MUN YI WATSI DA UMARNIN KARATU


A makon da ya gabata hoton wata budurwa mai siyar da Awara a bakin titi a cikin birnin Kano wadda ke suyar awararta sannan ta na rike da littafi ta na karatu, ya karade shafin facebook tare da tofa albarkacin bakin mutane da dama. Cikin irin martini da wasu su ka bayar na cewa ba wani abin birgewa a cikin lamarin, saboda littafin soyayyar hausa ta ke karantawa ya ja hankali na wajen yin wannan mukala domin kore irin wannan tunani. Zan bada misalai da abubuwa da suka shafi rayuwata a matsayin hujja. Na farko dai tun ina dan karami aka kaimu makarantar kwana ta firamare a garin Roni, daya daga cikin kwaya biyu kacal da ake da su a wancan lokaci a fadin arewacin Najeriya. A wannan makaranta na fara karatun littafan hausa irinsu Magana Jari ce, Dare dubu da daya, Gandoki, Iliya Dan Mai Karfi da sauransu. Wannan ya bani damar gogewa wajen iya karatu da kuma sabo da shi. Wani malaminmu inyamiri Mr. Ameachi ya hada gasar karatun hausa wadda na lashe kuma aka bani sulai bakwai, kudaden farko a rayuwata da na samu na kashin kaina. Wannan ya sa na dada jajircewa wajen karance-karance. Ina zuwa sakandare sai na fara karatun littafan turanci inda na rungumi littafan James Hardly Chase, yadda duk inda na ke sai ka ga wannan littafi tare da ni duk da cewa na sha tsangwama a lokuta kasancewar a bangon littafin akwai hotunan yan mata daga su sai dan kamfai. Karance karancen littafai na hausa da turanci ya sa na sami gogewa a magana da rubutu a yaren hausa da na turanci, baya ga saka min shaukin karatu. Na karanci fannin kimiyya a sakandare amma sakamakon faduwa a darasin Physics ya katse min burina na zama masani a fannin kimiyya abinda ya tilasta min canza layi yayin da na shiga jami’a. A jami’a sai na koma kan karatun hausa da sashen addinin musulunci abinda ya bude min sabon shafi saboda na fara yin nazarin Qur’ani maimaikon takararsa kawai. Cikin lokaci kankane na fahimci cewa shi Qur’ani ya na bukatar mai karanta shi ya zama mai bincike saboda ya tabo kowanne sashe na ilimi. Wannan dabi’a ta Qur’ani ita ce ta saka daular Abasiyawa ta yi shura a duniya a lokacin da musulunci yayi shaharar da ba’a taba gani ba a baya. Ilimin da na samu a nazarin Qur’ani da kuma na kimiyya ya bani damar yin zurfafan bincike yadda na rubuta littafai tare da makaloli iri-iri a wannan fanni na kimiyya da addini, yadda har daya daga cikin jami’o’i mafi girma a duniya, wato Jami’ar Cambridge da ke kasar Birtaniya ta karrama ni a shekarar 2008.

 

Ilimi shine ginshikin rayuwar Dan Adam kuma ba za ka iya samun ilimi ba har sai ka iya karatu kuma ka saba da yin karatun. Ni’imar karatu da rubutu ita ce ta banbanta Dan Adam da duk sauran dabbobi a wannan duniya domin sakamakon ta ne, mutane su ka iya neman ilimi su adana shi, sannan su yi amfani da shi da kuma yada shi. Duk wanda ya rayu tsawon shekaru hamsin da su ka gabata shaida ne kan yadda Dan Adam ya habaka fannonin ci gaba ta hanyar ingantar ilimai na fasaha da kimiyya. Abubuwan da aka kirkiro cikin wannan shekaru hamsin, ba wanda ya ke hasashen yiwuwarsu shekaru sama da dari da su ka gabata.

Alal hakika Musulunci shine ginshikin samar da ci gaban zamani wanda kasashen yamma su ka samar, kuma ya samo asali daga lokacin da a cikin kogo a wajen garin Makka, Annabi Muhammadu ya fara karbar wahayi daga ubangijinsa yayin da Jibrilu ya ce masa “Yi Karatu” inda annabi ya tambaye shi me zai karanta. Shin Jibrilu ya sanar da shi game da sallah, azumi ko zakka ne? A’a, ya umarce shi da ya karanta yadda Allah ya halicci mutum daga gudan jini, wato kai tsaye koyarwar farko ga manzo ita ce ta kudira da kimiyyar yadda Allah ya halitta mutum. An umarci annabi ya yi nazari da bincike wajen gane yadda Allah ya halicci mafificiyar halittarsa a doron kasa. Don haka a bayyane ya ke cewa umarnin farko a musulunci shine na neman ilimi kuma musamman ilimi na rayuwa da duk wani abu a doron kasa ko da kuwa shaidan ne, domin sai ka san yadda shedan ya ke kafin ka iya kaurace masa.

Neman ilimi a musulunci, sabanin sauran addinai ba aikin malamai kawai ba ne, kowanne mutum ya wajaba ya san daidai gwargwado na ilimi. Halifofon Abasiyawa, musamman Harun Al-Rashid da dansa Al-Mamun, sun yi rawar gani a tarihi yadda musulunci ya kai kokoluwar da bai taba kaiwa ba kuma su ka mamaye duniya ta wancan lokaci da karfin ilimi. A lokacinsu fannonin kimiyya, fasaha, falsafa, likitanci da sauransu sun habaka sakamakon sun bada damar bincike da nazari, kuma yawanci abubuwa na kimiyya sun samo asali daga irin wadancan bincike na daular musulunci. Harun Al-Rashid ya gina “Baitul-Hikma” (Gidan hikima) wurin da ya kasance cibiyar nazari da binciken kimiyya ta farko na kasa-da-kasa a tarihin duniya. Garin Bagadaza, wanda kakansa Khalifa Al-Mansur ya gina a gabar tekun Tigris, a karkashin mulkin Harun Al-Rashid ya zama birni mafi girma a duniya da cigaba wanda ke da littafan da babu irinsu a duniyar wancan lokaci kafin dakarun Hulagu Khan (jikan Ghengis Khan) ya kai wa garin Bagadaza hari a shekarar 1258 inda ya mamaye garin ya kuma kashe dubban daruruwan musulmi har da Khalifansu kuma ya sa aka kwashe littafan nan aka watsa su a kogin Tigris. Wasu masana tarihi sun ruwaito cewa sai da wannan kogi ya koma baki-kirin sakamakon daruruwan dubban littatafai da tawadar su ta wanke cikin kogin. Wannan hari na yan Mangoliya shi ya durkusar da daular musulunci a Gabas ta tsakiya wadda ba ta sake farfadowa ba.

Bayan kifar da yan gidan Umayya da daular Abasiyawa su ka yi, wani bangaren na su ya yi hijira inda su ka sake kokarin kafa daular a yankin Turai na yanzu, inda su ka mamaye zirin Iberia (inda kasar Portugal da Spain su ke a yanzu) suka kafa sabuwar daula da aka kira da daular Andalusiya. Wannan daula ta yi mulki a wannan waje na kimanin kusan shekaru dari takwas. A lokacin da ta ke ganiyarta, babban birnin wannan daula shine garin Cordoba, garin da ya zama mafi shahara a duniya, tamkar ka ce New York a yanzu. Wannan gari ya zama matattarar ilimi wadda sai dai a iya gwada ta da Bagadaza, domin a tsaikonta ta na da kimanin dakunan karatu da bincike sama da saba’in a lokacin da a gaba dayan turai babu dakin karatu na jama’a ko da guda. An fassara miliyoyin littafan Girkawa zuwa larabci a wannan gari, kama daga adabi, kimiyya, falsafa da sauransu. Dalibai sun yi ta barkowa daga Jamus, Ingila da Faransa domin kwankwadar ilimai daga wannan gari, domin babu inda za’a same shi a duniya a wancan lokaci idan ba Cordoba ba. Ba kawai a koyar da ilimin su ka tsaya ba, wannan daula ta samar da masana kimiyya da fasaha wadanda su ka habaka, a zahirance, yadda ake yin noman rani, tsaron garuruwa, gina jiragen ruwa yadda jiragen su na yaki su ka mamaye tekun Bahar Rum tare da kai hare-haren sojoji har cikin turai a kasashen Faransa da Vienna. Sun kirkiro sabbin hanyoyin kai hare-hare da makamai, da na tsarin gine-gine, yadda har a gobe masallacin Alhambara ke cikin tsarin gini da Dan Adam ya sanya cikin mafi kyau a tarihin gine-gine a duniya. A wannan gari aka fara tsarin Tsangaya, yadda kowanne masallaci ke da makaranta hade da shi wadda ake koyar da yayan talakawa ilimai. Daga wannan tsari na tsangaya aka samo kusan ilahirin tsarin jami’o’i na bangare-bangare, tsarin digiri na farko zuwa digirgir da kuma tsarin rigar da ake sawa lokacin kammala karatu (Academic gown) wadda asalinta daga alkyabba ne da rawani na manyan malamai. Hatta takardar rubutu, wadda aka fara kirkirarta kimanin shekaru dubu uku kafin zuwan annabi Isa a Misra, ta isa garin Makka a shekarar 707 AD sannan sai bayan shekaru dari hudu ta isa kasar Turai a shekarar 1109 ta hanyar wannan gari na Cordoba.

Wannan birni na Cordoba ya na da bandakin wanka na jama’a kimanin 900 a lokacin da turawa basa wanka, domin hatta sarauniyar Ingila ba za ta yi wanka ba sai dai idan likitanta ya ce ta yi wanka a matsayin maganin wata larura. Larabawa a Cordoba su ka kirkiro hanyar amfani da silki domin yin kamfai da singileti saboda tsafta, a lokacin da a garin Faransa kwatoci na bude kuma ana jefo shara kan tituna a birnin London. Birnin Cordoba na da manyan tituna da ke da filawoyi a gefensa kuma ana kunna musu fitulun a-ci-bal-bal da dare har gari ya waye. Kusan shekaru dari takwas wannan gari ya ci gaba da nunawa turawa yadda ake ci gaba.

Littafai uku, wato littafin The decline and fall or Roman Empire (na Edward Gibbons) da littafin Intellectual Development of Europe (na John William Draper) da kuma littafin The Moors in Spain (Lane-Poole) sun nuna mana yadda daular Musulmi ta Andalusia ta yi wa kasashen turai fintinkau a wancan lokaci, amma kuma turawa sun tashi tsaye wajen tura mutanensu cikin wannan daula domin gano sirrin wadannan mahaya rakuma da yadda su ka gina daula irin wannan. Wannan ne ya zaburar da kokarin farfado da ilimi a turai (Enlightenment) abinda ya jawo farkawar turawa (Renaissance) wanda ya wakana tsakankanin karni na 14th zuwa na 17th, wato farkawa domin a kwaikwayi musulmi.  Al-Khwarizmi, shahararren masanin lisafi shine wanda ya kawo alamar sifiri cikin lissafi, wadda musulmi su ka aro daga Indiya, kuma abinda turawa ba su san da shi ba a wancan lokaci. Alamar sifiri ita ta canza fannonin lissafi (Math) da na Ilimin cudanyar halitta mara rai (physics) har ma da ilimin mu’amalar sinadarai (Chemistry) kuma ta nan ne aka saka dan ba ga ilimin kwamfuta da zai zo nan gaba. Musulmi masana ilimin falaki da na sararin samaniya su ne su ka sakawa yawancin taurari sunayensu da muke amfani da su har yanzu. Masanin sararin samaniya Al-Sufi, ya buga littafinsa Book on fixed stars (Littafin tsayayyun taurari) a inda shine ya fara bayyana samuwar dabakar Andromeda. Al-Biruni ya bayyana dabakar mu ta Milky Way tun a karni 11th, amma sai bayan shekaru kusan 600 a ka baiwa baturen Italiya Galileo wannan martaba ta Al Biruni. Haka nan a bangaren ilimin halitta mai rai, Al-Nafis na garin Damascus shine ya fara gano yadda jini ke gudana a jijiyoyi a cikin karni na 14th (A shekarar 1547 kuma aka fassara littafinsa cikin yaren Latin) amma sai ga shi an lakabawa masanin kimiyya Dan kasar Ingila, William Harvey, a shekarar 1628 cewa shi ya gano wannan tsari. Omar Khayyam kuma a karni na 12th ya auna tsawon shekara da cewa kwanaki 365.24219858156 ne, abinda sai a karnin da ya gabata ne babban madubin hangen nesa na Hubble da ke sararin samaniya ta hanyar kwamfuta ya tabbatar da cewa tsawon shekara kwanaki 365.241290 ne. Al-Maimon shi ne wanda ya fara iya auna fadin duniya ta hanyar yin amfani da layukan da ke doron duniya a tekun maliya, ya tabbatar da cewa duniya kamar kwallon ta ke a lokacin da cibiyoyin kiristanci a  Constantinople da Rome ke cewa duniya kamar faranti ta ke a matsayin fatawarsu. A wannan lokaci malamai a jami’o’in Andalusiya na koyar da ilimi taswirar duniya ta yin amfani da mutum-mutumi na duniya (Globe) wajen misalai. Littafin Ibn Sina, Qanun fil Tibb, wani kundin kimiyya ne wanda ya kasance mahimmin littafin kimiyya wanda ake koyar da dalibai da shi a jami’o’in Montpelier da na Louvre da ke Faransa har zuwa tsakiyar karni na 17th. Ayyukan Ibn Rushid (Averroes 1126-1298) a fannin falsafanci shine ginshikin falsafanci na yammacin turai a yanzu, kuma shine wanda ya fara gano digo-digo da ke kan rana. Malaman musulunci sun yi ayyuka da dama a fannoni samar da karafa da tantance su abinda ya jawo juyin juya halin masana’antu a karni na 17 a Ingila. Babu wani sashe na kimiyya da fasaha wanda musulmi ba su bada gagarumar gudunmuwa ba, musamman idan ka yi la’akari da kalmomin da turanci ya ara daga Larabci wadanda daga ciki akwai kalmomi irinsu Alkali, Alchemy, Algorithm, Average, Alcohol, Almanac, Aorta, Admiral, Alcohol, Algebra, Syrup, Julep, Elixir, Chemise, Cotton, Cipher, Carat, Zenith da sauransu. A wancan lokaci, kamar yadda turanci ya ke a yanzu a matsayin yaren duniya na ilimi, haka larabci ya ke. Idan muka juya kan marubuta tarihi, ba wanda zai hada kafada da Ibn Batuta, saboda sabanin marubuta tarihi irinsu Democritus wanda ake gani babu kamarsa a turawa, shi Batuta yawo yayi kasa-kasa ya na kallon abubuwa ya na rubuta nasa tarihin. An kiyasce cewa ya ratsa kusan ilahirin kasashen duniya na wancan lokaci (har nan kasar hausa ya zo) inda ya yi tafiye-tafiye na kimanin kilomita 192,000 a zamanin da babu mota, jirgin kasa da na sama.

 

A karshe ya kamata mu gane cewa ilimi shine ginshikin rayuwa kuma shine abinda ya baiwa Dan Adam damar kasancewa halitta mafi karfin iko a doron duniya. Mun faro daga yan kalilan mutane da ke yawon farauta, muka fara samar da kauyuka muna noma, a yau gashi mun mamaye wannan duniyar ta kowacce fuska har ma mun fara mamayar sararin samaniya. Alkur’ani ya umarce mu da yin karatu a matsayin umarninsa na farko, don haka wajibi ne a kan mu jajircewa mu koyi dabi’ar muhimmantar da ilimi sama da komai, domin mun ga yadda magabatanmu su ka mamaye duniya sakamakon ilimi amma mun zama koma baya sakamakon watsar da shi. Wajibi ne mu gane cewa umarnin Allah cikin suratul Jasiya

 

Q45:3-5 "Lalle ne cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga masu imani. Kuma a cikin halittarku da abinda ke watsuwa na dabbobi akwai ayoyi ga mutane masu yakini. Kuma da sabawar dare da yini da abinda Allah ya saukar daga sama na arziki, sannan ya rayar da kasa game da shi a bayan mutuwarta, da juyawar iskoki, akwai ayoyi ga mutane masu yin hankali”

 

A takaice Allah na son mu yi nazarin fannonin ilimi da ya ambata a wannan aya wadanda su ka jibanci ilimin Sararin samaniya (Astronomy) da Taswirar Duniya (Geography) da na wanzuwar halitta mara rai (Physics) da na cudanyar sanadarai (Chemistry), da Yanayin sararin saman duniya (Meteorology) da ilimin Teku (Oceanography) da na halittu masu Rai (Biology) da na Asalin halittu (Evolution) da ilimin Dabbobi (Zoology) da na Tsirrai (Botany) da kuma na Tarihi (History) da Imani (Spirituality). Cikin wadannan ilimai, Dan Adam zai iya gane karfin ikon da Allah ya hore masa, da kuma gane dalilin da aka halitta shi, domin a duk fannoni zai gane sa hannun ubangiji wanda ya halitta ya kuma tsara komai.

 


Comments

Popular posts from this blog

ALAMUN TSINUWA...

Dabara Ta Rage Wa Mai Shiga Rijiya…

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?