SHIN KUDIN RUWA NA BANKI, RIBA CE?

 


Shekaru da dama da su ka wuce lokacin da na gama jami’a, inda na karanci fannin addinin musulunci, kai nay a na fizga da dan ilimina da bai fi cikin cokali ba, sai mahaifiyata ta nemi da na kaiwa wani kawu na da ke aiki a wani babban banki takardu na domin samun aiki. Nan take na ce ni ba zan yi aiki a masana’anta wadda a ka gina a kan RIBA ba. A wancan lokaci kamar yanzu, matasa irina da yawa na da irin wannan fahimta. Sannu a hankali na ci gaba da cin karo  da wannan matsala ta riba a lokuta da dama. Na lura cewa a duk inda musulmi su ke a fadin duniya, ana samun irin wannan matsala kuma ya jawo koma bayan tattalin arzikin musulmi. Wannan dalili ne ya sa na shiga bincike game da yadda riba ta ke a hakika a musulunci. Abinda ya fara bani mamaki shine na gano cewa babu wata matsala wadda ta dade ta na ciwa musulmi tuwo a kwarya irin maganar riba domin ta faro ne tun zamanin sahabbai.

 

Annobar Kwarona ta jefa miliyoyin mutane a Arewacin Najeriya cikin wannan tsaka me wuya sakamakon samun hanyoyin karbar basuka musamman wanda Babban Bankin kasa ya fito da shi na tallafawa mutane da kananan sana’o’i. Amma waccan Magana ta riba na yin tarnaki ga mutane da dama. Akwai wani matashi an bashi bashin miliyan hudu amma mahaifiyarsa ta hana shi karba, sannan wani abokina ya sami damar karbar bashi na kimanin miliyan 238 amma malamai sun hana shi, saboda dalilai na riba.

Abu na farko da ya kamata mu fara fahimta game da riba shine abinda malamai ke kira da Asbabul Nuzul, wato dalilin saukar aya. Jamhurun malamai sun yarda da cewa an saukar da ayar Riba a shekara ta biyu bayan hijirar manzon Allah domin hana tsarin riba wadda ke wanzuwa a kasashen larabawa tun zamanin jahiliyya (Riba Al-Jahiliyya) inda wanda ya karbi bashi idan lokacin biya ya yi bai iya biya ba, sai a ninka kudin a sake ba shi lokaci, idan lokacin ya zo amma dai ba zai iya biya ba sai a sake ninka kudin. Ta haka za’a tsiyata shi ko kuma a karshe a maida shi bawa saboda ya kasa biyan bashin. Misali idan zaka biya bashin rakumi 100 lokacin biya ya zo ka kasa, sai a maida abinda zaka biya ya zama rakumi 200, daga nan ya zama 400 haka dai za’a yi ta ninkawa har ka kasa biya. Irin wannan tsari na rashin adalci musulunci ya haramta a ayar da ta fassara mecece riba. Malaman Usul al-fiqh sun raba ayoyin Kur’ani iri biyu, wato akwai Qati, ayoyi bayyanannu wadanda sakonsu a bude ya ke kuma kai tsaye, sannan akwai ayoyi da su ka kira zanni, wadanda ke bukatar karin bayani. A bayyane ya ke cewa wannan aya

Q3:!30 “Ya ku wadanda su ka yi imani kada ku ci riba ninkin ninki, ribanye, kuma ku bi Allah da takawa”

Karara kuma a bayyane wannan aya ta fassara mana riba a wajen Allah, wato itace irin riba wadda ake kira  riba al-jahiliyya wadda ake ninninka kudin ruwa kuma a ribanya. Irin wannan riba ita ce Allah ya haramta kuma malaman musulunci tun daga zamanin sahabbai kawo yanzu sun gamsu da cewa wannan ce riba. A cikinsu akwai mashahurin sahabin manzon Allah wato Ibn Abbas wanda ya yarda da cewa riba al-jahiliyya, riba wadda ta ninninka ita ce riba. Haka nan manyan sahabbai irinsu Usama Bn Zaid, Abdullah Bn Mas’ud, Urwah Ibn Zubair da Zaid Ibn Arqam haka su ka yarda. A cikin Tabi’ai, Imam Ibn Hanbal, shugaban mazhabar Hanbaliya shi ma haka ya yarda kamar yadda Ibn Qayyim ya fada cewa Hanbali ya ce “Biya ko kari (ninkawa) ita ce kadai riba wadda haramcinta ba shi da tantama”. Malaman tafsiri irinsu Tabari, shi ma a tafsirinsa ya ce “Kada ku ci riba bayan kun musulunta kamar yadda ku ke cin riba a lokacin jahiliyya” Wasu masu tafsirin irinsu Jalaluddeen Suyudi, Ibn Arabi, Ibn Kathir da Al-Baydawi duk sun yadda da cewa riba ita ce irin ta jahiliyya wadda ake ninninkawa.

Rudani kan mas’alar riba ya faro daga inda aka maida hankali akan nau’o’in riba maimakon ma’anar mecece ita. An kasa riba gida biyu wato Riba al Nasee’ah (ribar jinkiri wadda ake bada bashi a jira lokacin biya) da kuma riba Al-Fadil wadda ta bani gishiri in baka manda wadda ake samun kari. Musulunci ya zo domin ya kawar da riba wadda ake ninninka kudin ruwa amma banda kudin ruwa wanda bai kai kashi dari ba. Ka da mu manta a karni na bakwai lokacin zuwan musulunci, basuka yawanci a tsakanin mutum da mutum ne ba bashi ba ne na saka jari (abinda ya dame mu a tattalin arziki na zamani). A wancan lokaci harkokin kasuwanci sun dogara yawanci akan cinikayya irin ta bani-gishiri-in-baka-manda. A cewar Mufti Muhammad Shafi “Abinda ke wanzuwa a kasashen larabawa a wancan lokaci (jahiliyya) ana bada bashi tare da kudin ruwa kuma idan lokacin biya ya yi sai wanda ya karbi bashin ya biya kudin da karin kudin ruwa da a ka saka masa, yin haka magana ta kare amma idan ya kasa biya sai a kara masa kudin ruwan”. Wannan Kari na kudin ruwa da ake ninkawa idan ka kasa biyan bashi, shine abinda Allah ya kira da RIBA kuma ya haramta. Ya zo cikin hadisai cewa manzon Allah da kansa ya yi cinikayya ta bashi kuma ya bada kudin ruwa kamar yadda ya zo cikin Sahih al-Bukhari, Vol. 3, No. 579, Jabir bin Abdullah y ace : “Na je wajen manzon Allah lokacin ya na masallaci (Mis’ar ya na zaton bayan sallar azahar ne) Bayan manzon Allah ya umarce ni da yin sallah raka’a biyu sai ya biya ni bashin da na ke binsa kuma ya kara min wani abu a kai” Sannan a wani hadisin ya biya rakumi biyu a maimakon daya (Muwatta kitabul Buyu hadith 1346), da kuma lokacin da  biya rakumi da wani wanda ya fi shi (Sahih Muslim Book 10, Number 3899:). (Tirmidhi) ya ruwaito cewa  Jabir ya ce:  Manzon Allah () ya ce: "Bada dabbobi biyu a maimakon daya ba daidai ba ne idan bashi ne, amma babu laifi idan hannu da hannu ne” Haka nan a littafi na 10, Hadith Na 3902 cikin Sahih Muslim: 'A'isha ta ruwaito cewa manzon Allah ya sayi tsabar abinci bashi daga wajen wani Bayahude inda ya bada garkuwarsa a matsayin jingina”. Wannan hadisi na Aisha ya tabbatar da yadda ake karbar abin jingina (collateral) a wajen bada bashi kamar yadda ake yi a tsarin banki irin na zamani. Sannan kuma ya dada tabbatar da cewa Annabi ya karbi bashi mai saukin kudin ruwa domin babu yadda za’a yi Bayahude ko da dan’uwansa ba zai ba shi bashi ba tare da dora kudin ruwa ba. A tsarin yahudanci babu bashi wanda ba shi da kudin ruwa kamar yadda Allah ya sanar da mu cikin surar Al-Nisa

Q4:60-61 “Saboda zalunci daga wadanda su ka tuba (Yahudu) muka haramta musu abubuwa masu dadi wadanda aka halatta su a gare su, kuma saboda taushewarsu daga hanyar Allah da yawa. DA KARBARSU GA RIBA, alhali kuwa an hana su daga gareta”

 

Don haka a bayyane ya ke cewa Annabi ya halatta bada ruwa mai sauki domin ya bayar bisa hujjojin wadannan hadisai na sama. Matukar ruwa bai wuce kaso 100% ba kuma matukar mutane sun aminta da kason ruwan za su iya karba ko bayarwa amma ninninka ruwa yadda kullum bashi zai ta hauhauwa shine zaluncin da musulunci ya haramta. Idan kudin ruwa ko wane iri haram ne babu yadda annabi zai bada shi ba, domin ba zai yiwu ya halatta abinda Allah ya haramta ba. Irin wannan tsari ne ya sa a yanzu bankunan musulunci ke tsarin Murabaha, wato tsarin da misali yanzu sai Ja’iz Bank su siya min gida na miliyan goma, wanda zan biya a hankali amma a karshe zan biya miliyan sha daya sakamakon ba  su ruwa na kashi goma. Idan za’a yi wannan tsari ga kadara don me ba zai yiwu a kudade ba?. Kudin ruwa matukar bai ninka ba halal ne domin ninninkawa ne Allah ya haramta.

 

Duk da bayanin Kurani karara na mecece riba, da kuma yadda annabi ya yi huldar bashi bai hana rudani cikin yadda ake kallon riba ba, saboda malamai na kawar da hankalinsu daga mahimman abubuwa biyu; Na farko abinda ake kira illat, wato illar riba a harkokin ciniki, saboda Allah baya son zalunci ko kadan, abu na biyu shine ta yaya za’a san cewa tsarin ya zama na zalunci? Shine abinda ayar ta kawo na fassara wane mizani ne ya kai riba? Allah ya fadi mizanin da cewa ninki baninki it ace riba. Maimakon fahimtar wannan sai aka maida hankali kan ire-iren riba. Tun zamanin sahabbai an sami rashin jituwar fahimta misali a hadisin Sahih Muslim Vol III hadith 3852 Inda 'Ubadah b. al-Samit—ya ce Annabi ya haramta riba ta kari (riba al-fadl), yayin da Mu’awiyya ya musa masa da cewa ba su taba jin manzon Allah ya haramta ba, "Duk da cewa mun rayu da manzon Allah”  sai 'Ubadah b. al-Samit ya amsa da cewa “Dole mu sanar da abinda mu ka ji daga manzon Allah ko da kuwa ba zai yi wa Mu’awiyya dadi ba”. Sannan akwai hadisi daga Usamah ibn Zayd: ya ce manzon Allah ya ce: “Babu Riba sai a jinkirtawa (al nasee’ah.” A wani hadisin kuma Sahih Bukhari, Kitab al-Buyu Vol. 3, Na. 386. “Babu riba a cinikin hannu da hannu.”

 

Bayan Musulunci ya dada fadada da mamaye kasashe, shekaru dari biyu bayan wafatin manzon Allah, Imam Shafi’I, shugaban mazhabar Shafi’iyya a yayin da ya yi nazarin abubuwa guda shida  wadanda riba ke shiga ciki (wato Zinare, Azurfa, Dabino, Gishiri, Alkama da Barley), ya ce kudaden musaya da ake kira fils, wato kudade na karfe riba ba ta shiga cikinsu. Wannan matsaya tasa irinta ce ta sa Abubakar Gumi shi ma ya ke da ra’ayin cewa kudaden takarda riba ba ta shiga ciki kuma za’a iya karbar kudin ruwa. Mazhabobin Hanbali, Hannafi da Shi’a, su ma sun fadada daga wadancan abubuwa shida da riba za ta iya shiga ciki zuwa duk wani abu irinsu wanda ake aunawa (kamar gwal da azurfa) ko kuma wanda ya ke da adadi irin na alkama, gishiri da sauransu.

 

A zamanin daular kalifofin musulunci na Abbasiyawa, kamar yadda Ibn Al-Miskawayh ya rubuta cikin littafi Taedrib Al-Umam, ya ce kalifa Muqtadir ya ci bashin Dirhami dubu dari biyu wanda aka saka masa kudin ruwa na kashi 7% a tsakanin shekarun 912-913. A cikin wannan karni na biyar da kimanin shekaru 60 bayan kalifan musulunci ya bada kudin ruwa a bashin da ya karba, sai Baihaqi ya ruwaito cikin sunan dinsa wani hadisi wanda malamai da dama sun hakikance cewa hadisi ne mai rauni (Mauquf) wato hadisi wanda isnadinsa bai kai ga manzon Allah ba ya yanke. Ga abinda Baihaqi ya ruwaito “Sahabin annabi Fudalah Bn Ubayd ya ce duk wani bashi wanda mai bada bashin ya sami kari akai na daya daga cikin nau’in riba”. Wannan hadisi ba shi da inganci musamman idan aka yi la’akari da sahihan hadisai cikin Bukhari, Muslim da sauransu wadanda sun zo kafin wannan sunan ta Baihaqi kuma da hadisai da su ka nu na annabi ya bada ruwa a bashi kuma duk cikinsu ba wanda ya ruwaito wannan hadisi. Amma sai gashi sannu a hankali, wannan hadisi ya bulla cikin littafin Lisanil Arab bayan shekaru 150 da ruwaito shi a cikin sunan ta Baihaqi. A cikin karni na goma bayan hijira, a littafinsa na Jami’al Saghir shi ma Imam Suyudi ya ruwaito hadisin inda abin mamaki sai kuma isnadinsa ya cika cif inda aka danganta shi da sayyidina Ali. Duk da wannan kwaskawrima ta isnadi, Suyudi ya tabbatar da cewa dai hadisin mai rauni ne. Duk da haka wannan hadisi ya ci gaba da samun tagomashi inda ya sake bulla cikin littafin Kanz Al-Ummal da Al-Siraj Al-Munir inda ajinsa ya daukaka daga hadisi mai rauni (Mauquf) zuwa ingantacce (Hasan).

A karni na 16 Sarkin daular Usmaniya Ahmet ya kayyade kudin ruwa a fadin daular zuwa kaso 15% wanda aka yi ta amfani da shi har zuwa bayan shekara dari biyu, wato a karni na 18 inda a ranar 18 ga watan Fabrairu 1838 lokacin sarki Mahmud II, ya kirkiri ma’aikatar cinikayya kuma bayan shekara biyu da samuwar wannan ma’aikata sai magajinsa Sarki Abdulmajid ya umarci samar da kudade na takarda wadanda su ka canji zinare da azurfa a matsayin kudaden musaya kuma aka kayyade kudin ruwa a kan kaso 8%. Har zuwa karni na 20, Alkalin Alkalai na daular Usmaniyya (Ottomon Empire) Mufti Ebussuud Efendi ya ci gaba da halatta kudin ruwa kamar yadda malamai da dama na zamani su ka yarda da halascin sa, wato irinsu Muhammad Abduh, Rashid Rida, Mahmud Shaltut, Syed Ahmad Khan, Fazl al-Rahman da Muhammad Sayyid Tantawy. Dukkansu shahararrun malamai ne a duniya kuma sun yarda cewa kudin ruwa idan bai zama wanda ake ninkin baninki ba ne to ya halatta kuma ba riba ba ne.

Wannan lamari na riba an farfado da shi ne karkashin gwamnatin yan salafiya na Saudi Arabia a shekarar 1976 inda su ka kira taro na duniya kuma malamai masu irin tunaninsu su ka yarda su haramta duk wani kudin ruwa a matsayin riba. Ta haka aka yada wannan fatawa a kasashen duniya kuma akasarin mutane su ka karbi fatawar da ka. Wannan lamari na daya daga cikin dalilan da ya sa kasashen musulmi, duk da irin makudan kudade da albarkatun kasa da su ka mallaka, kasashen ke cikin talauci da koma baya a fannonin kuma su ke saka kudadensu a bankunan turawa wanda ke inganta tattalin arzikin turawa. A nan Nijeriya muna da bankuna 24 amma babu guda daya wanda ke hannun musulmi. Abin kunya, bankin arewa wanda Sardauna karkashin jagorancin Abubakar Gumi wanda ya gane mahimmancin banki a kasa kuma ya fahimci cewa addini bai hana mu yin hurda da banki mai ruwa ba, a yanzu shi kansa ya koma hannun wadanda ba musulmi ba.

A karshe idan duk wadannan bayanai da hujjoji na Qur’ani, Hadisi da daulolin musulunci a baya ba su gamsar da kai cewa kudin ruwa sai ya nininka sannan ya zama riba ba, to mu na iya daukar maslahar da Abubakar Gumi ya bayar ga al’ummar musulmi na cewa za mu iya mu’amala da banki a matsayin larura domin duk da Allah da kansa ya haramta cin mushe amma sai ya saukaka cewa

Q2:173 “Kawai abinda ya haramta a kanku mushe da jinni da naman alade da abinda aka kururuta game das hi ga wanin Allah. To wanda aka matsa masa, ba don tawaye ba kuma banda mai zalunci to babu laifi a kansa. Lalle ne Allah mai gafara ne mai jin kai”

Don haka ya rage mu tashi tsaye mu farfado da tattalin arzikinmu a matsayin musulmi a fadin duniya ko kuma mu ci gaba da zama bayin turawa cikin talauci.

 

Comments

Popular posts from this blog

ALAMUN TSINUWA...

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

Dabara Ta Rage Wa Mai Shiga Rijiya…