DANGOTE NA KUKAN KARYA
A duk fadin Nigeria ko ma ince a arewacin Afirka babu wasu iyali da Allah ya albarkantaka da arziki irin iyalin gidan Alhassan Dantata. Domin a zamaninsa, Alhassan Dantata ya kasance mafificin attajiri wanda ba kamarsa a fadin arewacin Afirka. Cikin yayansa da su ka gaji arzikin kuma su ka shahara su ne Aminu Dantata da Sunusi Dantata, wato kakan Aliko Dangote ta wajen mahaifiyarsa Mariya Sunusi Dantata. Gidan Sunusi Dantata ya shahara da samar da hamshakan attairai inda aka fara da marigayi Usman Amakka wanda a shekarun 1980 ya kasance dan kasuwar da ya fi kowa arziki a fadin Nigeria. Ba domin harbinsa da wasu yan bindiga wadanda ba’a san ko su waye ba, abinda ya jaza masa mutuwar sassan jiki yadda sai a kujerar guragu ya karasa rayuwarsa, watakila da shine zai zauna matsayin da Dangote ke da shi a yanzu. Wani hamshakin attajirin daga gidan Sunusi Dantata shine marigayi Abdulkadir Sunusi Dantata mai kamfanin Dantata & Sawoe wadanda suka yi shura wajen gina tituna a fadin kasar nan. Aliko Dangote ya kasance attajiri na baya bayan nan da ya fito daga tsatson Sunusi Dantata.
A kididdigar attajiran duniya a yau Aliko Dangote ya kasance attajirin da ya fi kowa kudi ba kawai a Afirka ba, a cikin dukkan attajirai bakaken fata kuma shine na 136 a jerin attajiran duniya gaba daya. Arzikinsa ya kai gaya matukar gaske. A makon da ya gabata kungiyar dattawan Kano da ake ma lakabi da KCCI ta yi wani taro a jami’ar Bayero ta Kano domin lalubo hanyoyi na rage radadin talauchi a jihar inda Aliko Dangote cikin bayaninsa ya ke cewa “Akwai yiwuwar nan da shekaru biyar matasan jihar Kano za su iya hana manyan jihar fita ko da kofar gida ne, saboda barazanar da za su iya zama”. Kafin ya yi wannan bayani, a farkon wannan watan ma, attajirin ya kalubalanci gwamnonin arewa da su tashi tsaye wajen magance talauci a yanki, inda ya nuna cewa kashi 60% na jama’ar wannan yanki na arewacin Nigeria na cikin matsanancin talauchi, duk da cewa yankin ke da kaso 70% na fadin kasar da kuma kaso 54% na yawan jama’a, amma harajin da yankin ke iya samawar bai wuce kashi 21% ba daga cikin wanda kasar ke samarwa. Ya nuna takaicin cewa yankin na da albarkatun noma da zai iya kawar da talaucin jama’a amma an kasa cin moriyar hakan.
Abin tambaya a nan shine, shin me Dangote zai nuna na azo-a-gani wanda zai tabbatar wa da mutane cewa wadannan maganganu na sa da gaske ya ke? kuma me ya yi a baya? Kafin na lalubo wadannan amsoshi zan ja hankali masu karatu domin gane yadda tsarin tallafi ya ke a addinance da a zamanance. Kamar yadda kowa ya sani shi arziki Allah bai taba baka shi domin karan kan ka ba kawai, duk inda ka sami kanka da wata wadata, ka sani cewa ka zama wata sila ne ta raba wannan ni’ima da Allah ya yi maka. Dalilin haka Allah ya wajabta zakka da assasa kyauta da sadaka. Dole ka fitar da zakka domin taimakawa talakawa a al’ummar da ka ke ko kana so ko ba ka so matukar kai musulmi ne. Mahimmancin zakka ya fito karara a lokacin Sayyidina Abubakar wanda ya rika yakar musulmai wajen kwato zakka a hannunsu domin rabawa talakawa. Mutane da dama a duniya na mamakin yadda Yahudawa su ka zama al’umma mafi wadata a doron duniya. Sirri guda da mutane ba su sani ba game da Yahudawa shine a tsakaninsu ba sa wasa da zakka. A lokacin da aka fafare su daga turai zuwa Amurka sun kasance sun yi sansani a New York inda su ka aje wakilansu a bakin kogin Hudson wanda ya zama mashiga zuwa Amurka. Duk lokacin da wani bayahude ya iso daga turai, yan’uwansa za su tare shi kuma abu na farko da za su nema daga gurinsa shine ya fitar da zakka wadda za’a saka cikin baitulmali tun kafin ya sami inda zai zauna. Nan take zai bayar idan kuma ba shi da kudi sai a tambayi irin sana’ar da ya goge da ita sannan a saka shi koyar da wannan sana’a ga wani bayahuden a matsayin zakkarsa. Duk kudaden da su ke tarawa na zakka da shi su ke tallafawa masu rauni a cikinsu domin su sami ilimi ko gogewa a wata sana’a. Ba za ka taba ganin bayahude a kowacce irin kaskantacciyar sana’a ba a Amurka domin kowa sai ya sami ilimi ko an koya masa sana’a mai daraja. Duk da cewa ba su fi miliyan 15 a duniya ba, amma su ke da adadi mafi yawa a cikin gwarzayen masu ilimi da ke lashe lambar Nobel a duniya kuma su ka fi kowa yawa a hamshakan attairai na duniya, abinda ya ba su damar mulkar manyan kasashen duniya irinsu Amurka. Yanzu haka cikin wadanda su ka fi kowa bada zakka a duniya Yahudawan Amurka ne domin Zuckerberg (mai Facebook) ya bada dala biliyan 1.6, wato kimanin kaso 4% na arzikinsa (Dala biliyan 40) sannan shi ma wani hamshakin Bayahude Micheal Bloomberg ya sadaukar da kimanin kashi 8% wato dala biliyan 3 cikin arzikinsa (Dala biliyan 37). Wannan dabi’a ta addini da Yahudawa su ka rike wadda ta ba su damar cire al’ummarsu daga talauci, ita ragowar turawa su ka kwaikwaya. Sabanin yadda Yahudawa ke tallafar duk wani Bayahude domin tsame shi daga talauci, sai turawa, musamman hamshakan masu arziki su ka rungumi ba da tasu zakkar wajen tallafawa harkokin ilimi, binciken kimiyya ko nemo maganin wata cuta. Jami’ar da ta fi kowacce shahara a duniya yanzu, wato Havard da kuma jami’ar Stanford da ke Amurka duk daga kudaden zakka na masu kudi a ka samar da su.
A sani na, a shekarun baya Aliko Dangote ya yi kokarin raba zakka ta kudi ga talakawa, musamman wadanda ke kewayen unguwarsu ta Sarari da ke birnin Kano (inda nan a ka haife ni na taso). Amma tun daga mutuwar kakansa Sunusi Dantata wannan zakkar ta daina zuwa wajen talakawan unguwarsu yadda ake yin ta a baya. Amma kafin sannan ma, akwai wani lokaci da marigayi Dr.Abdullahi Bature ke shugabantar gidauniyar Dangote na taba zuwa ofishinsu na yi hira da manaja na wannan lokaci inda a hirar zakkar ya sanar da ni cewa abinda ya sa ake samun tsaiko wani lokaci na bayar da zakkar saboda bayan an kididdige kaso 2.5% da ake cirewa domin yin zakkar, a kan dauke wannan kaso a saka a asusun ajiyar da babu zara (Fixed Deposit) na wani lokaci yadda kafin wannan lokaci ajiyar ta samar da kudin ruwa mai gwabi, sai kawai a kwashe kudin ruwan a zo a raba zakkar sannan a mayar da ainihin kason 2.5% cikin uwar kudi. Sunusi Dantata na mutuwa a ka daina rabawa talakawan unguwar zakkar, amma an ci gaba da raba ta ga ma’aikatansa.
A maimakon assasa zakka, sai Dangote ya assasa almajiranci domin ya baiwa mahaifiyarsa damar ciyar da talakawa tuwo a kullum. Yanzu haka idan ka je kofar gidanta zaka tarar da tsoffi maza da mata da yara sun tare a wurin saboda abincin rana da na dare da ake basu. A matsayin Dangote ya ci a ce ya gina jami’arsa a Kano, da samar da asusun tallafin karatu, da kuma saka jari a harkokin noma da wasu mahimman masana’antu yadda ayyukan yi za su bunkasa a jihar Kano. Kamar yadda Bahaushe ke cewa ne Dangote kukan karya ya ke yi game da rashin aikin yi ga matasa a jihar Kano domin ya je jihar Lagos ya na gina matatar mai, wadda ke cikin mafi girma a duniya da zata lakume Dala biliyan 12. Ya na da katafaren kamfanin sumunti a Obajana da Benue. Ya saka kudade masu yawa wajen noman shinkafa a jihar Jigawa da Katsina. Ina dalilin da ya kasa saka jari a Kano? Jigawa da Katsina ba su kai kano albarkatun ruwa ba, domin a Kano akwai kimanin Dam-Dam sama da 16 da za’a iya yin noman alkama da shinkafa fiye da ko’ina a fadin Nigeria. Wani Abokina ya nemi bani hujja da cewa Dangote na tsoron saka kudinsa a Kano saboda kada a cinye masa. Wannan ba haka ba ne domin sama da shekaru 20 Dangote ya saka kudade a kamfanin fulawa wanda ya dauko wani Ba’indiye kuma har yau kamfanin ya na aiki tare da samar masa da riba. Duk kamfunan da ake zato na Dangote a Kano ba nasa ba ne, wato irinsu Dansa, Danhydro, Dangote Farms, Dangote Textile dukansu kamfunan kaninsa ne Sani Gote wadanda ya murkushe su da kansa abinda ya jawo sunansa shiga cikin mutane da aka wallafa sunansu sakamakon katutu na bashi. Kimanin shekaru shida tare da hadin kan gwamnatin tarayya sun samar da kamfanin matse tumatir a chiromawa wanda ya kasa fara aiki saboda gazawa wajen iya biyan manoma hakkinsu yadda ya kamata su samar da tumatirin.
Abin akwai daure kai ganin yadda Dangote ya kasa tallafawa mahaifarsa wajen saka jari domin bunkasa arzikinta. Ya kasa fitar da hakkin Allah na zakka ko yin sadaka ta tallafin karatu amma sai ya je jami’a ya yi ginin azuzuwa ko dakunan kwana, kuma akasari ma a wasu jihohin. Gina al’umma ta hanyar samar da ilimi da aikin yi shine hakki na farko da ya rataya a kan wanda duk zai iya bada gudunmuwa ba wani gini wanda za’a kalla kawai a ce ai wane ne ya gina ba.
Wallahi maganar Dangote gaskiya ce cewar nan da wani lokaci matasa za su hana manya fitowa a Kano, domin hujjoji da su ka bayyana yadda ake garkuwa da mutane ya nuna cewa ba wanda zai tsira daga bala’in da muke Tarawa kan mu. A yau akwai yara almajirai sama da miliyan 10 a arewacin Nigeria, wato kimanin kashi 10% na daukacin al’ummar yankin, wadanda ke gararamba ba ilimin addini balle na boko sannan sun taso ba su san mecece soyayya ta iyaye ko al’umma ba, gaya min dalilin da za su tausaya wa wani? Munga yadda aka kassara arewa maso gabas da Boko Haram yanzu kuma ana kokarin kassara arewa maso yamma. Idan muka zuba ido har lokacin da samarin Kano su ka rungumi daukar hanyar ta’addanci, wallahi arewa ta tarwatse Kenan, sai mun koma kamar, ko ma fiye da Libya. Wajibi a tashi tsaye wajen samar da ayyukan yi ga matasa, ita ce kadai mafita. Samarinmu na tasowa babu ilimi kowanne iri, babu tarbiya da tsoron Allah don haka ko ba su yi shaye-shaye ba wallahi babu abinda ba za su iya aikatawa ba. Noma kadai zai iya cetar arewa idan akwai jari da ilimi na zamani.
Na yi takaicin siye ginar Songhay ta Dutesn-Ma a jihar Katsina da Dangote ya yi da zummar yin shinkafa. Dalili kuwa shine zai iya zuwa ko’ina ya yi noman shinkafa amma wannan gonar babu irinta a arewacin arewa, kamata ya yi a ce ya assasa ta domin irin ilimin da wannan gonar zata bayar zai canja akalar noma gaba daya a arewa da an yada shi. Na yi yawo iya gwargwado amma ban taba shiga wani waje da ya dimauta ni ba irin wannan gonar saboda sun zo da ilimin da zai iya sa manoma su daina amfani da takin zamani, da maganin feshi na kwari da samar da tumatiri wanda zai iya sati biyu a waje bai rube ba sannan ya ninka yabanya sau takwas akan wadda aka saba me amfani da takin zamani.
Don haka maimakon wancan kuka da Dangote ya ke, kamata ya yi ya ware Dala biliyan Daya, ba cewa mu ke ya yi zakka ko sadaka da ita ba, a’a ya saka jari a harkar noma na zamani a jihar Kano. Mun ga yadda jihar Kebbi cikin lokaci kankane ta tallafa wajen rage shigo da shinkafa kasar nan. A wannan dala biliyan daya Dangote na iya samar da manyan gonaki na alkama da shinkafa a gefunan dam-dam sama da 16 da mu ke da su a Kano sannan ana iya yin burtalai na zamani (Ranches) yadda makiyaya za su daina yawace-yawace kuma a samar da kudaden shiga da ayyukan yi, shi kuma Dangote ya sami gwaggwabar riba. Idan ba’a fara rarraba arzikin kasar nan ga matasa ba, wallahi tallahi sai kowa ya gagara sakewa cikin kasar. Aiki ne da kowa zai bada tasa gudunmuwa, idan kowa ya ki kuma to akwai ranar biya wadda idan ta zo mai kan uwa da wabi ce!

Comments
Post a Comment