RUFE KAN IYAKA: ILLA DA NASARORINTA
Ranar 3 ga watan Nuwamba shugaba Buhari ya jaddada kudurin tsawaita rufe kan iyakokin Nigeria har zuwa karshen watan Janairu bayan kimanin watanni biyu da bodojin kasar su ka kasance a rufe. Hakika rufe kan iyakoki ya jawo cece-kuce da mabanbantan ra’ayoyi tsakanin masu goyon bayan hakan da masu adawa da shirin.
Duk wani tsari a duniya, na daidaikun mutane ko na jama’a idan aka yi nazarinsa sai an tarar da illoli da alfanun wannan abu, sai dai a kullum yin adalci shine aza sikeli domin tantancewa tsakanin illa da amfani wane ne ya fi rinjaye. Ko a addinance mun ga yadda Allah ke sanar da mu cewa ko a lahira sikeli zai aza mana domin tantance mutanen kirki da na banza. Don haka wajibinmu ne a koda yaushe zamu yanke wani hukunci idan dai har muna son yin adalci mu azawa abin sikeli.
Hakika rufe iyakokin Nigeria ya jefa miliyoyin mutane, ba ma a nan kasar ba har makwabtan kasashe irinsu Benin, Niger, Ivory Coast da Ghana da ma wadanda su ke wata uwa duniya kamar su Indonesia da Malaysia da ke shigo mana da shinkafa. A daya bangaren kuma, kasarmu kasancewar akwai wasu abubuwa da mu ka fi kowa yawan sarrafa su a yankin Afirka ta yamma, misali kayan robobi, kamfunan mu sun sami nakasu wajen fitar da irin wadannan kayayyaki. Hakika wannan tsari ya kawo hauhauwar kayayyaki da kunci ga yan kasa a yanayi wanda dama a cikin mummunan matsi a ke.
Babban kuskuren gwamnati ba daukar matsayin rufe bodar ba ne sai dai rashin yin cikkaken shiri na wayar da kan mutane tun kafin a aiwatar da shirin tare da samar da hanyoyin da za su rage radadi da kunci da mutane zasu fuskanta sakanmakon shirin. Rufe boda na da matukar amfani ga tattalin arzikin kasar nan idan mu ka yi la’akari da yadda iyakokin kasar su ka kasance a bude yadda ake iya shigowa da abubuwa wadanda bas u dace ba ko su ked a mummunar illa ga tsaro da tattalin arzikin kasar.
Babu wata kasa a duniya da zata saka ido a rika illatar da tattalin arzikinta da tsaronta. Don haka yanke shawarar rufe iyakokin ya na da mahimmanci matuka sai dai kawai kamar yadda na fada Allah ya hada mu da wata kurmar gwamnati wadda jami’anta bas u damu da wayar da kan mutane game da manufofinta ba. Duk kyaun tsari mutane ba za su taba ganin alherinsa ba idan bas u san ainihin kyaun abin ba, shi kuma hakki ne na gwamnati ta tabbatar ta wayar da kan yan kasar ta domin samun goyon bayansu. Menene amfani gidan talabijin na NTA, NOA ma’aikatar yada labarai ta tarin masu baiwa shugaban kasa shawara?
Cikin amfani na gajeren zango da rufe kan iyakoki ya haifar shine a kalla a yanzu idan ka shiga kasuwannin mu kasha 80% na shinkafar da ake siyarwa zaka samu wadda aka noma ce a cikin gida, duk da cewa farashin ta bai sauka ba (wannan sai an kwana biyu). Sannan kuma yawaitar makamai da ake shigowa das u wadanda ke ta’azzara rashin tsaro a kasar ya ragu sosai baya ga samun makudan kudaden shiga da hukumomi da ke tsaron kan iyaka ke Tarawa a kullum. Hakika duk wadannan abubuwa sun tabbata a tsawon watanni biyu das u ka gabata kuma zasu ci gaba da habaka daga nan zuwa watan janairu da aka tsawaita shirin. Sannan a fannin alfanu na dogon zango, wannan rufe iyakoki zai zaburar da kafa kamfuna a cikin kasa wadanda zai samar da ayyukan yi ga matasa tare da inganta kayayyaki da ake sarrafawa a cikin gida. Idan aka sami habakar masana’antu (industry) da samar da kayayyaki (manufacture) hakika tattalin arziki zai habaka sannan aikin yi zai karu wanda rashin shi ke haifar da rashin tsaro da muke fuskanta.
To amma fa duk da wadannan alfanu da rufe iyakokin zai haifar, idan hard a gaske gwamnati ke yi kuma tan a son wannan tsari ya yi tasirin day a dace dole sai ta dora wajen samar da yanayi a cikin kasa wanda zai tallafi harkokin nomad a na masana’antu. Idan ka rufe boda ba ka iya samar da yanayi day an kasar ka zasu inganta kayayyakinsu ba, to tamkar tsiyaya ruwa a Kwando ne. Musamman harkar noman shinkafar nan, duk da cewa a cikin shekaru uku das u ka gabata, kowa ya ga yadda aka sami nasarar habaka noman shinkafa yadda muka rage shigo da ita kuma mu ka kasance kasar da ta fi kowacce yawan nomata a Afirka. Hakika wannan ci gaba ne gagarumi, amma kada mu manta cewa har yanzu shinkafar da muke nomawa bat a ishe mu a cikin gida ba kuma kamata ya yi a ce duk kasashen Afirka ta yamma mu ke samar musu da shinkafa. Tsarin bashin manoma (Anchor Borrower) da ake amfani das hi ya na da nakasu kuma halayyar mu ta cin hanci da rashawa sun dakile shirin. Misali a jihar Kano gwamnati ta rabawa manoman shinkafa, kaskashin kungiyarsu ta RIFAN (wadda ked a membobi sama da dubu dari) bashin day a kai na naira biliyan Goma amma kawo yanzu manoman das u ka ci gajiyar bas u iya mayar da abinda ya wuce naira miliyan dari ba (wato kashi 1% kenan). Duk da cewa bashin ba kudi a ke baiwa manoman ba, sai dai kayan aiki na noma irinsu taki, feshi da famfon ban ruwa. Yawanci wadanda su ka karbi basukan kayan aikin zaka samu nan take su ke siyar das hi domin wasu yan siyasa ne da zauna gari ke kutsawa su karbi bashin. Akwai wanda y ace min famfon ban ruwa da ake bada shi a Naira dubu 34 sai ka tarar an siyar das hi dubu 18. Maganar gaskiya wannan tsari na Anchor Borrower siyasa ce kawai ake son yi domin ba wata gwamnati indai da gaske ta ke yi domin habaka nomad a ke bin irin wannan tsari. Magana ta gaskiya it ace gwamnati ta maida hankali wajen samar da tallafin noma ga manoman gaske. Yadda ake yi a kowacce kasa shine a fitar da tallafin noma ta hanyar sassauta taki, iri, feshi, injunan ban ruwa, turaktoci da sauran kayan aikin gona yadda duk wanda manomi ne na gaske zai saka kudinsa ya siya. Sannan a tabbatar duk wani manomi ya sami inshore (kuma ina amfanin banki NAIC da muke das hi?) sannan idan y agama nomansa ya girbe amfanin gonarsa sai gwamnati ta zo ta siya kai tsaye a farashi mai daraja.
A yan shekarun nan gwamnati ta saka biliyoyin kudade a harkar noman shinkafa, kudaden day a kamata a ce an yi amfani das u wajen samar da cibiyoyi na dindindin da zasu samarwa manoma wancan tsari da zai tabbatar duk manomi zai iya siyen taki da kayan feshi da kayan aiki cikin sauki. Sannan wajibi ne a kafa cibiyar hada-hadar amfani gona (wato irin marketing board a baya wadda turawa su ka yi amfani da ita a cinikin auduga da gyada). Duk duniya haka ake tallfawa manoma ba basu bashi ba. Shi bashin noma ga wanda duk ke bukatarsa shi ya sa aka samar da bankunan NACB da BOA sai ya je ya karbar ko biliyan nawa yake bukata. Amma Magana ta gaskiya idan da gaske noman ake da niyyar yi to wajibi a rabu da bada bashi a koma samar da tallafin noma. A kasar China su kan je su share kamar hectar 1000 a kira manoma a raba musu fili sannan a basu iris u shuka su kula das hi har ya isa girbi, sai a zo a girbe musu sannan a auna iya abinda su ka samu. Gwamnati za ta sayi duk yawan buhunan das u ka samar a farashi mai daraja sannan a cire kudin fili, da iri da girbi a basu ragowar. Wannan shine tallafin noma, kuma hanyar da zamu bi wajen tabbar da mutane sun rungumi noma ba don cin abinci ba don samun riba a matsayin kasuwanci. Haka abin ya kamata ya kasance a fannin masana’antu.
Don haka duk da cewa rufe boda na da amfani, matukar ba a saka tallafin nomad a na masana’antu ba, rufe boda ba zai yi tasiri na dogon zango ba sai dai kawai ya wahalar day an kasa da sake tsunduma su a talauci, wanda shine babban hadarin da wannan gwamnati ta ke fuskanta.

Comments
Post a Comment