MUTUWAR ABBA KYARI WA’AZI CE
Hakika ba wata tantama
cewar a tarihin mulkin siyasa a Nijeriya ba’a taba samun shugaban maikatan
fadar shugaban kasa mai karfin iko irin Abba Kyari ba (Sai dai ko a lokacin
mulkin soja inda Abba Al-Mustapha ya kwatanta irin wanna iko). Abba Kyari dai
ya koma ga ubangijinsa amma ya bar yamadidi tsakanin yan Najieriya, wasu na
yabonsa wasu na suka. Ita mutuwa a kowane lokaci ta faru, a kan sami wadanda ke
alhinin rashin da wadanda kuma ke murna. Abu mafi mahimmanci a game da kowacce
mutuwa shine ta zama wa’azi ga wadanda ke raye tare da yi musu izina a
yunkurinsu na gyara rayuwarsu ta zama mafi alheri saboda tabbacin cewa ba wanda
zai dawwama.
Idan muka duba tarihi,
hatta fiyayyen halitta, a lokacin da ana tsaka da yakin Uhudu sai aka rika yada
jita-jitar cewa ya mutu, abinda ya jefa rudani da dimuwa cikin musulmi a daidai
lokacin da Kuraishawan Makka suka kama murna. Haka nan a yayin da sayyada
Maryamu ke kallo aka tsire Annabi Isa, a daya gefen Yahudawa ne ke murnar cewa
an kashe almasihu. Lokacin da katsam aka sanar da mutuwar Sani Abacha, wasu
sassan Najeriya sun barke da murna har da fitowa kan tituna, yayin da wani
sashen ya shiga zaman makoki. Shi ma Yar’Adua a yayin da na kusa da shi ke
tararrabi da jan kafa wajen sanar da mutuwarsa wasu sun kebe kansu domin shawarar yadda zasu karbi mulki. A lokacin da
sojojin Burutai su ka kashe daruruwan yan shi’a a gyallesu, wasu yan Sunna sun
kama murnar hakan. Don haka mu gane cewa halayyar dan Adam a kullum game da
mamata ita ce, lokacin da abokai da iyalai ke jimami, su kuma makiya murna su
ke yi. Mashahurin marubuci Shakespeare, a wani rabin shagube ya na cewa
“Sharrin da mutum ya shuka a rayuwarsa na binsa har bayan ransa” yayin da
Qur’ani ya zo da cikakken zance cikin suratul Zalzala Quran 99:6-8 “A ranar da mutane za su fito daban-daban domin a nuna mu
su ayyukansu, To wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra na alheri
zai ganshi, kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri zai ganshi”
Wato a tsarin adalci
na ubangiji duk abinda ka shuka shi zaka girba in hairan ne to hairan, haka
zalika idan kayi sharran zai dawo maka. Shi ne ya sa a ranar lahira yayin da
aka kawo sakamakon ayyuka, wasu za su koka yadda za’a nuna musu wani aikinsu na
sharri wanda tuni sun manta sun aikata shi inda za su ce Quran 18:49 “…Kaicon mu! Menene ga wannan littafi baya barin karama
kuma baya barin babba (na laifi) sai ya kididdige?” Wannan ya isa ya ja
kunnuwanmu mu saduda cewa aikinmu shine sakamakon mu kuma mutuwar kowanne irin
mutum ya cancanci ta zamar mana tunatarwa domin mu gyara kafin lokaci ya kure.
Halayyar mu a wannan
zamani ta yabon duk wanda ya mutu (musamman masu iko ko mawadata) na nuna irin
munafincinmu. Hakika ba wanda zai iya yankewa wani mahaluki hukunci sai Allah
amma wannan bai hana mu lura da yadda mutum ya rayu ba wajen zama mana izina
domin gyara tamu rayuwar da zama wa’azi yadda mutane za su rika hankoron yin
alheri sabanin sharri. Manzon Allah ya ce abubuwa uku basa yankewa mamaci: wato
duk wata sadakatul jariya da ya bari a baya zata ci gaba da zama hanyar samun
ladansa, sannan idan ya yada ilimi na alheri shi ma ba ya yankewa da kuma barin
zuri’a ta-gari wadda zata rika yi masa addu’a. Wadannan abubuwa kamar yadda
zasu dorar da alheri haka sabaninsu ke dorar da sharrin da mutum ya aikata
bayan ya mutu yadda zai ci gaba da samu a matsayin alhaki da ba ya yankewa. Game
da Abba Kyari, idan mu ka kau da kai da zargin cin hanci na Naira miliyan 500 a
badakalar MTN, ko hannunsa wajen sa a kori Oyo-Ita da kuma tuhumarta, da zance wasikar
korafin Monguno, ko jita-jitar dankwafe mataimakin shugaban kasa, har da dokar
hana Ministoci ganin shugaban kasa sai ya sahale, da maganar cin hanci wadda
gidan talabijin na Berkete ya yi makonni ya na nunawa tsakaninsa da wani wanda
ya ce dan’uwansa ne, hakika bai kamata mu kau da kai da maganar annobar Kwarona
ba.
Idan ba mu manta ba, ana tsaka da wannan annoba Abba Kyari ya
kwashi tawaga zuwa Jamus a lokacin da kasashe ke kokarin rufe kan iyakokinsu. A
daidai wannan lokaci mun yi ta kiraye-kiraye da gwamnatin Najeriya ta rufe
iyakokinta amma saboda irinsu Abba Kyari na kasashen waje an ki daukar wannan
mataki. Su Abba Kyari sun dawo Najeriya ba tare da killace kansu ba duk da
sanin cewa sun fito daga kasa wadda a wannan lokaci ke cikin wadanda annobar ta
watsu sosai. Wannan halayya ta saba wa umarnin addini da tsarin hukumomin
lafiya na duniya, amma duk da cewa sun shigo kasar maimakon su killace kansu
ayi musu gwaji sai gashi Abba Kyari ya halarci manyan taruka a kasar inda
yawancin shugabanninmu, har da shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnoni, su ka
halarta. Sai da alamun cutar su ka bayyana sosai sannan ya killace kansa bayan
ya yada cutar. A ranar 27 ga watan Maris da a ka yi sanarwar Abba Kyari ya kamu
da Kwarona a duk fadin kasar nan mutane 61 ne kacal ke da ita. Ba sai na yi
bayanin abinda ya biyo baya daga waccan rana zuwa yanzu ba.
Darasin farko da ya kamata mutuwar Abba Kyari ta bamu shine
gwamnati da al’umma za ta ci gaba da gudana ba lalle sai da wani mahaluki ba
komai mahimmancinsa, kuma duk yadda kake da iko wata rana sunanka matacce, idan
ka mutu kuma sai abinda ka bari a baya shine kadai zai rage don haka ka yi
kokarin barin alheri kawai. Wannan annoba ya kamata ta saka hankalin
shugabanninmu ya dawo jikinsu su gane cewa su na da hanyoyi biyu da za su runguma wajen kawo canjin da ake
bukata. Na farko shine dole su cire son kai game da sha’anin shugabanci
musamman wajen yakar wannan cuta domin a dakile ta da kuma sake lale wajen
tsara harkokin tattalin arzikin kasar nan. Dangane da maganar Kwarona hatta
mutane a kasashe masu karfin tattalin arziki sun fara gajiya da kulle a gida
domin a Amurka an fara zanga-zanga bude garuruwa. Don haka mu gane cewa kulle
na tsawon lokaci ba namu ba ne. A wannan shekara gwamnatin tarayya ta yi
kasafin kudi na Tiriliyan goma amma abin takaici Naira biliyan 46 kacal (wato kaso 0.4%) a ka warewa fannin lafiya. Ya
ilahi ko kashi guda ya gagara a warewa lafiya kuma a daidai lokacin da shugaban
gwamanti ya yi shekaru da dama kafin hawansa mulki yana caccakar shugabanni cewa
sun kasa komai a harkar lafiya, shugaban da ya sha fama da jiyya tsawon watanni
a asibitin ketare. Shi kansa marigayi Abba Kyari ya mutu a asibiti a Lagos,
wanda da duniya lafiya ta ke, da sai dai a kai shi turai, amma da shi aka tsara
da sahale baiwa harkar lafiya ta mutane miliyan dari biyu Naira biliyan 46 a
kasafin Naira Tiriliyan Goma. Ina ma a ce gwamnatin ta iya ware kaso 15%, wato
matakin da kungiyar hadin kan Afirka ta cimma na kason kasafin kudi na kasashe day
a cancanta su rika sawa a harkar lafiya, abinda wannan gwamnati ta amince da shit
a rattaba hannu a kai. Amma mu na gani a cikin wannan kasafin kudi an ware
biliyan 37 domin gyaran ofisoshin yan majalisa da ke Abuja. Wannan gwamanti ta
kafa tarihi wajen ciyo basuka a kasashen ketere, kuma a halin yanzu kasar nan
na biyan kaso 23% na kasafin kudinta wajen biyan kudaden ruwa na bashi duk
shekara. A bana ana sa ran zamu saka Naira Tiriliyan 2.3 wajen biyan bashi,
kudaden da za’a iya gina asibitoci na
Naira miliyan 600 a kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar nan.
Yadda kasuwar mai ke faduwa a
duniya (kuma babu alamar sauki daga nan zuwa badi) wajibi Najeriya ta farka
wajen ganin ta kawar da kan ta daga dogaro da mai, dan abinda ya rage mata ta
karkatar da shi zuwa samar da jari ga kananan sana’o’i ta hanyar bankin Nirsal
wanda babu ajiyar kadara kafin samun bashi. Samar da irin wadannan basuka cikin
gaggawa shi zai kawo habakar tattalin arziki kuma ya bunkasa masana’antu yadda
za’a rage shigo da kayan da ake bukata daga kasashen waje. A halin yanzu wannan
tsari na Nirsal ba ya tafiya daidai domin akwai wadanda sun mika takardunsu
sama da shekara amma shiru kake ji. Dole gwamnati ta daina waka game da bunkasa
noma, ta nemo sabon tsari domin tallafawa noma da gaske. Shirin Anchor borrower
ba zai kaimu ko’ina ba saboda an dabaibaye shi da siyasa da cin hancin, kuma
kudaden basa dawowa lalitar gwamnati.
Ya kamata mu kwaikwayi China yadda
ta ceto mutane sama da miliyan 850 daga cikin talauci tun daga shekarar 1981, yadda
a duk shekara mutane sama da miliyan ashirin ake cetowa daga talauci. A 1981
China na da kaso 88% na talakawa amma zuwa shekarar 2015 sun dawo kasa da kaso 1%
(wato 0.7% kacal). Ba irin namu yaki da
talaucin da a ke cewa an ciro mutane miliyan uku da baki ba, saboda ana baiwa
mutane dubu biyar a wata (kudaden da ko rabin buhun shinkafa ba zasu siya maka
ba). Muna da mafita a harkar noma da samarwa matasa jari. Duk wani kalubale da
ya zo maka idan ka yi amfani da basira ya kan zamar maka alheri, don haka
lokaci ya yi da wannan annoba za ta saita tunanin mu mu gane cewa zaman
lafiyarmu shine shugabanni su rike amanar Allah su yi ayyuka da za su kawo ci
gaba a kasarsu. Wannan masifa ta kwarona ba babba ba yaro baya ga rugurguza
tattalin arziki na kasashe da ta ke yi. Shugabanni su sani cewa mai da ake
takama da shi ya zama abin banza a yau domin ga man an tara amma an rasa me
saye, idan kuma an sami mai sayen to kudin basu isa na wahalar da ake hako shi
ba..
A karshe mu gane cewa Abba Kyari
dai ya gama ta sa rayuwar ya mutu, kuma
ni ko kai zamu iya bin sa a yau ko gobe, amma da yawanmu wannan annoba za ta
tafi ta barsu a baya, don haka yadda muka tunkari wannan annoba da irin matakan
da muke dauka a yau, hakika su ne za su yi tasiri a kan yadda rayuwarmu za ta
kasance nan da shekaru masu zuwa.
Comments
Post a Comment