mu ta mutu. Kada mu manta a Lagos an wayi gari saboda gwamna ya kaucewa kudurin ci gaban shekaru da su Tinubu su ka aza ya jawo an hana shi tsayawa takara kuma ya hakura bai bar jam’iyya ba, kuma mun san cewa zunubinsa bai kai na Ganduje ba. Kano ce ta fara nuna wannan a 1983 wajen kada Abubakar Rimi. Yadda alkalumma siyasa su ka tabbatar a Nigeria, siyasar da ke mulki ko adawa kadai ke iya cin zabe a sama ko a kasa, don haka Takai kasancewar ya shiga karamar siyasa, zai wahala ya iya cin zaben gwamna duk da cewa a yanzu yafi kusan kowanne dan takara alamun cancanta. Duk da cewa ita kuma PDP an dawo daga rakiyarta saboda gazawarta, Dan takararta, Abba Kabir sakamakon karanci shekarunsa da kuma irin abubuwa da ya yi a baya da kuma alkawuransa, watakila kanawa su ba shi dama. Idan zai iya kauracewa son rai irin na Kwankwaso ya yi aiki yadda ya alkawarta, hakika zabensa zai iya kawo wa Kano canjin da ta ke nema a yanzu, domin duk wadanda a ka gwada a baya sun gaza. Kuskuren da Kanawa su ke yi ayanzu shine kasancewar kowa ya nade hannu ya bar abubuwa su faru yadda su ka zo. Babu kuskuren da al’umma za ta yi da ya wuce kyale kowanne kare-da-doki darewa mulki, dole maus fada a ji a Kano su tashi haikan wajen yi wa jihar tunani da dora ta bisa turba. Muna ganin yadda Tinubu ya saita Lagos, ga shi nan kullum sai gaba-gaba su ke yi. Kwankwaso ne ya cancanci ya zama mana kamar Tinubu a Kano, amma saboda son rai irin nasa da kasa gane Allah ya yi masa kebantacciyar ni’ima, ya yi watsi da damarmaki da Allah ya ba shi. A Dimokuradiya, lokacin zabe shine lokacin hisabi, mun ga yadda mutanen Kwara su ka fatattaki Bukola Saraki daga majalisa, amma kuma mutanen Bauchi su ka maida Yakubu Dogara majalisa saboda sun gamsu kuma an tabbatar ya kula da mazabarsa. Wajibi Kano mu fito mu sami canji, domin ita ce hanya daya ta jan kunnen yan siyasa su rika abin kirki idan an zabe su. Badakalar Ganduje ta zubar da mutunci Kano da Kanawa, wajibi mu yi wa kan mu hisabi da kuri’unmu a ranar zabe.

 

 

 

 

 

Comments

Popular posts from this blog

ALAMUN TSINUWA...

Dabara Ta Rage Wa Mai Shiga Rijiya…

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?