INA SU KASAGI?



Satin da ya gabata na shiga Katsina in da na yi karo da shahararren tsohon dan wasan kwaikwayo Malam Umaru Danjuma (Kasagi) a kofar wajen wani cin abinci inda muka dan tattauna na wani lokaci. Kasagi na rike da wani kwanon abinci wanda ke kunshe da wake zalla. Da alamu cewa bayan tsufa akwai alamun rashin lafiya in da ya tabbatar min cewa ya na dauke da ciwon sukari, dalilin da ya je siyen wannan wake. Kasagi na cikin jerin mashahuran masu wasan kwaikwayo na farko a arewacin Nigeria wanda zaka yi tsammanin cewa a shekarunsa na tsufa ya kamata a ce ya yi ritaya cikin natsuwa da wadata kuma ya na iya kula da lafiyarsa ba tare da matsala ba sakamakon irin gagarumar gudun mawar da ya bayar a fanninsa. Amma Kasagin ya sanar da cewa akwai ranakun da ya kan tashi da safe ba shi da kudin da zai iya siyen maganinsa na ciwon sukari. Irin wannan larura ta sami dan’uwan wasansa wato, Tumbuleke, wanda shi ma ya na cikin wani yanayi. Kwanakin baya haka a ka sami labarin larurar Usman Baba Pategi (Samanja) inda ya kusa rasa idonsa. Haka nan mun ga yadda kwanan nan inda kokarin Jafar Jafar na yin gangamin neman tallafawa tsohuwar yar wasan Hausa Magajiya Dambatta aka tara mata sama da Naira Miliyan biyar, abinda ya ceto ta daga yin bara a kan titi.

 

Kasagi ya zama daban cikin tsoffin yan wasan kwaikwayo sakamakon cewa bayan wannan harka ya kuma kasance marubuci na littafai inda daya daga cikin littafinsa, wato Kulba Na Barna, ya yi fice cikin littafan hausa a tarihin rubuce-rubuce a kasar hausa. Wannan littafi ya karbu sosai yadda har aka wassafa shi zuwa wasan dabe wanda shahararriyar yar jaridar BBC, Bilkisu Ladan, ta fito a ciki. Littafin ya sami cin lambar yabo a baje kolin littafai na kasa-da-kasa dalilin da ya sa hukumar shirin fina-finai da jami’ar Ahmadu Bello su ka shirya karramawa a fadojin garuruwan Gumel, Katsina da Kano wanda ya sami halartar wadannan sarakuna domin taya murna. Ba na mantawa a shekarun 1980 wannan littafi ya zama cikin manhajar makarantu inda ake karanta Hausa. Duk da wadannan nasarori da wannan littafi ya samu bai hana a shekarun mawallafin ya sami kansa cikin matsala ba. Kasagi ya habarta min cewa a halin yanzu gwamnan jihar Kaduna na kokarin sake siyen wannan littafi domin rabawa a makarantu, amma ka san harkar gwamnati domin rijiya na iya bada ruwa amma guga ya hana.

A wata hira da rediyo Faransa wadda su ka yi tare da abokin wasan kwaikwayo Najume Muhammed wanda aka fi sani da Mutuwa Dole na cikin shirin Samanja, Kasagi ya ya nuna cewa a baya lokacin da su ke kan ganiyarsu, ba kudi ne a gabansu ba, illa dai samun nutusuwa ta yin amfani da baiwar da Allah ya ba su wajen fadakar da al’umma amma su na jin dadi duk lokacin da al’umma su ka jinjinawa wannan kokari na su. Ya bada labarin wata rana su fito wajen filin wasan gof a Kaduna sai gwamnan soja na wancan lokacin, Birgediya Abba Kyari ya hange su ya tsaida su kuma ya ce ya kalli wasansu na jiya kuma abin ya birge shi don haka ya na gayyatar su zuwa gidan gwamnati cin abinci. Wannan karramawa ta yi musu dadi kuma itace al’ada wadda ta bace a yanzu cikin al’ummarmu. Yan wasan hausa irinsu Kasimu Yero, Usman Baba Pategi (Samanja) Muhammadu Sani Gwarzo (Tumbuleke), Najume Mohammed (Mutuwa dole), Umaru Danjuma (Kasagi), Mohammed Mustapha (Malam Mamman ko Dan Haki) da duk sauran irin alewa-ta-da, sun cancanci a ce su na cikin jerin mutanen da kasar Najeriya ta karrama da lambobin yabionta irinsu OFR. Amma abin takaici ba wani cikinsu wanda ya taba samun irin wannan karramawa amma duk shekara za ka ga jerin sunaye daruruwan mutane wadanda ba su bada rabin gudunmuwa ga al’umma irin tasu ba amma an karrama su.

A tsawon tarihin al’ummomi duk al’ummar da ba ta karrama jajirtattun cikinta, wadanda su ka bada gagarumar gudunmuwa zaka samu ta na kasancewa koma baya. Wannan dalili ne ya haifar da koma baya a arewacin Nijeriya kuma ya samo asali ne daga shuwagabannin mu na farko saboda assasa alfarma maimakon cancanta a al’amura, musamman na gwamnati da siyasa. Duk da cewa sahun farko na shugabanninmu yawancinsu ba yayan kowa ba ne amma sakamakon samun damar yin karatun boko ya kai su kan mukamai a sassan rayuwa daban daban, maimakon su rike da kuma assasa wannan tsari na cancanta da karrama kwarewa, sai su ka bige da alfarma a harkokin gwamnati da na siyasa wanda shi kuma ya haifar da rashawa da cin hanci. Wadancan shugabannin na farko, irinsu Sardauna sun sami komai a sama kama daga yadda su ka yi karatun boko zuwa yin aikin gwamnati har zuwa ritayar su amma sai su ka kasa assasa wannan tsari da ya yi musu riga-da-wando suka rungumi alfarma wadda ta kassara komai. Wannan mummunan tsari ya mamayi duk wata harka ta zamantakewa a arewacin Najeriya wadda ita ta saka ba ma iya karrama mutane irinsu Kasagi wadanda su ka bada gudunmuwa sai dai wadanda da su a ke dada lalata al’umma. Wannan tsari na alfarma shi ya rusa tsarinmu na bada ilimi da tarbiya kuma a duk lokacin da ilimi da tarbiya su ka gurbace babu sauran fata ga wannan al’umma. Babbar illar gurgunta cancanta da assasa alfarma bai tsaya ga nan kawai ba, sai da ya tsallaka wajen dawwamar da rashin gaskiya da cuta domin itace ke maye gurbin cancanta. Shi yasa a yanzu zaka sami manyan mutane na aikata miyagun abubuwa wadanda a shekarun baya ko rabin abinda su ka aikata ka aikata wallahi sai ka tattara kayanka ka bar garinku saboda kunya. Yanzu abin kunya ya zama ado don haka mutane basa shayin aikata shi domin, maimakon al’umma ta kyamace su sai ta zama ita ke kare su da karrama su. Rashin daukar cancanta da mahimmanci na kashe duk wani kuzari da masu tasowa za su samu wanda zai zaburar da su wajen ganin sun yi abin arziki wanda zai taimaki al’umma, don haka duk munin abu sai su na iya rungumarsa domin shine su ke gani mafita kawai. Kamar yadda manzon Allah ke cewa “Wanda duk ba ya jin kunya, sai ya aikata abinda ya so”

Wajibi idan mu na son kaiwa gaci mu farfado da al’adar karrama duk abin kirki da mutanen kirki. Ba kawai domin farantawa ma su yin abin kirkin ba, har ma da zaburar da masu tasowa wajen ganin sun kwaikwayi hakan. A matsayin yadda muke samun karuwar jama’a a arewacin Najeriya da irin tulin matsalolin da su ka baibaye mu, hakika muna kan mugun siradi wanda idan ba mu yi hobbasa wajen juya akalar tsarin da mu ke a kai yanzu ba, zuwa wani sabon tsari wanda zai tabbatar da kirkirar damarmaki bisa cancanta da kuma karrama cancantar ba, to Allah kadai ya san irin masifun da zamu fuskanta nan gaba kadan. Allah ya kiyaye.

Comments

Popular posts from this blog

ALAMUN TSINUWA...

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

Dabara Ta Rage Wa Mai Shiga Rijiya…