INA MA DAI…


Hankalin yan Nigeria da ma na kasashen duniya ya koma kan zaben watan afrilu saboda mahimmancinsa ga kasar da ma duniya gaba daya. Dalilai da dama sun saka wannan zabe ya fi kowanne mahimmancin a tarihin wannan dimokuradiya tun daga 1999. Da farko dai kowa ya ga irin guguwar Canji da take kadawa a kasashen arewacin afurka saboda talakawa sun fara gajiya da irin mulkin kama-karya da shugabanni ke yi. Zaben 2007 ya zama matattara ta magudi, sannan mutuwar Yar Adua ta kawo wani yanayi mai wahala kan tsarin bangaren da ya cancanci mulki.

Idan muka kalli wadannan matsaloli, zamu fahimci cewa kamar yan uwanmu na arewawacin afurka, duk da cewa basu da matsalar rashin wutar lantarki, asibitoci, makarantu ko abinci, mun fi su cancantar muyi bore, saboda shekaru 12 na PDP, maimakon kawo ci gaba cikin al’amuran kasa sai koma baya. Idan muka kalli alkaluma na samar da man fetur, aikin yi, asibitoci, cin jarrabawar dalibai, tsaro da tulin abubuwa zamu fahimci cewa 1999 ta fi 2011 ta kowacce fuska. Kasar Egypt, wadda ta dogara da kashi 37% na kudin shigar ta daga baki masu yawon bude ido, wanda ke samar mata da dala biliya 10 a shekara kuma ita ce kasar da ke bin Nigeria a yawan jama’a da mutane miliya 80. A Nigeria cikin shekarar da ta gabata 2010, rahoton hukumar hada haraji na cikin gida (Federal Inland Revenue) sun ce sun samar da dala biliya 18. To idan ka hada wannan da abinda hukumar shige da fice (customs) da ta man fetur (NNPC) ke samarwa, abin zai ruda tunaninka. Amma duk da irin wannan arziki a Nigeria, idan ciwo ya kama ka, kasa mafi saukin zuwa don neman magani itace Egypt.

Bayan shekaru sha biyu da kuma kashe sama da dala Biliya 20 (wadda aka sani) wutar lantarki maimakon ta gyaru sai dada lalacewa ta ke yi. A cikin yan shekarun nan bayan yakin Iraqi ya lafa, bangaren Kurdawa, saboda harin boma bomai da ya lalata wutar lantarki sai su ka yanke shawarar yin tashar wutar lantarki tasu ta kansu yadda ba za su dogara da Bagdaza ba, kun san nawa a ka kashe cikin tsawon wane lokaci? An kashe dala miliyan dari biyar cikin watanni kasa da sha uku. Kada mu manta cewa wannan sashe na kurdawa ya fi mu yawan wutar lantarki da ya ke bukata, sannan a cikin yanayi na yaki aka yi wannan aiki da kudin da basu wuce kashi 2.5% na abinda muka kashe cikin shekaru 12.

Babu wanda ya san adadin mutane da aka kashe, basu ji ba basu gani ba, daga hawan Obasanjo zuwa yau a rikicin addini da na kabilanci, kuma muna gani yadda Jos ta zama a yanzu. Amma mutuwar mutum guda, wato wani yaro da ya gama makaranta amma ya rasa aikin yi a Tunisia, ya yi kokarin saida kayan marmari a bakin titi amma hukumomi suka hana shi asboda cewar bashi da izini. Sakamakon haka ya sa ya kona kansa don bakin ciki, wannan shi ya haifar da juyin-juya-hali da yayi awon gaba da shugaban Tunusia Ben Ali. Kuma burbushin hakan ya haifar da cewa yanzu dole sai Mubarak ya sauka daga mulki a Egypt.

Duk wanda ya karanta tarihi, zai fahimci cewa turawa yan mulkin mallaka sun yi tsari a cikin shekarar 1882 a Berlin conference wanda ya haifar da karkasa kasashen afurka karkashin mulkin kasashen yamma. Kasancewar masu hangen nesa ne, sun tabbatar da cewa dole za’a wayi gari wata rana su bar wadannan kasashe don haka ne sai suka shirya harhade mabanbanta kabilu da addinai karkashin kasa daya domin yin amfani da wannan dama ta ci gaba da ganin kasashen cewa ba su sami damar ci gaba irin na sauran mutane ba. Misali akwai Nigeria a ciki, Sudan, india da Pakistan, Indonesia da sauransu. Wannan banbanci na addini da kabila yayi tsirin da suke so domin har a yau, muna gani yadda a nan Nigeria, Sudan da India/Pakistan kabilanci da addini ke haifar da zubar da jinni da tauye ci gaba. Hanya daya da zata kawo canji a wadannan kasashe musamman Nigeria ba shi ne aware ba (kada mu manta wannan yunkuri na aware a 1967 ya haifar da yakin basasa a Nigeria wanda ya haifar da zubar da jini mafi muni a wannan nahiya ta afurka domin an kashe sama da mutane miliyan daya). Kuma muna gani sama da shekaru hamsin da raba India da Pakistan amma a yau din nan ana neman tattaunawa tsakaninsu saboda gaba da hare-hare. Wannan kuskuren muna ganin yadda aka maimaita shi cikin wannan shekara na raba Sudan ta kudu da arewa. Mafita daga wannan matsala ita ce kamar yadda wasu dattijai na PDP suka yi tunani a 1999 na cewa a rika mulkin karba-karba. Hikimomin da ke cikin wannan tsari na da yawa domin dai abu na farko shine zai dakushe wutar kabilanci da addini, domin kowa yana ganin cewa akwai lokacinsa don haka zai bada hadin kai. Wannan shine ya baiwa wannan jamhuriya damar kaiwa tsawon shekaru da ba’a taba samun gwamnatin farar hula ta yi ba a Nigeria. Hadarin wannan tsari shine kawai idan da za’a wayi gari a ce an kashe shugaban kasa (matukar ba a juyin mulkin soja ba ne) zai iya jefa kasa hadari (kamar yadda ya faru a Rwanda). To amma shi kansa wannan tsoro, yana iya hana masu tunanin kashe shugaba su ja da baya (Mun ga yadda hankula su ka tashi lokacin da aka fara cewa obasanjo ya mutu). Mutuwar Yar Adua ta wuce lami lafiya kuma aka ci gaba da harkoki yadda aka saba saboda dai wancan tunani na karba-karba. Amma me ya faru da zarar Jonathan ya nuna aniyar sa ta watsi da karba-karba ya shiga zabe? An farfado da gabar kabilanci da ta addini wadda tun yakin basasa ba’a taba irinta ba. Karancin ilimi da yawaitar jahilci ya sa talakawa sun kasa fahimtar cewa banbanci biyu ne a kasarnan, na masu mulki da yan barandansu da kuma talakawa a daya bangaren. Dole ne sai an yi watsi da wadannan banbance-banbance matukar ana son a ci gaba, kuma bama gani cewa mataimakin Jonathan dan arewa ne musulmi, kuma na Buhari kirista? Sannan kuma kuri’un wakilan arewa su ne suka ba Jonathan takara a PDP?

Wannan farfado da banbanci ya fito karara idan muka duba kwarya-kwaryar sakamakon wanda suka yi rajista inda aka sami sakamako kamar haka (amma fa INEC bata tabbatar da shi ba tukuna)

Arewa maso yamma da ke da jihohi bakwai an sami masu katin jefa kuri’a miliyan 13, sannan jihoji shida arewa maso gabas miliyan 8, arewa ta tsakiya miliyan 5. A kudu kuma jihohi shida na kudu maso yamma miliyan 14, jihohin kudu maso kudu miliyan 8 sannan kudu masu gabas miliyan 9. Wato a jumlace arewacin Nigeria (amma ba katsina) suna da masu jefa kuri’a miliyan 28 sannan kudu na da miliyan 32. Matukar za’ a bari kabilanci da addini yayi tasiri a wannan zabe, zai wahala kasar nan a kwashe lafiya bayan zabe domin za’a yi kare-jini, biri-jini. Alal hakika idan za’a cire son rai da bangaranci, Jonathan shine ya haifar da duk wata fitina da ake ciki saboda neman biyan bukatunsa na kansa, domin kowa ya gani cewa tun da ya hau mulki me yayi wanda zai sa ma ace ya tsaya takara? Ba’a taba samun shugaba wanda ya nuna bashi da wata alkibla ta kawo gyara a kasar nan kamar sa ba, kuma idan aka bashi dama (ba wai don bana son sa ko kabilanci ba) zai jefa kasar nan a hadari.

Ina ma dai a ce jam’iyyun siyasa da ke adawa zasu yarda su yi kawance wanda zai sa Buhari ya hakura da takara ya bar wa Nuhu Ribadu domin shi ya fi cancanta a tunani na. Dalili kuwa shine na farko dai matashi ne wanda ke da kishin kasarsa kuma an bashi dama yayi abubuwan da ko a mafarki ba wanda yayi zaton zasu iya faruwa. Na farko ya karbo kudaden da Abacha ya sace, karo na farko da turawa suka yarda da yin abu makamancin haka. Ya daure maigidansa, wato Tafa Balogun da gwamna mai ci (Ala meseigha). Ya binciki gwamnoni 31 masu ci ya kai wasu kotu. Ya karbe kudade makudai (sama da dala biliyan 5 daga hannun yan 419 da yan siyasa). Ya samar wa da Nigeria kimar da bata taba samu ba a sahun kasashen duniya. Dalilin aikinsa an yafe mana bashi na dala biliyan 38. Ya kawo canj a harkar hada hadar kudi ta bankuna yadda barayin kudaden jama’a suka fara gagara kai kudi bankuna. A karo na farko, mahukunta sun fara tsoron bincike daga EFCC. Na san akwai mutane da ke ganinsa a Karen farautar Obasanjo, amma sun kasa fahimtar da Allah zai bamu irin wadannan Karen farauta cikin yan shekaru da Nigeria ta canza. A cikin abubuwan da nake zargin marigayi yar Adua shine dakile tashen da hukumar EFCC Ta yi, wanda hakan ya sa an koma gidan jiya yadda yan siyasa basa tsoron kowa don haka su ke cin karensu ba babbaka. Babu wata al’umma da ta ci gaba sai ta yarda da cewa za’a iya hukunta masu mulki da iko kamar yadda Nuhu ya fara, domin daga nan ne kowa zai yadda ya bi doka. Wani abu da na ke ganin a yanzu Nuhu ya fi Buhari cancanta shi ne ina ganin zai fi karbuwa a kudu maso kudu da kudu maso gabas fiye da Buhari. Kuma dama inda ya sami karbuwa fiye da ko ina shine kudu maso yamma domin sune ma suka bashi damar ya tsaya takara.

Kash, sai dai na san wanna abubuwa da na ke fada mafarki ne nake yi domin zai wahala. To yan Nigeria, ya kamata ku fahimci cewa lokaci yayi da zamu daina tunani a doron addini da kabilanci mu tsaya mu lura da wadanda za su cece mu. Idan muka gaza, kuma ina kyautata zaton zamu gaza, PDP zata ci gaba da mulki kuma zamu ci gaba da komawa baya har sai watakila mun ga dole kanwar naki, mun kwaikwayi makwabatan mu a Tunisia da Egypt.

Comments

Popular posts from this blog

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

ALAMUN TSINUWA...

SARKIN KANO DA GWANINTAR IYA SUKA