SARKIN KANO DA GWANINTAR IYA SUKA


Duk wanda ya sami tattaunnawa da Sarki Kano, babu makawa zai sami kansa cike da mamaki na irin basira, ilimi da iya Maganarsa. Ba zan manta da samun kaina a a irin wannan yanayi ba, wasu shekaru a baya, da muka sami zama da shi, mu ka yi doguwar tattaunawa a gidansa na Gandun Albasa tun kafin ya zama sarkin Kano. Duk da cewa abubuwa biyu da muka tattauna a wannan rana, wato maganar jefe mazinata wadda a  lokacin su ka yi ta takaddama da marigayi Sheik Jafar, sannan da maganar cire kakansa Sunusi Murabus wanda Sardauna ya yi, na sami karuwa ta ilimi sosai a kan wandannan maudu’ai da muka tattauna. Na kasance a wannan lokaci ina yin bincike domin wallafa littafi na a kan jefewa sannan kuma kasancewar babban yayana, ya na auren yar sarki Sunusi wato goggon Sunusi Lamido, wadda na taso a gidansu, labarin wahalar da iyalan sarki Sunusi su ka fuskanta ba sabon abu bane a wajena, amma dai na karu da wasu abubuwan da ban taba ji ba a lokacin. Sunusi Lamido bai taba boye burinsa na gadar kakansa ba, kuma a duk inda ya sami dama ya na nuna hakan. A gaskiya Sunusi Lamido na cikin jerin wadanda su ka karfafa min gwiwa wajen zama marubuci a jarida, ta hanyar yadda su ka kasance su na rubutu cike da ilimi da hujja ba tare da tsoro ba.

Sunusi Lamido ya kasance gwarzo wanda ba ya tsoron tattauna kowanne irin lamari ba tare da tsoron cewa zai sosawa wa su rai ba. Hakan ya saka shi cikin rigingimu da manyan mutane iri-iri kama daga yan majalisa na kasa, Manyan ma’aikatan banki, Gwamnoni har ma da shugaban kasa. Irin wannan jajircewa ta shi na cikin dalilan da ya sa marigayi Yar’ Adua ya ba shi mukamin Gwamnan babban bankin Nigeria. Kuma irin wannan halayyar dai ita ce ta sa shugaba Jonathan ya kore shi daga mukamin, sakamakon bankado badakalar kudade da ya yi a karkashin wannan gwamnati.

Sunusi Lamido ya kasance cikin tsiraran yan Afirka wadanda su ka shiga cikin jerin sunaye 100 na mutane da su ka fi tasiri a duniya. Maganganu da hasashen sa a fagen tattalin arziki wani lokaci sai ka ga kamar wahayi a ka yi masa.

Sakamakon takun saka tsakanin Kwankwaso da shugaba Jonathan, Sunusi Lamido ya sami damar cikar babban burinsa na zama sarkin Kano, bayan mutuwar Ado Bayero. Ranar da aka rantsar da shi a matsayin Sarki, ba zan manta ba muna tare da wasu abokaina muna ta murna, sai wani ya ce “To, daga yau dai an yi maganin surutunsa” nan take na bashi amsa da cewa ko kadan abin da ya ke zato ba zai faru ba. Domin a sanin da na yi wa Sarkin, na tabbatar rawani ba zai hana shi tsoma baki a inda ya ke so ba. Abokin musu na ya ce dokar kasa ta hana sarakuna tsoma baki cikin harkokin siyasa, sai na ce masa duk da haka, rawanin sarki ba zai iya zama masa takunkumi ba. A yanzu dai na san kowa ya gani a zahiri cewa sarki ba zai daina surutu ba. Tashin farko da gwamnatin da ta dora shi kan kagara su ka fara artabu game da ciyar da Almajirai a fadarsa, saboda a lokacin Kwankwaso ya sa a kame Almajirai. Allah dai ya taimaki sarkin saboda Kwankwaso ya zo karshen mulkinsa a karo na biyu.

Sarki ya karkata sukarsa zuwa ga gwamanatin Buhari game da matsalar tattalin arziki da a ka shiga tare da bada shawarar cewa lallai Buhari ya kafa kwamitin tattalin arziki na kasa tare da karya darajar Naira idan a na son a dakile faduwar darajarta. Shawarwarin da har shugabar bankin duniya, Legarde, sai da ta zo Nigeria takanas domin ganin an aiwatar da ita, amma Buharin ya yi kunnen uwar shegu da su. Duk da kin bin wannan shawara ta wadanda su ke ganin kansu a matsayin yan ba’ura ne su a harkar tattalin arziki, sai ga shi tsarin da Buharin ya dauka ya yi nasarar dakile faduwar Naira tare da farfado da tattalin arzikin daga koma bayan da ya shiga.

Suka da surutai irin na Sarki Sunusi ba su taba yin nasara ba, irin a lokacin da ya soki shirin gwamna Ganduje na gina layin dogo a cikin kwaryar birnin Kano, wanda zai lakume kimanin dala biliyan $1.2 wato kimanin naira Biliyan 400 kenan. A wajen taron shugabannin arewa a Kaduna, Sarki Sunusi ya soki lamarin da bada kwararan hujjoji wadanda cikin taimakon Allah wannan suka ta sa ita ce ummul-aba’isi ta sanyaya gwiwar Ganduje yadda ba shiri ya hakura da wannan shiri. Da tsarin ya tabbata, da a kalla kimanin Naira biliyan 108, wato kashi 25% na kwangilar, Ganduje zai kalmashe ya sa a babbar rigarsa kuma ba wanda zai iya cewa komai.

Hakika wannan jihadi da Sarki Sunusi ya yi wa kanawa, saura kiris ya sa tarihi ya maimaita kansa, domin zafin wannan asara da ya jaza wa Ganduje ta sa ya lashi takobin sauke shi daga karagar mulki, ba don wasu manya na Arewa sun tsoma ba ki ba, tare da sa Sarkin ya bada hakuri. A wannan gaba na ke son Sarki ya gane cewa muryarsa na da karfi kuma idan zai karkata ta inda ya kamata tare da yin aikin da ya kamata hakika zai iya cetar al’ummarsa ta fannoni da dama. Fiye da shekaru ashirin Sarki ba abinda bai soka ba, ya kamata ya maida hankalinsa wajen yin suka a ire-ire abubuwa da za su yi tasiri sosai kamar na kashe maganar titin dogo a Kano. Wajibi shugabanninmu su gane cewa kowacce al’umma fa ta na da wasu kebabbun mutane da ke mata tunani na gajere da dogon Zango, wani ginshiki da wannan al’umma tamu ta rasa. Suka nan da can ba zata amfani mutane ba, har sai an sami jajirtattun shugabanni da su ke yin shiri na sokar duk wani abu da zai cutar da al’umma sannan da kawo wadanda za su amfane ta.

Sarki ya lura da cewa ita suka don a ji ka kawai ba ta da amfani domin shi tarihi a kullum bai cika tuna zancen magabata ba kamar yadda ya ke tuna aikinsu. Don haka duk zancen da ba’a gina shi da aiki ba, zai zama aikin kawai ne. Duk yadda ka kai da iya suka ko zancen, bayan yan shekaru kalilan ba wanda zai tuna abubuwan da ka fada, domin wadanda ka fada domin ka burge su duk sun kauce tare da zancenka, amma idan ka yi aiki guda daya sai ya sa ka shiga jerin wadanda har abada ba za’a manta da su ba. Idan mu ka duba tarihin masarautar Kano, Sarkin da ya fi kowa shahara shine Muhammadu Rumfa, wanda a yau ba na jin akwai wanda zai iya kawo maka jawabinsa guda daya, wanda ya yi a rayuwarsa, amma saboda muhimman ayyuka da ya aiwatar a zamaninsa, har duniya ta nade ba za’a manta da shi a tarihin Kano ba. Saboda haka mai Martaba lokaci ya yi da za ka rage zance ka kama aiki, hanya tilo wadda za ta sa a tuna da kai har abada, domin Allah ma a kullum zancensa na yan tagwaye ne wato “Amanu” da “Amila”.

 

Comments

Popular posts from this blog

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

ALAMUN TSINUWA...