TSINUWA TA TABBATA A KAN MU…?

An yi zabe an gama, duk da dai cewa rigingimu sun biyo bayan zaben, kuma an tabbatar da cewa shugaba Goodluck shine ya cinye zaben da gagarumin rinjaye. Kafin a yi wannan zaben marubuta iri-iri sun yi sharhi kuma ina daya daga cikinsu, cikin wani sharhi da na yi, na zargi Muhammadu Buhari da yin taurin kai wanda zai iya sa kasar ta kasa samun canji, kuma hakan ya faru a yau. Babu yadda za’a yi ka ci mulkin Nigeria ba tare da kana da kyakkyawan kawance da yarbawa da inyamurai ba, kuma jam’iyya ke cin zabe na kasa ba mutum ba. Muna gani Buhari ya ci jihohi sha biyu amma da kyar ya sami kason 25 a cikin 16. A yanzu muna gani Kano, Bauchi, Katsina, Kaduna da su ka bashi kuri’a sama da Miliyan dai dai, sai ga shi Duk wadannan jihohi sun zabi gwamnonin PDP. Domin kamar yadda n ace, hakika ba mutum guda ke cin zabe ba sai jam’iyya. Mutane da dama sun harzuka da irin bayanai na tare da maida min martini ta hanyoyi daban-daban, amma na san yanzu zasu iya fahimtar dalilan da muka zargi Buhari kafin zabe. Abin lura shine, mun shekara 12 cikin ukubar PDP kuma bata da niyyar kawo canji amma duk da haka sai gashi a yau an sake zabar su kan mulki.

Kowa ya kwana da sanin cewa Allah ya bamu damar kawo canji a kasar nan cikin salun-alun amma saboda son kai (na wasu yan arewa) da kuma kabilanci (na yan kudu), PDP ta sake darewa kan karagar mulki. Taurin kai irin na Buhari, munafinci irin na yarbawa da cin amana irin na ‘yan arewa ya sake kakaba mana PDP nan da wasu shekaru 8 masu zuwa(kwarai kuwa domin babu abinda zai hana Jonathan Tazarce). Don haka duk wani bala’i na kunci da ci baya da zai biyo baya kada wani ya zargi kowa, mu zargi kanmu. Kuma ina tabbatar muku cewa nan ba da dadewa ba mutanen kasar, musamman yan uwan mu na kudu, zaka fara jinsu suna kai ruwa rana da wannan gwamnati. Kada ku yi mamakin wannan Magana tawa domin ina da dalilai. Shugaba Jonathan yana da zabi biyu da ba makawa sai ya yi daya daga cikinsu; Na farko shine zabi mafi ingancin da ya kamata ya yi, amma ina da shakkun zai yi shi, wato ya karkade rigarsa ya dukufa da aiki tukuru babu nuna banbanci na ganin ya kawo gyara mai amfani cikin wannan kasa ta hanyar tunkarar cin hanci da rashawa, yakar talauci a kasar, bunkasa tattalin arziki da gyara Niger Delta. Idan har ya yi wadannan abubuwa zai sami kalubale daga mutanen kudu, musamman mai gidansa Obasanjo, domin za su so su ga cewa yayi watsi da arewa ya maida hankalinsa ga kudanci don haka za’a gansu a rana kace-kace. Zabi na biyu shine, ya ci gaba da mulki kamar yadda yayi na rikon kwarya, wato ya ci gaba da ajandar PDP na mulkin tamore da sace kudaden jama’a ba tare da nuna wani abin azo a gani ba. Yin haka shima zai saka mutanen Kudu, wadanda a yanzu kabilanci ya rufe musu ido wajen zabensa su gane kurensu na daure wa mulkin danniya gindi, wanda hakan zai saka su zama masu adawa da shi mai zafi. Idan kuma ya ci gaba da watsi da manufofin Yar Adua da ya gada a kan Niger Delta, su ma zasu dawo da hare-harensu da yakar gwamnati.

Kabilanci da nuna banbancin addini shine mafi munin halin da muka sami kanmu a yau a wannan kasa, kuma shugabanni a kullum babu abinda su ke yi sai kara rura wannan wuta. Kuma wallahi matukar bamu tashi tsaye wajen yakar wannan matsala ba, maganar ci gaba ko kasancewar kasar a dunkule, ba zai taba samuwa ba. Duk wanda ya fahimci yadda kasar nan take kuma ya san tarihinta, ya san cewa abu guda da ya kawo kwanciyar hankali har aka sami mulkin dumokurodiya ya dore daga daga 1999-2011 shine kasancewar dattakun yan arewa na fito da Obasanjo a 1999 da mara masa baya ya yi shekaru 8 da zummar cewa za’a dawo da mulki arewa, wanda aka yi. Amma da zarar mutuwar Yar Adua da kuma zuga Jonathan ya yi watsi da wannan tsari na karba-karba (wato bin son rai na mutum guda da ‘yan barandansa) hakan ya dawo da wutar kabilanci (tsakanin mutane sama da miliyan 150) fiye da kowane lokaci a tarihin kasar tun bayan yakin basasa.  A ka’ida bai kamata a ce ana dimokuradiya da wani tsari na karba-karba ba domin karan tsaye ne ga dimokuradiyar. Amma kasancewar mu yan Nigeria mun saka kabilanci da addini cikin tsarin rayuwarmu kuma muka bashi tasiri fiye da komai, wajibi ne mu yi wannan mummunan hali tarnaki. Tarnakin kuwa shine kadai idan za’a yi karba-karba yadda kowa zai iya hakuri lokacinsa ya kewayo kamar yadda muka gani daga 1999-2007.  Kamar yadda wani jigon PDP ya fada a baya cewa sai PDP ta yi shekaru 60 tana mulki har mutane na masa dariya, to mu fara kuka domin ta kamo hanya. Abu guda da zai hana ta cimma wannan buri shine har sai dai idan soja zai karbe mulki ya rusa siyasun ya kawo sababbi. Kasarmu na da tarin arziki da kowa zai wadata amma hakan ya gagara saboda muna kallo yan siyasa sun kasa kawo ci gaba domin suna gina kansu ne kawai. Kamar

Duk wanda ya kwana ya tashi a wannan kasa, ya san PDP ta gaza kuma ya san baza su iya kawo canjin da ake bukata ba, amma saboda an hura wutar kabilanci sai gashi yan uwanmu na kudu sun yi watsi da nagarta sun bi kabilanci don sake dora PDP  a mulki. Shugaban sashen Hausa na Jamus, wanda bajamushe ne ya yi sharhi cikin wannan satin inda ya ke dora alhakin rigingimun da suka biyo bayan zaben Shugaban kasa a kan watsin da Jonathan ya yi da tsarin karba-karba. Kuma duk mai hankali da adalci ya san wannan ita ce babbar matsala amma saboda kabilanci, yan uwanmu na kudu sun kasa kallon abin a haka. A yanzu sun sami biyan bukata amma kowa ya sani cewa wannan matsala an tura ta gaba ne kawai domin sai ta dawo ta bibiye mu ko a dade ko a jima. Kuma idan bamu kau da ita ba illarta mummuna ce a gaba domin tana iya raba kasar. Idan mu ka yi duba na tsanaki ya kamata mu tambayi kanmu dalilin da ya sa a 2003 da 2007, duk da cewa a tarihin kasar nan ba’a taba samun magudi na siyasa kamar wadannan zabubbuka ba, amma babu inda aka yi kone-kone ballantana kashe rayuka. Amma a 2011, mun ga zabe mafi nagarta daga wadancan kuma duk da cewa akwai magudi amma bai kai na baya ba, kuma daga dukkan alamu kowa ya san cewa Jonathan ya ci zabe, amma sai gashi an barke da tarzoma mafi girma tun yakin basasa (domin akalla jihohi goma ne suka kama wuta). Dalili guda shine na watsi da karba karba, domin a 2003 kowa ya yarda cewa Obasanjo ne ya cancanci ya nemi takara, haka nan a 2007 kowa ya gamsu cewa zagayen arewa ne don haka Yar ‘Adua ya cancanta. Amma a 2011 kowa ya san cewa ba hakkin Goodluck ba ne, fashin takarar yayi da karfin gwamnati. Kabilanci da banbancin addini ya yi mana katutu yadda zaka ga mutane shahararru da ko’ina a duniya ana ganin kimarsu da yardar cewa masu basira ne, amma sai kaga wutar kabilanci na nan tare da su misali akwai wani shahararren Malamin Jami’a a arewa da kuma wani shahararren Reverend. Idan mutane kamar wadannan sun kasa yakar kabilanci a cikin rayuwarsu ya kake tsammani talakawa (wanda akasari jahilai ne matalauta da ke kashe junansu) zasu kauce wa kabilanci?  Wallahi matukar ba’a yarda da dabbaka tsarin karba-karba ba, to akwai barazana mummuna, sai dai fa idan dama ajandar su Obasanjo ita ce ta tabbatar da cewa kasar ta tsage kamar yadda a jawabin Jonathan ya ke nuna cewa zabubbukan shekarun 1950’s da hargitsin da ya biyo baya shine ummul aba’isin yakin basasa. Amurka da ma ta ce a nata hasashen nan da yan shekaru kasar zata wargaje. Muna raina wannan hasashe amma kuma mun kama hanya.

Tarzomar da ta barke a arewa kararrawa ce ga wannan kasa gaba daya, koda yake yan kudu suna ganin cewa kamar kabilanci ne kawai aka nuna. Tabbas akwai kabilanci a ciki, kuma da abin takaici na far wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Ni kaina a Kano sai da na baiwa makwabta na mafaka, kuma ni da wasu makwabta muka tashi tsaye wajen ganin ba’a kona gidajensu ba. Amma abinda ya faru ya zarce haka domin a karo na farko a arewacin Nigeria ko ma a kasar gaba daya an wayi gari matasa masu tarzoma sun far ma  manyan mutane. A Kano an kai hari a kan gidaje guda biyu mafi kima da mahimmanci; wato gidan Sarkin Kano Ado Bayero da kuma Galadiman Kano Tijjani Hashim. Wadannan gidaje a mafarki babu wanda zai iya cewa za’a iya kai musu hari amma Gidan Galadima an kona shi kuma an kona motoci a gidan sarki. Abin ba anan kawai ya tsaya ba domin an kona gidan tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na’abba da Gidan Tsohon dan takarar shugaban kasa, Bashir Tofa, da gidan Sani Rogo har da kai hari gidan Sheik Isyaka Rabiu da sauransu. A wasu garuruwan a fadin yankin hakan ne ta faru domin an hari fada mafi daraja a yankin, wato fadar mai alfarma Sarkin musulmi, fadar da kamar za’a bauta mata (domin har gobe ana ziyararta) amma sai aka wayi gari sai da sojoji suka kewaye ta don kare ta daga harin matasan. Sarkin Zazzau ma bai tsira don sai da aka kone gidansa na Kaduna.

Wannan al’amari babba ne kuma sako ne da martini mai karfi ga shugabannin arewa gaba daya har ma da shi sabon shugaban kasa. Matukar mahukunta su ka ci gaba da watsi da muradun talakawa to, su sani fa cewa matasa sun fara kai musu hari a karon farko a wannan yanki kuma zasu iya mamaitawa. A rubutun da na yi kafin zabe na yi wata makala da na kira “ALAMUN TSINUWA” inda na nuna dukkan alamomi da ke nuna cewa kasar nan tana cikin tsinuwa. A yau kasancewar Allah ya bamu dama cikin ruwan sanyi yadda zamu kau da PDP da zaluncinsu sai aka wayi gari mun ki yarda domin ci gaba da hura wata wuta (ta kabilanci da bangarancin addini) wadda zata cinye mu gaba daya. Yanzu na gamsu da cewa hakika, tsinuwa ta tabbata a kan mu! Don haka Allah ba zai taimake mu ba har sai ranar da muka yarda mu bi sahun kasashe na gari wadanda su ka yaki banbance-banbance suka gina kasashen su a kan adalci da nagarta. Idan mun yi haka, watakila Allah ya dube mu ya kawar mana da annobar da muka kakaba wa kanmu, wato PDP.

 

 

Comments

Popular posts from this blog

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

ALAMUN TSINUWA...

SARKIN KANO DA GWANINTAR IYA SUKA