MANYAN AYYUKA: GASKE KO GANGAN?
Tun da aka kafa Nigeria ba na jin akwai wata gwamnati da ta bijiro da
manyan ayyuka masu matukar mahimmanci irin wadanda gwamnatin Buhari ta fitar
daga 2015. A zangon farko na mulkinsa na yi amfani da wadannan ayyuka wajen
rufe bakin yan adawa da karfafawa magoya bayansa gwiwa domin sake zabensa. Amma
cikin ikon Allah kafin karshen zango na farko ni kaina na fara dari-dari da
yadda yak e tafiyar da mulkinsa sakamakon irin yadda na ga wadannan manan
ayyuka na tafiyar hawainiya.
Hudu daga cikin wadannan manyan ayyuka an yi ta yada furofagandar cewar
za su kankama a watan Disamba na 2018. Cikinsu akwai tashar jirgin ruwa ta Baro
da katafaren kamfanin karafuna na Ajaokuta da kamfanin jiragen saman Nigeria da
kuma tashar wutar lantarki ta Mambila. Hakika duk wanda ya san tattalin arziki
ya san cewa idan wadannan ayyuka kadai Buhari ya aiwatar a shekaru 8 hakika ya
samarwa Nigeria tudun dafawa a matsayin babbar kasa a Afirka. Amma sai dai
kash! Watan Disamba na 2018 ya zama tarihi kuma yanzu watanni sama da bakwai
sun shude bayan nan, amma babu wata kwakkwarar shaidar wadannan ayyuka sun kai
gacin da a ke so su cimma. Abin tambaya
a nan shine ina dalili?
Tashar jiragen ruwa ta Baro, asali Buhari ne ya kirkiro aikin tun ya na
mulkin soja sama da shekaru talatin da suka wuce don haka aiki ne wanda ya ke
alfahari da shi. Daf da zaben 2019 a wani yanayi na gaggawa an yi wani
kwarya-kwaryar bikin bude wannan tasha inda shugaba Buhari da kansa ya halarta.
Watanni kusan takwas da wannan biki shiru ka ke ji game da fara aikin tashar.
An yi jita-jitar cewa tun a bayan kaddamar da tashar Buhari ya fusata saboda ya
gano cewa akwai burum-burum game da matsayin aikin samar da wannan tasha.
A kusan wannan lokaci da aka kaddamar da tashar Baro kuma wani bidiyo
wanda gidan talabijin na Al-Jazeera ya aiwatar ya yi ta zagaya tsakanin yan
Nigeria da ke nuna cewa aikin Ajaokuta ya kai kusan kashi 98% na kammalawa,
kuma ana sa ran a watan Disamba na 2018 ita ma za ta kama aiki ka’in-da’na’in.
Muna watan Yuli na 2019 amma shiru ka ke ji.
Ministan Sufurin sama a wani gagarumin biki a can kasar Ingila ya
kaddamar da samar da sabon kamfanin jiragen sama na gwamnatin tarayya, abinda
ya farantawa duk wani mai kishin Nigeria. An yi ta yayata cewa a watan Disamba
na 2018 shi ma wannan kamfani zai fara jigila ta cikin gida da kasashen waje,
har an fara daukar ma’aikata. Amma sai gashi abin ya balbalce, yanzu ko zancen
ba a yi.
Na karshe shine aikin tashar wutar lantarki ta Mambila, aiki mafi girma
da mahimmanci da wannan gwamnati ta bijiro da shi domin zai lakume kusan dala
biliyan 6. Wanna aiki zai samar da Mega Watt 3050 idan a ka kammala shi (wato
kwatankwacin abinda ake iya rarrabawa a fadin kasar a yanzu). Wannan aiki na
Mambila ya kasance aiki mafi girma irinsa a fadin Afirka kuma na 9 a duk fadin
duniya.
Katafaren kamfanin kasar China, CCCG, wanda ya gina Dam mafi girma a
duniya, wato Dam din 3 Gorges da ke kasar China shine kamfani da Buhari ya zabo
domin yin wanna aiki bayan an kori kamfani SinoHydro na kasar China daga
kwangilar a 2013. CCCG sun gina wancan dam a kasar su wanda ya ke samar da Mega
Watt 22,500 wanda ke bada wuta ta TeraWatt 98 a awa guda. Aikin wannan dam din
ya lakume dalar Amurka biliyan 31 kafin kammala shi. CCCG za su gina dam guda
uku a kan kogin Donga da ke jihar Taraba wanda su ka saka hannu a kan kwangila
ta dala biliyan 5.8 da cewar a shekaru shida zasu kammala aikin.
An yi ta tsammanin cewa shima wannan aiki a watan Disamba na 2018 zai
kankama, amma saboda irin tsarin Nigeria na rudani ga shi bayan wata bakwai
ba’a fara ba. Cikin tarnakin da wannan aiki ya samu shine na cewa asali an saka
kwamitin shugaban kasa game da jihohin arewa maso gabas (Presidential Committee
on Northeast Initiative PCNI) a cikin masu kula da yadda aikin zai gudana, sai
kuma ga shi daga baya an kafa hukumar ci gaban yankin arewa maso gaba
(Northeast Development Commission NDC) wadda ita hukuma ce ta dindindin maimako
wancan kwamiti na PCNI. Don haka an canza PCNI da NDC a matsayin masu wakilcin
kula da aikin. Wani lamarin kuma shine na kasancewar Maikatar kudi ta kasa,
kasancewar ita za ta fitar da kudaden gudunmuwa da na Nigeria za ta saka a
aikin, ita ma ta cancanci wakilci a kwamitin kula da aiwatar da aikin. To amma
jinkirin rantsar da Board na ma’aikatar ya sa ba za a iya nada wakilai ba har
sai bayan an rantsar da su. Haka kuma ita kanta ma’aikatar kudi har yanzu ba ta
iya saka wadancan kudade na ta cikin asusun wannan aiki ba tukuna. A
yarjejiniyar aiki kamfanin CCCG ne zai samar da kashi 75% na kudaden aikin ita
kuma Nigeria ta bayar da kashi 25% amma mun bar yan China na jiranmu tsawon
watanni bakwai wadanda ya kamata a ce a cikin shekaru shida na tsawon lokacin
da aikin zai dauka aka ci wadannan watanni.
Hadari da kowa ya sani shine cewa wannan jan kafa da aikin ke yi zai
iya zama hadari, domin kuwa idan APC ta fadi a zaben 2023 (abinda mai iya
faruwa ne ganin yadda siyasar kasar ke tafiya a yanzu) ba tare da cewa aikin ya
kai wani gaci da babu abinda zai sa a yi watsi da shi ba, to hakika idan PDP ta
ci mulki ana iya tsayar da aikin. Idan ba mu manta ba PDP ce ta fara kokarin
yin wannan aikin tun lokacin Obasanjo har zuwa Jonathan. Mun ga yadda Jonathan ya baiwa SinoHydro
aikin a dala biliyan 36 kafin a soke aikin.
Ba za mu iya gane mahimmancin wanna aiki ba da kuma irin hadarin da
rasa shi zai jawo mana sai mun san cewa idan da a ce kamfanin Ajaokuta zai yi
aiki ba tsayawa na tsawon shekara guda ya na samar da karafa, to duk karfen da
ya samar a shekarar, aikin Mambila zai iya lakume ilahirin karfen da za ta
samar. Wa zai iya kiyasce yawan sumunti da za’a nema wajen binne wannan karafa
a Dam uku da za’a gina? Sannan mu duba tireloli nawa za su yi jigilar wannan
karafa da sumunti? Banda kuma manyan kayan aiki da za’a kawo daga China zuwa
wajen. Gwamnatin Taraba har ta fara shirye-shirye na gina filin jirgin sama da
kuma manyan Otal domin mutane da za su shiga jihar sakamakon aikin.
Al’ummar yankin za su ci moriyar aikin ta hanyar filayen gonaki da
gwamnati za ta siye daga hannunsu, da kokarin samar da sabbin matsugunai
wadanda zai haifar da sabbin tituna, makarantun, asibitoci da sauran ayyuka ga
jama’ar garuruwan. Duk wadannan za su samu sakamakon aikin a tsawon shekaru
shida da aka dauka, amma mafi girman moriyar aikin shine idan an gama zai samar
da wuta mai karfin Mega Watt 3050, Allah kadai ya san irin gagarumin canji da
hakan zai kawo. Kamfanoni da su ka durkushe a arewa sakamakon rashin lantarki
duk za su farfado, musamman masaku wadanda ke da alaka da harkar noma. Za’a
samar da miliyoyin ayyukan yi idan aka gama wannan aiki, kuma samar da ayyuka
da yawa a arewa shine kadai mafita daga cikin tsaka mai wuya da muka sami kanmu
na ta’addanci da garkuwa da mutane.
Ko mun ki, ko mun so, Nigeria ba ta taba samun shugaba wanda talakawa
su ka amince da kuma bashi amana kamar Buhari ba amma kash! Shi kuma ya kasa
jajircewa wajen ganin ya yi abubuwa da zafi-zafi kamar yadda ya kamata ba. Idan
Buhari zai iya samar da wadannan manyan ayyuka guda hudu kacal a tsawon
mulkinsa, sai in ce ya biya talakawa. Amma gashi an cinye shekaru hudu ba tare
da wani gagarumin ci gaba a kan wadannan ayyuka ba. Yan Nigeria sun sake
amincewa Buhari wasu shekaru hudu masu zuwa, don haka wajibinsa idan ya na son
barin tarihi ya tsaya ya tabbatar da cewa akalla ko da wadannan ayyuka sun kammala.
A ganina babu wani abu da Buhari zai rasa sama da komai a rayuwarsa a yanzu
wanda ya wuce a ce ya yi shekaru takwas ba tare da tsamo Nigeria daga halin da
ya same ta ba, hakika hakan zai zama cin amanar da talakawa su ka ba shi. A
wannan karo na biyu ya sani cewa ba shi da wani uzuri idan ya kasa, domin hatta
majalisar da ake ganin ta zamar masa kadangaren bakin tulu a wancan zangon, to a wannan karon duk shugabannin majalisun biyu mutanensa ne,
don haka mu na fata shugaba Buhari ba zai rataye kansa da kansa ba a gaban
Allah da mutanen Nigeria.
Comments
Post a Comment