JAZALLAH...AYA NE GA MASU HANKALI
A
cikin zamaninmu ba'a yi irinsa ba kuma da wuya a sake samun kamarsa. Mutane
mafiya daraja sune wadanda Allah ya ce mana
Q3:169
"Ka da ka yi zaton wadanda aka kashe (ko suka mutu) a cikin hanyar Allah
matattu ne, a'a rayayyu ne su, a wurin ubangijinsu"
Nayi
imani cewa Malam Auwalu Abubakar Nagwaggo wanda aka fi sani da JAZALLAH, na
cikin wadannan zababbu domin yayi shahada idan muka dubi yanayin mutuwarsa da
abinda ya biyo bayan rasuwarsa.
A
ranar alhamis, sauran kwana guda ya koma ga mahaliccinsa, bayan sun idar da
sallar la'asar shi da dalibansa da wani bakonsa sai yace da wannan malami bakon
ya fassara masa mafarkin da yayi jiya. A cikin mafarkin wani dalibinsa ya kawo
masa goruba amma danya, sai yace da dalibin nasa "ka rasa abinda zaka bani
sai goruba, kuma danya?" sai almajirin na sa ya ce "Malam ai wannan
gorubar ba irin wadda ka sani ba ce" ya ce "To wacce iri ce?"
Sai ya ce masa "Wannan gorubar ta gidan aljanna ce" Wannan bakon
malami sai ya dubi Jazallah yace Allah gafarta kai ya kamata ka yi fassarar
wannan mafarkin da kan ka. Bayan nan sai Malam yace da direbansa su shiga gari
ya duba mahaifinsa wanda sai dai a kwantar dashi a tayar. Bayan sun gama dubiya
ya sanar da cewa gobe ba zai shigo dubiya ba saboda za su yi tafiya tare da
Malam Nasidi Goron Dutse da Malam Ibrahim Khaleel kuma sai lahadi zasu dawo.
Bisa al'ada duk ranar lahadi su kan zauna karatu a gidan Malam Nasidi na Goron
Dutse amma wannan sati sai aka shirya tafiya ta kwana biyu domin yin nazari da
bincike. Bayan sun dawo Gida a Mil Tara, sai Malam yace da direbansa akwai mai
nama yana bin sa dubu uku amma yana da dubu biyar wajen wani dalibinsa yaje ya
karbo ta, sai ya kaiwa mai nama kudinsa shi kuma ya dauki dubu daya ya hau mota
zuwa gida sai ya kawowa Malam dubu dayar.
Washegari
da la'asar Malam Nasidi ya zo shi da Malam Ibrahim Khaleel sun dauke shi su ka
wuce. Sun je sun kama nazari har kusan sha biyun dare sai Jazallah ya tashi
yaje yayi alwala yayi sallah ya dawo ya zauna. Shiru su ka ji bai ce komai ba.
Ana taba shi yadda yake zaune a harde sai ya bingire, ashe tuni Allah ya karbi
abinsa.
Tun
daga unguwar sarari, inda aka dauko gawar Jazallah, jama'a ne a cunkushe har
zuwa makabartar kwastam da ke Kem. Hatta yan karota da ke bada hannu a danjojin
kofar mazugal da na katsina road watsi suka yi da aiki suka bi gawar. Wasu
mutane da dama cikin adaidaita sahu sun yi watsi da inda za su je sun bi gawar.
Cunkuson abin hawa tun daga gidan Malam har zuwa wapa da katsina road. Saboda
yadda makabartar ta cika makil kafin isowar gawar, sai dai mika makarar aka
rika yi gaba-gaba zuwa bakin kabarin.
Karramawar
da Allah yayi wa Jazallah a cikin mutuwarsa wallahi kudi ko mukami ba zai iya
siyenta ba sai dai ayyukan alheri. Duk maluntarka, Jazallah ya fi ka raba ilimi
kyauta kuma a kowanme yanayi na rayuwarsa ilimintarwa ya ke domin ba shi da
wani shinge da jama'a, haka nan duk arzikinka Jazallah ya fi ka wadata domin a
koyaushe ya na iya bayar da duk abinda ke hannunsa ko da su kenan kuma ga
mabukata na hakika wadanda Allah ke farin ciki a taimakawa. Malam Auwalu daban
yake domin wallahi ban taba ganin fushinsa ba ballantana abokin fadansa tsawon
rayuwa. Babu wani abu nasa na kan sa, komai nasa na jama'a ne. Malam bai iya
cewa babu ba. Duk sanda kaje da bukata ko bashi ne sai yaci. Ba na mantawa wata
shekara yata bata koma makaranta ba saboda bani da kudin registration. Da ya
sami labari sai ya kirani naje na same shi. Yace muje bankinsa sun ce idan yana
son bashi ya zo. Muka je su kayi masa bayani ya ce a bashi dubu dari kawai. Aka
bashi bashin ya raba biyu ya bani rabi yace aje a kai yarsa makaranta. A yanzu
haka ana tattara alkalumma na basuka da kantuna ke binsa. Akasari magidanta
idan basu da abinci a gidansu sai ya tura su shago a karbi bashin abinci sai ya
sami faraga sannan ya biya.
Kai
hatta yan shaye -shaye na area din unguwarmu su kan je su jira Malam ya gama
karatu su ganshi ya taimaka musu da kudin abinci. Malam ba ya kyamatar kowa, na
kirki da na banza, kowa nasa ne. Malam na da dubu goma a aljihunsa amma yana
iya shiga gida ba shi da ko sisi na cefane. Wata rana a kan hanyarmu zuwa
Bauchi sai muka tsaya a Kafin Madaki sallah muka rasa ruwan alwala, hatta pure
water. Kawai sai ga wata mata Kirista ta taho da ledar pure water guda daya a
hannunta ta doshi Malam kai tsaye ta durkusa ta gaishe shi ta kuma mika masa
ruwan cikin girmamawa.
Ni
da Malam ya gaya min cewa bashi da burin da ya wuce ganin an gina makarantarsa
ta Mil Tara kuma bai bar Duniya ba sai da wannan buri nasa ya cika domin an ce
min Alasan Dan Abdulkadir Dantata ya alkawarta miliyan 35 kuma an fara ganin
makarantar, a yanzu haka ana yin azuzuwa na farko.
Muna
samari ya kira ni ya shawarce ni da in tattaro matasa abokanmu domin ya rika
koya mana fiqihu da sauran littafai. Ka na zuwa makaranta zaka tarar da
littafin da za'a karanta a tsakiyar da'irar sai ya ce ka dauki naka kuma
kyauta. Kowacce rana akwai littafin da ake karantawa. Wannan makaranta na cikin
ginshikan da ya sa ni nazarin addini mai zurfi yadda a jami'a ma addinin
musulunci na cikin abubuwan da na karanta.
Jazallah
wayayye ne na hakika domin duk da girma ya kama shi ya nemi ilmin boko inda
yayi diploma a Aminu Kano Aminu School for Islamic legal studies sannan ya wuce
ya yi digiri a jami'ar musulunci ta Katsina.
Duk
ni'imar da Allah ya yiwa Malam abar yadawa ce ga al'umma. Duk inda ya zauna abu
biyu ya ke yi tsawon rayuwarsa, wato yada ilimi da dan abin masarufin da Allah
ya huwace masa.
Wallahi
ban san wani malami da ya fahimci cikakkiyar koyarwar addinin musulunci ta
'yanuwantaka, kuma ya aiwatar da ita a zahiri kamar Jazallah ba. Duk da cewa
shi batijjane ne ba zaka taba jin ya na la'antar yan izala ko yan shi'a ba
domin ya fahimci yancin ra'ayi. Kuma hakika na gamsu da cewa Allah ya karbi
ayyukan Malam saboda ya zabi raya shi bayan mutuwarsa a cikin zukatan mutane. A
wajen zaman makokinsa duk wanda yazo yana da wani labari na alherin malam. Mun
shiga adaidaita sahu ni da yayana muna jimaminsa sai kawai Dan adaidaita yace
"Kai wallahi wannan mutumin waliyyi ne, saboda tun jiya zai wahala in
dauki fasinja biyu ko uku ban ji suna irin wannan yabo na wannan bawan Allah
ba"
Rayuwar Jazallah ya
isa ta ja hankulanmu mu gane cewa ba yawan karatu ko dukiya ke kai mutum
kusanci da Allah ba, saidai yadda ka yada wannan ilimi ko ka wadata mabukata da
tsarkakakkiyar zuciya. Malam ya tsarkake zuciyarsa kuma ya yada ilimi da
arzikin da Allah ya ba shi ba tare da rowa ko kyashi ba, sakamakon haka Allah
ya nunawa duniya ya karbi aikin malam ta hanyar raya shi bayan mutuwarsa. Ya
rage namu mu yi nazari mu gane kuma mu san cewa tsarkake zuciya shine jihadi da
zai kai mu ga nasara. Hakika mun yi asarar Uba, Dan'uwa, Aboki kuma Malami, na
yi kuka da hawaye kashirban da aka sanar da ni mutuwar malam amma kuma na yi
murna da farin ciki yadda Allah ya nunawa duniya cewa hakika Jazallah, Jazallah
din ne domin a rayuwarmu bamu taba ganin wanda ya sami shaidar jama'a irinsa
ba. Allah ya jikansa ya saka mu a danshinsa.
Comments
Post a Comment