KASAFIN KUDI KO RABON GANIMA?
Tsarin kasafin kudi da shugabannin kasa ke gabatarwa a gaban majalisa a duk shekara, tsari ne wanda aka gadar mana tun daga kafuwar mulkin dimokuradiya a dawowar jamhuriya ta hudu tun shekarar 1999. Amma babban abin lura shine wannan tsarin bai wuce taron kasafta kudaden kasa a matsayin ganima ba ga mahukunta a matakan mulkin da ma'aikatan gwamnati. Talakawa, tattalin arziki da ci gaban kasa ba wani romo da ke isa garesu sakamakon kasafin kudin.
Rabe-raben kawuna a kowanne fanni na rayuwa ya hana yan kasa gane inda gizon ke saka. Don haka abinda ke gaban kowa shine bukatarsa, amma ba adalci ba. Sakamakon haka mahukunta ke cin karensu babu babbaka wajen wadaka da dukiyoyin al'umma tare da jefa al'ummar cikin kuncin talauci da jahilci.
Idan muka duba kasafin kudin shekara me zuwa (2021) wadda a satin da ya gabata shugaba Buhari ya kaddamar gaban yan majalisu, zamu ga cewa shine mafi tsoka a tarihi inda ya kai Tiriliyan 13.08, duk fa da cewa ana cikin annobar kwarona. A cikin wannan adadi zamu ga cewa gibin da za'a samu cikin wannan kasafin kudi zai kai Naira Tiriliyan 5.21, wanda a tashin farko hakan ya karya tsohuwar dokar majalisa ta sanin ya kamata wajen kashe kudaden gwamnati (2007 Fiscal responsibility act). Dokar ta haramta barin gibin kasafin kudi ya haura kashi 3% na ilahirin yawan adadin karfin arzikin kasa (GDP). Wanda wannan adadi a shekarar 2019 ya kai kimanin dalar amurka biliyan $447. Ko a wannan adadi na 2019, gibin ya kai kaso 3.5% wanda sakamakon annobar kwarona a wannan shekara wajibi adadin yayi kasa da haka wanda zai sa adadin gibin ya karu.
Sannan kuma kaso mafi tsoka da kasafin ya ware shine na ayyukan gudanar da gwamnati na yau da kullum wanda zai lakume Tiriliyan 5.65, wato kashi 43% na ilahirin kasafin kudin wajen biyan ma'aikata albashi, alawus, fansho da gudanar da aiki na ma'aikata, masu rike da mukamai na siyasa a gwamnatoci da ma'aikatan gwamnati sama da 40 da muke da su hadi da hukumomin gwamnati sama da 400, wadanda Idan ka tattare su gaba daya basu kai kashi 5% na yawan al'ummar Nijeriya mai miliyan 200 ba. Amma wadannan tsiraru su ne za su lakume kashi 43% na kasafin kudin.
A shekarar 2012, lokacin da Sunusi Lamido ya soki wannan tsari sai aka yi masa ca kamar za a cinye shi. A rahoton Farfesa Anna O. Anya shi ma ya tabbatarwa gwamnati cewa wannan tsari ba mai dorewa bane. A daidai lokacin kuma ma'aikatar kudi ta kasa ta fitar da wani rahoto wanda ya nuna cewa a cikin shekara takwas an fitar da Naira Tiriliyan 16.44 daga asusun tarayya wanda aka kashewa mutane 17,474 da ke cikin gwamnati. Wato kaso 0.0001% na yawan adadin yan Najeriya miliyan 180 a wannan lokaci.
Babu inda aka fi cutar talaka a tsarin kasafin kudi irin bangaren manyan ayyukan da ke fadowa karkashin ayyukan gudanarwa na yau da kullum (capital recurrent expenditure). Domin alal misali a karkashin wannan ne a kasafin kudi na shekarar 2010 aka ware Naira miliyan 1.19 domin kayan kicin a fadar shugaban kasa, amma da shekara ta kewayo sai ga shi an sake sahale Naira miliyan 489 ga wannan kayan kicin. Na san bamu manta korafin Aisha Buhari ba na cewa a asibitin fadar shugaban kasa babu ko sirinji kuma na'urar daukan hoton kashi ba ta aiki duk da cewa tsawon shekaru wannan asibiti ya lakume Naira biliyan 11. Kwanan nan muka gani a akwatunan talabijin yadda ba shiri majalisa ta dage binciken ba'asi kan hukumar Naija Delta sakamakon barazanar tona asirin yan majalisar da ke da hannubabu a badakalolin hukumar. Haka kuma wani jami'in wannan hukumar shima a talabijin yazo da takardu ya na ikirarin cewa ana bada kwangila sama da sauce 20 kuma a fitar da kudaden ba tare da an aiwatar da ita ba.
Obasanjo ya shigo da tsarin daina baiwa ma'aikata gidaje ko motoci da saransu (monetization) wanda ya fara aiki a 2004 amma daga zuwan gwamnatin Yar'Adua sai ga sakataren gwamnatin, Babagana Kingibe, ya sanar da soke wannan tsari wanda zai rage barnatar da kudin jama'a wajen siyen motoci ga ma'aikata kimanin 996,774, da zababbu 1,448 da yan majalisa 469 da alkalai 1,152, da ire iren wadannan.
Zuwan Buhari a 2015 ya sa mun yi tsalle da murna a zaton cewa ga macecinmu ya zo. Kuma ba mu yi kasa a gwiwa ba sakamakon yana zuwa ya kaddamar da shirin da gwamnatin Jonathan ta kirkiro na asusun bai daya (TSA) amma ta kasa wanzarwa. Kasafin kudin Buhari na farko a 2016 bai saba da yadda aka saba ba, amma sai muka yi masa uzuri sakamakon zuwansa kenan. Wannan kasafi kamar yadda aka saba ya mika kashi 65% wajen ayyukan yau da kullum (kashi 43%) da kuma biyan basuka (kaso 22%). A abinda ya rage an baiwa ayyukan raya kasa kashi 29%, wanda a hakika shi ma zaka samu yan kwangila da ma'aikatan gwamnati ke morarsa. A takaice talaka ya tashi a tutar babu domin su kansu ayyukan raya kasar zaka samu basa kammaluwa a kasafin kudi na wannan shekara.
To, a shekarar 2017 sai muka sami kwarin gwiwa sakamakon a wannan kasafi mun ga raguwar kudaden ayyukan yau da kullum da kashi 3% kuma manyan ayyuka su ka sami karuwa daga kashi 22% a bara zuwa har kashi 31%. Hakan ya rage kason adadin kudin gudanarwa da na biyan bashi ya fado daga kaso 65% zuwa kaso 62%. Wannan abin a yaba ne, ko kuwa?
Duk da raguwar karfin tattalin arziki sakamakon faduwar mai, yan Najeriya sun ci gaba da goyon baya ga Buhari musamman a rikicin cushe a kasafin kudi tsakaninsa da majalisa wanda aka yi ta kai ruwa rana kafin su sahalewa kasafin na Naira Tiriliyan 9.12. Shi ma wannan kasafi a karshe dai ya koma gidan jiya yayin da adadin kudaden gudanarwa da biyan bashi a jumlace su ka lakume kaso 64%.
Kasafin shekarar 2019 bai zo da mamaki ba domin daga dukkan alamu ba ta canza zani ba, domin kason ayyukan yau da kullum da biyan bashi ya falle da gudu inda ya kai kashi 69%. A kasafin 2020 ne mu ka ga abin mamaki kasancewa a kasafin Naira Tiriliyan 10.3, kason ayyukan gudanarwa da na biyan bashi sun kai har kaso 73%. Mamakin ba a nan ya tsaya ba domin kwatsam sai ga annobar kwarona wadda ta haifar da lockdown, sannan fetur yayi kwantai yayin da duk wani ciniki ya tsaya. A wannan yanayi gwamnati ta sake neman bitar kasafin kudin sakamakon rasa kudaden shiga. A tsammani za ta rage kasafin kudin amma sai ga shi ta kara yawan kasafin kudin zuwa Tiriliyan 10.8 ana tsakiyar annoba.
A shekaru biyar na mulkin wannan gwamnati, ta yi kasafin kudi na Naira Tiriliyan 44.07 wanda kashi 71% na wannan adadi (Tiriliyan 31.5) ya tafi ga kudaden gudanarwa (Tiriliyan 18.07) da kuma biyan bashi (na Tiriliyan 13.5). Wato kason da ya tafi ga ayyukan raya kasa (shi ma a alkalumma kawai) shine Tiriliyan 12.5. Don Allah abin tambaya shine akwai ayyukan raya kasa na wannan adadi da zamu iya nunawa tsawon shekaru biyar dinnan?
Hakika wannan gwamnati ta zakulo aiki mafi mahimmanci a tarihin wannan kasa wanda shekaru 40 ana zancensa, wato aikin lantarki na Mambila. An saka hannu a kan kwangilar wannan aiki a 2017 da wani kamfanin China wanda a cikin adadin kwangilar ta dalar amurka biliyan 5.7, yarjejeniyar ita ce gwamnatin Najeriya za ta bada kashi 15% ne kacal (wato dala miliyan 850 kimanin Naira biliyan 300) inda China zata bada sauran a matsayin bashi mai dogon zango. Tun daga 2018 wannan aiki na Mambila sai ya shiga kasafin kudi, har a wannan kasafin kudi na 2021 an ambace shi amma har yau ba a fara shi ba. Abin tambaya a nan shine, shin Naira biliyan 300 ta gagari kasar da ta yi kasafin Tiriliyan 28 a shekaru ukun da su ka gabata? Biliyan 300 fa kashi daya ne kacal na Tiriliyan 28.
Babban abin damuwa baya ga barnatar da kudaden talakawa a inda ba zai amfane su ba shine maganar tara mana bashi. A yanzu wannan gwamnati ta tara bashin da ya kai Naira Tiriliyan 33 (wato dalar biliyan 87). Shin idan muka kwatanta yawan wannan bashi da ingancin rayuwar dan Najeriya da ayyukan raya kasa ko rage talauci, akwai abin hadawa? Hakika cin bashi ba laifi bane domin kowacce gwamnati na ci, amma wannan basuka da muke ciyowa duk shekara bama ganin komai a kasa, idan banda tulin bashin. Dubi aikin jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan wanda ya ke cikin kasafin kudi na hudu, haka shi ma aikin Mambila na cikin kasafin kudi na uku, haka nan ayyukan Baro, bututun gas na AKK da sauransu. Duk wadannan ayyukan ba wanda zai kasa gamuwa cikin shekaru shida amma ba ko daya. Kuma sauran shekaru uku su ka ragewa wannan gwamnati, me ke faruwa?
Karuwar basuka na yin mummunar illa ga tattalin arzikin mu domin basukan cikin gida na saka kudin ruwa na basukan banki su ci gaba da zama sama sosai wanda ke haifar da rashin habakar tattalin arziki. Sannan basukan kasashen wajen zai ci gaba da uzzurawa Naira yadda ba zata yi daraja ba wajen musaya da manyan kudade wajen canji.
Duk da tabargazar da mahukunta ke yi wajen kashe kudaden kasa ta hanyoyin da ba zasu mori akasarin yan kasa ba, sai kuma gwamnatin ke kara kudaden haraji ba ji ba gani, a lokacin da wasu kasashen ke cire haraji da bada tallafi ga yan kasa. Saboda rashin adalci a daidai lokacin da matakan matse talaka ke kara kamari sakamakon rufe iyakokin kasa, da kara kudin man fetur da harajin wutar lantarki, da rashin tsaro yadda manoma basa iya zuwa gona, sai gashi mahukunta na karawa kansu kudade ta ko'ina a cikin kasafin kudi ba tare da rage nasu bukatun ba kamar yadda suka matse talaka. A wannan kasafi na 2021 fadar shugaban kasa ta ware Naira miliyan 582 domin ciye-ciye da tande-tande a fadar. Koda yake har gara kasafin kudin fadar shugaban kasa na biliyan 72 an ga yadda aka rarraba shi fiye da na majalisar tarayya na biliyan 128 wanda ba wanda ya san ya kasonsa ya ke.
Babu wata kasa da zata ci gaba, matukar ba a yada arzikinta ga yan kasa ba. Ta hanyar rarraba arziki kasa a ke iya cin moriyar basirar matasanta kuma masana'antunta su habaka. Ilimi shine garkuwar al'umma kuma ginshikin ci gabanta amma wannan gwamnati kamar yaki ma take da Ilimi Saboda maida shi kurar baya cikin kasafinta.
Wajibi mu fahimci cewa tsarin tattalin arzikinmu da gudanar da shi akwai babbar matsala musamman ganin yadda kasafin kudi ya zama rabon ganima tsakanin mahukunta na matakan tarayya, jihohi da kananan hukumomi. Ba PDP ce ta fara wannan tsari ba amma ita ce ta assasa shi yayin da a yanzu APC ke kara munana shi. Idan da zamu iya saka rabin kudaden da muke kasaftawa duk shekara a ayyukan jama'a wallahi da cikin yan shekaru mun ga gagarumin ci gaba, kuma wannan dalilia ne ya sa muka zabi wannan gwamnati amma ta kasa tabukawa a cikin shekaru 5. Daga dukkan alamu kuma wannan buri namu na ganin canji zai yi wahala matukar akasarinmu bamu rungumi gayawa kai gaskiya ba, da watsi da son kai wanda a kullum ke raba kawunanmu. Dole mu farka mu gane cewa kasafin kudi ba wani abu bane illa rabon ganima tsakanin masu mulkarmu wadanda muka kakabawa kanmu da kanmu ta hanyar dimokuradiya. Amma mu sani idan mun jajjirce zamu gane cewa ikon fa a hannunmu yake kuma zamu iya amfani da shi wajen tursasa mahukunta su biya mana bukatun mu da kudadenmu a cikin kasafin kudin.
Comments
Post a Comment