MARTANIN DA NA BA MARIGAYI SHEIKH JAFAR MAHMUD ADAM
Laraba, 29 ga watan Maris
na shekarar 2006, ran ace wadda a ka dade ana dakonta sakamakon yayata zuwan
husufin rana da kafafen yada labarai na duniya su ka yi makonni sun a yi.
Masana kimiyya sun yi has ashen cewa za’a sami husufi a wannan rana a fadin
duniya wanda za’a ga cikakken husufin dag inda zai faro a kasar Brazil ya keto
tekun Atalantika, ya bi ta arewacin Afirka ya ratsa tsakiyar Asiya inda zai
kare daidai faduwar rana a yammacin Mongolia. Sauran kasashe dab a za su ga
cikakken husufin ba sun hadar da kasha biyu cikin uku na kasashen Afirka hard a
Najeriya, da wasu kasashen Turai da tsakiyar Asiya. A wannan safiya ina zaune
da biro na zan fara rubutun shiri na da na ke gabatarwa na TSOKACI wanda na ke
bayanin ayoyin Qur’ani da kimiyya a sabon gidan rediyon Freedom na Kano, sai na
jiyo muryar marigayi Sheikh Jafar ya na bayani a gidan rediyon na Freedom inda
yake bayani kai tsaye game da wannan husufi ta mahangarsa ta addini. Hakika
Jafar na cikin mashahuran malamai das u ka fito daga arewacin Nijeriya saboda
iliminsa na larabci da Qur’ani sai dai kawai kasancewar ya na da tsaurin ra’ayi
irin na izala. Maimakon ci gaba da rubuta na sai na zauna na saurarin shirin
gaba dayansa inda na dauki wasu abubuwa wadanda na ke ganin cewa da kuskure a
cikinsu. Sakamakon haka na yanke shawarar mayar masa da martini a cikin shirina
na gaba sakamakon ya jibanci abubuwan. Washegari na tafi gidan rediyon Freedom
inda na gabatar da shirin.
Da farko dai Sheik Jafar ya zargi turawan yamma da cewa maganar
das u ke yi cewa husufi sakamakon wata na shiga tsakanin rana da duniya ne ba
daidai ba ne kuma ya sabawa ayar Qur’ani wadda ke cewa
Q36:40 “Rana bay a kamata a gareta, ta riski wata. Kuma dare
bay a kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukkansu a cikin wani
sarari guda su ke yin iyo”
A fassarar Malam Jafar wannan aya ta kore wancan ikirari na
masana kimiyya da ke cewa wata ya shiga tsakanin rana da duniya kuma ya kara da
wani hadisin da ke cewa idan ana husufi musulmi su shiga masallatai su yi ta
addu’a domin zazzabi yak e. A cikin shiri na, na ambaci cewa dalilin da Jafar
da wasu malamai su ka yi wa wannan aya gurguwar fahimta shine sakamakon bas u
da ilimin kimiyya, domin da suna da ilimin kimiyya zasu gane cewa hakika wannan
aya bat a yi karo da bayanai na kimiyya da lamarin husufi ba ko na Rana ko na
Wata. Na ci gaba inda na bada sassaukan misali wanda ko wanda bai je makarantar
boko ba zai iya fahimtar hakan. Na yi amfani da misali da agogon bango wanda
ked a hannayen dakika, minti da awa wadanda ke cikin farantin agogon. Idan muka
dauki farantin agogon inda wadannan hannaye ke zagaye a ciki tamkar shine
sararin samaniya wanda Rana, Wata da Duniyarmu ke iyo a ciki. Idan mu ka dauka
cewa hannayen dakika da na minti da na awa su ne a maimakon Rana, Wata da
Duniyarmu sai mu dauka cewa hannun dakika da ke sama shine rana, hannun minti
kuma wata sannan hannun awa kuma duniya. A misalign agogo duk inda sha biyun
rana ko ta dare ta yi, wadannan hannaye su kan kasance a layi guda wanda ke
tsaye a kan sha biyun, to kamar haka duk sanda rana, wata da duniya a yayin
kewayensu su ka tsaya a saitin layi guda shine sanda ake samun husufi. Idan
husufin rana ne kaga rana dake hannun dakika idan haskenta ya taho zai tarar da
wata da ke tsakiya wanda zai hana hasken nan isa doron duniya maimakon haka sai
inuwarsa ta fado kan doron duniya yadda wanda ke duniya idan ya kalli rana sai
ya ga duhun wata yak are ta. Haka abin yake a lokacin husufin wata inda duniya
ke shiga tsakanin rana da wata yadda hasken rana da dama shi ke haskakka wata
sai duniya da ke tsakiya ta kare shi yadda ba zai isa watan ba, a maimakon haka
sai mu ga inuwar duniya ta rufe wata yadda zai zama baki babu haskensa.
Don haka duk da cewa wadannan halittu na duniya, wata da rana
na iyo a sarari guda ba wanda zai taba wani amma kuma wani na iya kare hasken
wani isa wajen wani, abinda ke zama husufi ba tare da karya dokar wani wa baya
tarar da wani. Wannan bayani na kimiyya ba inda ya yi karo da waccan aya ta cikin
Yasin. Bayani nay a sami karbuwa sosai ga masu sauraro na amma dai dalilin haka
ya san a bar ci gaba da gabatar da wannan shiri. Ba anan kawai Malam Jafar ya
tsaya ba domin akwai inda yak e cewa idan da duniya na kewaye da sai a ga
masallacinsa da ke Gadon a yammacin Kano ya karkata wajajen Tarauni da ke
gabashin Kano. Amma shi katantanwa da duniyar mu ke yi abu ne dam asana su ka
gano kuma ilimi ne na yakini wanda aka iya tabbatar da sashihancinsa domin shi
ne dalilin day a sa a ake sallar Azahar a masallacin Annabi amma sai bayan awa
biyu za’a yi azahar din a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna. Da duniya bat a
katantanwa da lokaci a doron ta zai kasance bai daya a ko’ina cikin duniya amma
kasancewar wannan katantanwa shi yasa a ka sami zangogin lokaci goma sha biyu a
doron kasa yadda yayin da wani ke shiga safiya wani ke shiga yamma.
Abin day a kamata mu tambayi kanmu shi me yasa manyan malaman
ke jahiltar kimiyya wadda yara yan firamare ya cancanta su sani? Shin Qur’ani
da Hadisi bas u nuna mana mahimmancin ilimi ba, wanda ya shafi kimiyya da
sauran fannoni a matsayin wajibi a san su? Shin neman ilimi bas hi umarnin
farko da Allah ya sanarwa da Annabi ba a kogon hira? A littafin Bukhari na farko
wato Kitabul Ilm, shin ba akwai hadisai sama da 134 wadanda ke nuna martabar
neman ilimi ba?shi ma Imam Gazali ya bude littafinsa na Ihya-al-ulum das ashen
ilimi kuma shin ba mu ga yadda Allah ya nuna mana fadin ilimi cikin tafiyar
Musa da Kidir na banbancin ilimin annabta da na walittaka ba? Shin ba ilimin kimiyya
ba ne ya kai musulmi tsaikonsu a baya yadda su ka kafa daular da ba’a taba
ganin irinta ba kafin zuwan musulunci? Musulman bay a su ne su ka gina
ginshikin kimiyya wadda duniya ke takama da ita a yanzu amma me yasa malaman mu
na zamani da dama ke kyamatar kimiyya, ina dalili? Shin malaman mu na zamani
zasu iya yin shura a fannonin ilimi irinsu Ibn Sina, Ibn Rushudi, Ibn Khaldun,
Al-Gazali, Al-Haitham da ire-iren magabata wadanda su ka shahara a fanonin
kimiyya kama dag a ilimin sararin samaniya, likitanci, falsafa, lissafi da
sauransu kuwa?
Amma baa bin mamaki ba ne yadda daga malaman musulmi su ka
zama koma baya a fannonin ilimi domin an yi daruruwan shekaru ana cusa abubuwa
da sunan addini wadanda ba addinin ba. Musamman idan mu ka dauki yadda Salafiyanci
ya bada gudunmuwa ta wannan fanni. Salafiyanci ya fara samo asali daga Imamu
Ibn Hanbal (d. 825) daga wancan lokaci su ka yanke shawarar bin hanyar magabata
kawai (wato As-Salaf al-salih) wadda Ibn Taimiyya ya inganta (d. 1328) yayin da
Muhammad Bn Abdulwahab ya dabbaka. Asalin salafiyanci ya faro da zummar karkade
duk wata bid’a da tsayar da sunna, wanda hakan abu ne mai kyau sosai amma kuma
wajen aiwatar da hakan sai ya sami matsaloli guda biyu. Matsalar farko it ace
wajen yin fassarar Qur’ani kai tsaye yadda ta zo (kamar yadda Jafar yayi wa
waccan aya ta Yasain) sannan abu na biyu shine kafirta wanda ya yi sabani da
ra’ayi (wato Takfir). Ibn Hanbal shine asalin salafiyanci idan mu ka yi
la’akari da komawa kan fassarar kai tsaye ga Qur’ani amma a matsayin darika sai
a karni na sha hudu Ibn Taimiyya ya kai ta cikakkiyar darika. Aure tsakanin
yunkurin Ibn Abdulwahab da na Ibn Saud a karni na sha takwas ya bada damar
amfani da karfin soja wajen kafa daular kasar Saudi Arabia. Mazhabar Hanafi, it
ace aka fara kafawa kuma wadda ita kadai ta yarda da amfani da ra’ayin masana
wajen kiyas yadda shugabanta ya yi ikirarin cewa “Mu mun yarda da ra’ayi amma
ba zamu tilasta wani bin wannan ra’ayi ba idan ka na da hujja wadda ta fi tamu
karfi ka zo da ita” da ace duk mazhabobi sun dauki wannan ra’ayi da hakika
ilimi ya bunkasa a musulunci musamman a bangaren bincike amma sai mazhabobin
Maliki da na Hanbali (wadanda yan salafiya ke bi) su ka kaucewa wannan ra’ayi
tare da sukarsa. Shi kuma shafi’I sai ya raba kafa a matsayin mai sassauci
tsakianin biyun.
Annabi dai shine annabin karshe kuma musulunci ne saukakken
addini na karshe amma duk da haka babu wani mai tafsiri (Mufassir) ko mai
ilimin shari’a (Faqih) wanda za’a ce shine mai fassarar karshe ko mai ilimin
shari’a na karshe. Amma a farkon karni na goma wadannan mazhabobi musamman
karkashin hanbalawa an rufe kofar ijtihadi (bincike na masana) kuma duk wanda
ya kaucewa wannan ra’ayi ana ganinsa a matsayin dan bidi’a. Daga wannan lokaci
sai kururutar Taqlid (wato karbar hukuncin magabata ba tantama) ya zama rowan
dare, duk da cewa dai hakan kuma ba zai rasa nasaba da Mihna (azabtarwa) wadda
sarakunan musulunci a lokacin (Mamun, Mu’tasim, Wathiq da shekaru biyu na
Mutawakkil) karkashin malaman mutazilawa su ka rika yi wa malamai, musamman yan
sunni wadanda ke da’awar cewa Qur’ani ba halittacce ba ne. Imam Hanbali na
cikin wadanda aka azabtar tare da daurin kurkuku sakamakon wannan ra’ayi.
Watakila wannan lamari na cikin dalilan da yasa ya zama a gaba wajen ganin an
rufe kofar ijitihadi. Amma kuma rufe wannan kofa, bayan sabawa umarnin Allah na
“Ku tambayi masana, idan ba ku sani ba” na cikin dalilin koma bayan ilimi a
musulunci.
Mulkin mallaka da rugujewar daular usmaniyya (Ottomon) ya
zaburar da masanan zamani irinsu Sayyid Qutub, Muhammad Abduh da Rashid Rida
farfado da ra’ayin rikau a matsayin hanyar das u ke ganin uata za ta ceci
al’ummar musulmi daga tasirin turawa, kuma dukkansu sun yi rubuce-rubuce mai
yawa a fannin. Kafa madabba’ar Salafiyya da saida littafai mai suna Al-Maktaba
al Salafiyya a kasar Misra a shekarar 1909 karkashin jagorancin Muhibb Khatib,
ta samar da dimbin littafai ire-iren haka. A lokacin yakin duniya na biyu,
A;-Khatib ya sami gayyatar Amirin Makka inda ya je ya kafa madabba’ar Al
Amiriyya. Zuwa shekarar 1924 kasar Saudiyya ta kaddamar da buga rubuce-rubucen
Imam Hanbali. Cikin littafan farko da wannan madabba’a ta fara bugawa shine
littafin Ibn Qayyim wanda Sarki Sa’ud da kansa ya dauki nauyinsa. Wannan ya
bude hanyar rubuce-rubuce hanbalawa masu tsaurin ra’ayi kuma nabuga dubban
daruruwa wadanda aka rika rabawa mahajjata a kokarin assasa salafiyanci. Zuwa
shekarar 1921 an bude wajen saida littafai mai suna Salafiyya a kasar Pakistan
da kuma a wani a shekarar 1922 a Damaskus ta Syria baya ga samar da tallafin
karatu ga dalibai zuwa jami’aUmmul Qura da ke makka.
An ci gaba da yada Wahabiyanci baya ga rubuce-rubuce littafai
da ake baiwa mahajjata kyauta ta hanyar kafa Ribida da wata jami’ar a Madina
wadda ita ma ke daukar nauyin dalibai kyauta a horar das u salafiyanci kafin su
koma kasarsu su ci gaba da da’awa. A Najeriya kuwa salafiyanci ya samoasali
daga yunkurin mutane biyu, wato Ahmadu Bello Sardauna da kuma Sheik Abubakar
Gumi bayan sun dawo daga aikin Haji a shekarar 1955. Gumi yayi wa kasar saudiya
ayyukan fassara shi kuma Sardauna na cikin iyayen da suka kafa rabida (Muslim
World League) a wannan shekara a Saudi. Gumi ya kafa kungiyar Izalatul Bidi’a
wadda ta fara da’awa ga mutanen gari yayin da Sardauna ya kafa Jama’atu Nasril
Islam wadda ta tunkari yan boko da ma’aikata.
Ta’addanci da muke fama das hi yau a Najeriya kuwa, ko mun ki
ko mun so, ba zamu iya raba shi da tsarin Takfir (na kafirtawa) wanda Sheikh
Jafar ya assasa a tsawon shekaru sama da goma ya na tafsiri a Maiduguri ba.
Tafsirin tsaurin ra’ayi na kiran a yi jihadi da kuma kafirta yan uwa musulmi
tare da kyamatar ilimi daga nasara (kamar yadda na bada misalign a sama na
Jafar) su ne su ka jawo mana Boko Haram. Jafar mazaunin Kano ne amma Boko Haram
bat a faru a Kano ba, menene dalili sai a Maiduguri? Dalili shine can Jafar ya
maida hankalinsa wajen wa’azinsa duk shekara kuma mutanen Maiduguri bas u sami
wayewar ilimi na addini da na boko ba (idan banda na haddar Qur’ani) sannan
talauci da rashin kasuwanci mai karfi ya ja hankali masu ra’ayin rikau irinsu
Muhammad Yusuf sun kwankwadi wannan akida ta salafiyanci mai tsauri fiye da
malamansu yadda su ka yi watsi da boko kwata-kwata kuma su ke yaki da kimiyya
tare da mafani da Takfiranci akan duk wanda bai yadda da ra’ayinsu ba sakamakon
day a saka shi kansa Jafar ya kasance mutum babba na farko day an Boko Haram su
ka kasha.
Ba a nan Najeriya kawai ba a duk fadin duniya kama daga
Afghanistan da Pakistan, zuwa Syria da Bagadaza, a Nigeria, Mali da Somaliya duk
kungiyoyin Al’qaeda, Taliban, Isis, Al-Shabab da Boko Haram, sun kasance tamkar
bangaren masu daukar makami ne na
kungiyar salafiya kamar yadda kungiyar falasdinawa ked a PLO da Hamas. A yanzu
hatta kasar Saudiyya, wadanda su ne suka dauki nauyi da assasa salafiyanci a
doron duniya, sun fara dawowa daga rakiyar malamaimasu tsaurin ra’ayi yadda su
ka fara cire wasu tsauraran fatawoyi da suka samar a baya domin rage karfin
irin wadannan malamai.
Musulunci bai taba samun kansa a tsaka mai wuya irin ta
wannan zamani ba saboda yadda turawan yamma su ka sako addinin a gaba sannan a
cikin gida ake fuskantar tsatstsauran ra’ayi wanda ya haifar da ta’addanci ga
kan mai uwa da wabi. Mafitar musulmi day ace, at yin watsi da duk
banbance-banbance na kungiyanci da darika a dunkule waje guda a kwaikwayi
hakikar rayuwar da annabi ya yi a Madina. Dole mu gane mahimmancin zabin yin
addini yadda Annabi ya nuna a Madina inda ya samar da al’umma dake kunshe da
Kiristoci da yahudawa a karkashin adalcin kasa daya. Duniya ta zama dunkulalliya
a yau kuma rashin adalci na habaka ta ko’ina, dole mu kalli wancan lokaci na
baya mu gane abubuwan das u ka hadamu waje guda amatsayin mutane masu imani
maimakon yan izala, yan shi’a ko yan darika domin duk wadannan bajo da muke
makalawa juna ba wanda ya sansu lokacin da Annabi ya kafa addinin a madina.
Comments
Post a Comment