SARKI SANUSI: GABA KURA BAYA SAYAKI


Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafe sai ya cire Sarki Sunusi daga kan karagarsa ko ta halin kaka, sakamakon sabani  da ya samo asali tun a wurin taron manyan Arewa da aka yi a Kaduna. Sarki Sunusi a halayyarsa ta fadar abubuwa a wurin da ba mahallinsu ba, ya sha jefa shi cikin cece-kuce. Yawancin lokatai, Sarkin na fadar abinda ya k e gaskiya ne amma a wurin da bai kamata ba. A wannan taro na Kaduna a gaban manyan Arewa ya caccaki gwamnatin Ganduje da kokarin amfani da kudaden jama’a ba bisa fa’ida ba, na kokarin gina titin dogo a birnin Kano wanda zai lakume kimanin Naira Biliyan 432. Hakika birnin Kano na da bukatu mahimmai wadanda su ka fi titin jirgin kasa mahimmanci, sannan kudin ya yi yawan gaske yadda idan aka karkata su zuwa harkokin samar da ruwan sha, wutar lantarki da ilimi hakika sai sun fi mahimmanci ga talakawa. Duk da cewa wannan suka da Sunusi ya yi, ta taimaka wajen dakile maganar wannan kwangila amma kuma ta kunna wutar gaba tsakaninsa da Gwamna Ganduje.

 

A yayin da wannan gaba ta ci gaba da tsamari tsakanin manyan biyu na Kano, yan baranda daga kowanne bangare sun ci gaba da hura wutar rikicin domin biyan bukatunsu. Duk da cewa wasu a bayan Fage sun yi kokarin sasanci tsakaninsu, amma dai abin ya faskara. Alal Hakika mutum guda da zai iya wannan sasantawar ta kuma yiwu shine shugaba Buhari amma sai ya ki saka bakinsa. Yayin da zaben 2019 ya karato, sai Sarkin ya kara hurawa wutar kalanzir ta hanyar goyon bayan yan Kwankwasiyya a zaben Gwamna, a tunaninsa cewa ta haka zai yi maganin matsin lamba da ya ke sha daga wajen Ganduje. Ba’a taba zaben gwamna mai zafi irin wanda a ka yi a 2019 ba, kuma kowa yaga yadda wasu manya a APC a gwamnatin tarayya su ka yi kane-kane wajen zaben, saboda tunanin zabe mai zuwa na 2023.

Wannan caca da Sarki ya yi, ta kuskure domin Ganduje na sake dare kujerar Gwamna a karo na biyu, sai ya fito da sabbin hanyoyi muzgunawa Sarkin da masarautarsa. Abinda ya faru na nan kusa shine, kasancewar kotu ta soke masauratu 4 da Ganduje ya kirkiro, sai Gwamnan ya sake turawa majalisa sabon kuduri na sake maida su. Kasancewar yan majalisa sun gaggauta sahalewa sake sabbin masarautun, nan da nan sai Ganduje ya nada Sarki Sunusi a matsayin sabon shugaban majalisar sarakuna ta Kano amma da sharadin wannan mukami zai rika zagayawa tsakanin masarautun duk bayan shekaru biyu. Alal hakika wannan kudiri na Ganduje tarko ne ya dana wa Sarki domin idan ya amince da wannan sabon mukami, to ya nuna cewa ya yarda da kirkirar sabbin masarautun kenan, abinda zai gurgunta ikon da ya ke da shi a baya na shugaban majalisar sarakuna na dindindin. Nan da shekaru biyu dole ya hakura da shugabancin ya baiwa wani. A daya hannun kuma, idan ya ki kiran taron kaddamar da sabuwar majalisar sarakunan, Ganduje na iya yin amfani da sabuwar dokar masarauta wadda ta ba shi damar ladabtarwa har ma da cire Sarki. A takaice da Ganduje ya saka Sarkin a tsaka mai wuya, wato gaba kura baya sayaki.

Wannan badakala ta masauratar Kano ba sabon abu ba ne domin dai tarihi ne ke maimaita kansa. Kimanin shekaru hamsin da su ka wuce an sami irin wannan takaddama tsakanin Sarki Sunusi (Kakan wannan sarkin na yanzu) da Firimiyan jihar Arewa, Sardaunan Sokoto. Amma a wancan lokaci saboda akwai dattaku da girmama masarauta da kuma kare martabar mutum, ba’a ga hauma-hauma irin wadda mu ke gani a yanzu ba. Duk da cewa Sardauna ya yi amfani da karfin gwamnati amma bai wuce gona da iri irinta Ganduje ba wajen tsayar da rigimar tsakinsu ba tare da jefa dukkan al’umma cikin rikicin ba. Sardauna sai kawai ya tilastawa Sir Sunusi yin murabus ba tare da taba masarauta ba, abinda ya kebance mutane daga rarrabuwar kawuna irin na yanzu. Shi kuma Sarki Sunusi a nasa bangaren sai ya kare kimarsa ta hanyar kin ja da gwamnati ya yi murabus salu-alun. Sarki Sunusi ya ajiye kujerar ya yarda aka kai shi garin Azare gudun hijira amma Allah cikin ikonsa har ya mutu ya na da gagarumar kima a idon duniya yadda a kullum gidansa ya zama wajen ziyara. An dade ba’a kuma ga wani wanda ya mutu ya tara al’umma kamarsa ba.

Masarautar Kano na daya daga cikin wadanda ba a Afirka kawai ba, har ma a duniya da ta fi tsufa kuma take wanzuwa har yau. Gidan Rumfa (Wato Gidan Sarki na yanzu) shine fada mafi tsufa wadda ake zaune har yanzu a cikinta a duk fadin Najeriya, domin tun a karni na sha biyar (1463-1499) aka gina ta kuma sarakunan Kano ke zama a cikinta kawo yanzu. Daga kan Sarkin Kano na farko, wato Bagauda (AD 999) zuwa sarki Sunusi na biyu an yi sarakuna guda 57, wadanda a yanzu duk sun zama tarihi amma ita masarautar na nan daram. A bangaren gwamnoni kuwa kama daga kan Audu Bako zuwa Ganduje an sami gwamnoni 18 a Kano wadanda su ma sun zama tarihi, kuma shi Gandujen da ke kan mulki a yau, nan da shekaru uku masu zuwa zai bi sahunsu.

Don haka ya kamata Ganduje da Sunusi su kwaikwayi magabatansu (Sardana da Sunusi na daya) wadanda dukkansu sun zama tarihi a yau, wajen warware wannan rikici cikin ruwan sanyi. Rigimar ta su ta nuna cewa Kano ta zama saura, yadda babu hadin kai da son juna irin na baya domin manya da kanana sun kasa haduwa waje guda domin su kare masarautarsu da kimar shugabancinsu. Ya tabbata cewa tarbiyar da magabata su ka bar mana ta son juna da kare muradin juna wanda a ka san Kano da shi a baya, kuma shine abinda ya daukaka sunan Kano ya ratsa Hamada har zuwa Turai sannan ya ratso kudu har zuwa tekun Atalantika. Kada mu manta cewa Annabi ya shawarce mu da cewa wanda duk ke neman halaka sai ya…

Dauki hassada, wadda zata saka shi zama aminin shaidan

Ya kuma zabi rowa, wadda zata bude masa kofofin wuta

Amma wanda ke son shiga Aljanna a duniya da lahira sai ya zabi yin alheri ga danuwansa.

Zabi ya rage namu, shin zamu koma mu dauki tarbiyar iyaye da kakanni wadda musulunci ya koya mana ta so da kulawa da juna ko kuwa zamu ci gaba a wannan mummunar hanya da muka dauka ta son kawunanmu kawai?

                

Comments

Popular posts from this blog

ALAMUN TSINUWA...

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

Dabara Ta Rage Wa Mai Shiga Rijiya…