TURAWAN MULKI DA MASARAUTA SU KA KASSARA AREWA


Arewacin Najeriya, duk da kasancewar Allah ya albarkace mu da dimbin arzikin kasa, ma’adinai da yawan al’umma, bai hana mu zama yanki mafi talauci, jahilci da rashin tsaro a duniya ba, sakamakon gadon da muka samu ta hanyar mulkin mallaka da bautarwar shugabanni. Cikin shekaru uku, tsakanin 1900-1903,  Lord Luggard tare da sojojinsa na yammacin Afirka sun murkushe masarautun arewa daya bayan daya har zuwa lokacin da Captain Moorland ya ci Kano a shekarar 1903 kuma turawa su ka kafa mulkin mallaka a fadin Najeriya.

Ana samun wannan nasara sai Lugard ya sanarwa da iyayen gidansa fitar da tsarin mulkin mallaka irin wanda ya gani a India na mallakar kasa ta hanyar sarakunanta, maimakon mulkar ta kai tsaye. Don haka a arewa sun yanke shawarar ilimintar da yayan sarakuna da na kusa da su domin su ne za su ci gaba da daukar ragamar mulki sakamakon tsoron ilimintar da dukkan talakawa domin kada su sami kalubale irin wanda su ka samu a kasashen Egypt da India inda yan kasa su ka waye kuma su ka fara yakar tsarin mulkin mallaka, abinda ya fara faruwa a wannan lokaci a sashen kudancin Najeriya musamman ma a Lagos. An kafa makarantar farko a yankin Lagos shekaru kusan hamsin kafin wannan lokaci a shekarar 1859. Wannan makaranta wadda wani Dan Najeriya Kyaftin Davies ya baiwa TB Macaulay tallafin fam hamsin domin siyen littafai da kayan aiki, ta sami dalibai na farko guda ashirin da biyar wadanda iyayen takwas daga cikin daliban yan kasuwa ne, sannan guda sha hudu yayan masu kananan sana’o’i ne da kuma dan malamin coci guda daya, da dan kafinta da kuma dan mai karatun Bible. Wato ilahirin daliban duk yayan talakawa ne ba yayan sarakai ba.

Amma sai tsarin ya canza a arewacin Najeriya inda turawa su ka nuna karara cewa yayan sarakai su ke so su sami ilimi domin su ake sa ran za su karbi mulki a gaba. Cikin wata takarda da Lugard ya rubutawa sakataren kasashen waje na Birtaniya a shekarar 1906 ya ce “Idan shugabanni da za su zo nan gaba na Najeriya daga yan kasa su ka kasance sun sami ilimin turanci…Fulani za su zama, sakamakon kwarewarsu wajen iya mulki, zama mahimman abokan hurdar mulki ga kasar Birtaniya” don haka makarantar firamare ta farko a arewacin arewa wadda aka bude a shekarar 1905 a garin Sakkwato, gaba dayan dalibanta yayan sarauta ne ko wadanda su ka jibance su. Sai dai wannan makaranta ba ta sami karbuwa ga sauran sarakunan arewa ba saboda nisan Sakkwato da garuruwansu. A shekarar 1907, duk dalibai 36 da ke cikin wannan makaranta yayan sarakuna ne. Shekaru uku bayan nan, wato a shekarar 1910 sai Dan Hausa (Hans Vischer) ya samar da irin waccan makaranta ta Sakkwato a birnin Kano wadda ita ma aka debi yayan sarakuna zalla a cikinta. Har zuwa shekarar 1930 kimanin kashi sittin na dalibai a yankin Sakkwato duk yayan sarauta ne ko yayan ma’aikatan NA. Kwalejin Katsina,  a shekarun 1930 ta kasance makarantar da dalibanta su ma fiye da kashi tamanin daga cikinsu yayan sarakai ne da  ma’aikatan gwamnati. Sarakunan Arewa sun fahimci cewa ilimin boko hanya ce ta horar da yayayensu domin shirya su, su karbe madafun iko a cikin gwamnati ba domin a maishe su kiristoci ba, wato abinda aka rika siyarwa talakawa wanda ya sa su ka kyamaci harkar boko har ake wakar “Yan boko, bokoko a wuta”, wato tsangwamar da ba’a daina ta ba har zuwa shekarun 1980.

Manhajar karatu a wancan lokaci ita kanta an tsara ta yadda za ta dakile ilimin yan arewa domin an hana koyar da turanci a firamare, domin ba’a fara koyawa dalibai turanci sai sun tsallake karamar sakadandare sun shiga babba (a lokacin da duk littafan ilimi da turanci ake buga su), amma kuma makarantun Mishan suna koyarwa da turanci kuma har tallafi ake basu don yin hakan. Sannan babu wata jarrabawa daga waje (wato irinsu Cambridge da Oxford) wadanda makarantun kudu su ke dauka kafin kammala kowane mataki na ilimi. Shekaru biyar bayan hade kudanci da arewacin Najeriya a matsayin kasa daya, da kansa Lugard ya amsa cewa “Yankin Arewa duk da yawan mutane kimanin miliyan tara, ya kasa samar da akawu ko ma’aikaci guda cikin yayanta masu basira”

A lokacin yakin duniya na farko, cikin shekarar 1917, Sarkin Musulmi Muhammadu Dan Ahmadu, ya nemi a sahale masa fam sittin da tara domin ya ginawa dalibai dakin kwana a makarantar firamare ta Sakkwato kasancewar wasu daliban da dama na tafiya mai nisa daga garuruwansu domin halarta, amma sai Gwamna na lokacin, wato H.M. Goldsmith, ya yi kememe ya hana shi wannan izini, duk da cewa yankin Sakkwato a duk shekara yana tara kudaden da su ka kai fam dubu arba’in, wanda a cikin su a ke ware fam dubu takwas domin taimakawa kasar Birtaniya da kudaden a asusunta na aiwatar da yakin duniya na farko.

A shekarar 1919 wani jami’in ilimin boko a kasar Zaria ya gaya wa babban darektan ilimi na yankin cewa “Ba wanda ya fahimci mahimmancin ilimin boko a makarantar Firamare ta Zaria kamar Sarkin Zaria (Aliyu) wanda ya saka iyaye talatin da hudu su ka kai yayansu makaranta a wannan shekara…(Sarkin) na burin ganin cewa yayansa da na makusantansa sun ci gajiyar ilimin boko amma ba ya son yayan wasu wadanda ba nasa ko na na mutanensa ba, da wadanda ya ke adawa da su, su sami irin wannan dama da mutanensa su ka samu”

Zuwa shekarar 1920, yan uwan Sarkin Gwandu Usman (1918-1938) da yayan kannensa biyu duk sun shiga makarantar elementary ta Kebbi. Sannan a shekarar 1935, shida a cikin sarakuna da ke kan gadon mulki da fiye da hakimai talatin (yawancin yayan sarakuna) sun sami ilimin boko. Cikin Sarakuna masu daraja ta daya, Sultan Abubakar III, Ahmed Lamidon Adamawa (1843-1953), Sama’ila na Argungu (1942-53), Yahaya Sarkin Gwandu (1938-57) Usman Nagoggo Sarkin Katsina (1944-1981) da Sarki Jafaru na Zazzau (1937-59) duk sun yi ilimin boko. Amma Sarki Umar Al-Kanemi na Barno, Yakubun Bauchi, Abdullahi Bayero Sarkin Kano, Abdulkadir na Ilorin da Muhammadu Ndayako na Bidda ba su sami ilimin boko  ba saboda kasancewa shekarunsu sun ja sosai a lokacin da a ka kafa irin wadannan makarantu a yankunansu. Sir Theodore Adams, kwamishinan yankin arewa a shekarun (1937-1943) ya gargadi sarakunan arewa cewa idan ba a baiwa yayansu ilimi mafi inganci fiye da wadanda za’a baiwa talakawa, wata rana za’a wayi gari yayan talaka sun karbe mulki daga hannunsu ta hanyar samun ilimi mai zurfi.

Shi kansa yaduwar ilimin boko ta hannun makarantun mishan ya sami cikas daga wajen turawa a Arewa saboda dakile su a yayin da su ka nemi izinin kafa irin wadannan makarantu. Sannan kuma su kansu sarakai su na jin tsoron ayyukan yan mishan a yankunansu. Wannan tsoro ya fi jibantar siyasa fiye da addini musamman idan mu ka yi la’akari hujjar cewa a shekarar 1903 Dr. W. R. Miller na kungiyar yan mishan ya fadawa Lugard cewa yawancin mutanen arewa jikinsu ya yi sanyi ganin yadda Birtaniya ta bar mulki a hannun “Azzaluman sarakunan Fulani”.

 

Sarkin Gwandu Usman, ya sanar da J. H. Harrow, wato Rasdan na Sakkwato cewar a shirye yak e ya bar yan mishan su kafa makarantunsu a yankin sa saboda malaman musulmi basu damu da tubar da maguzawa ba sai an biya su kudade, don haka gara yan mishan su mayar das u kiristoci. Sarkin Zazzau Aliyu ya bada hadin kai a yankin kasarsa lokacin da ake kokarin kafa makarantar mishan ta Dr. Miller a Zaria (1906-1909), Sarki Aliyu ya bada matukar goyon baya ga yunkurin, amma kuma daga baya shi Dr. Miller ne ya shigar da korafi gaban Gwamna wanda dalilinsa aka tube Sarki Aliyu a shekarar 1920.

Da kyar da jibin goshi kafin turawan mulkin mallaka su yadda da bukatar wasu sarakunan arewa wajen samar da makarantun boko na mata a yankin. A shekarar 1933 ne su ka sahale da kafa makarantun mata guda biyu, daya a Kano daya a Katsina duk da goton da Sarkin Gwandu ya yi ta yi kan a yi masa guda daya a yankinsa, amma sai Gwamna G. J. Lethem ya katse masa hanzari da cewa ba su da isassun kudi da za su iya dauko malamai turawa biyu mata daga Ingila domin kula da makarantar.

A bayyane ya ke idan mu ka yi la’akari da wadannan hujjoji na sama mu gane cewa da gangan aka tsara yadda arewa za ta kasance koma baya cikin harkokin ilimin boko ta hanyar daurewa yayan sarakuna da mukarrabansu su yi ilimi amma banda akasarin talakawa. Wannan tsari shi ya haifar da yanayin da arewa ke ciki a yanzu. Biyayya ga yan kalilan da ke da madafan iko (masarauta da ma’aikatan gwamnati) wadda ta samo asali daga mulkin turawa ita ce ta ci gaba da tasiri har bayan yancin kai lokacin da su Sardauna su ka karbi mulki. Maimakon juya akalar wancan tsari sai su ka assasa shi wanda kasancewar babu turawa masu saka ido a harkokin gwamnati, sai kuma wasu sharruka biyu su ka biyo ba, wato cin hanci da bangaranci. Bangarancin an ci gaba da gina shi kan alfarma wadda ta dakile kowacce irin cancanta. Goyon bayan Birtaniya ga mutanen arewa wajen mulkin kasar, ya sa yan arewa sun mamaye harkokin soji da na siyasa. Alfarma da cin hanci wadanda su ka bulla lokacin su Sardauna su ne har a yau su ka dakile kasar gabadaya musamman arewaci.

Arewa na da duk wani abu da ake nema domin samun ci gaba amma sai manyanmu su ka saitata yadda za ta rika biyan bukatunsu kawai ba na jama’a ba. Su kuma al’ummar arewa sakamakon talauci da jahilci sun karbi muguwar hanyar banbancin kabila da addini yadda ta wannan mahanga kadai ka ke iya ganin fushinsu a zahiri. Hatta wadanda su ka je makaranta za ka ga cewa an wanke kwakwalwarsu wajen kare manyan arewa da kuma fusata a duk wani lamari da ya jibanci addini ko kabila amma banda na ci gaban al’ummar arewa. Wadannan manyan namu ba za su taba gyara kasar nan ba domin haka su ka tsara kuma su ke so a yi ta tafiya. Mu matasa ne ya kamata mu kawo canji amma abin takaici sakamakon hassada da son kai ya sa ba wani abu da zamu iya haduwa mu cimma. Matukar ba mu gane cewa manyan mu ba za su taba gyara kasar nan ba, kuma ba wanda zai zo daga waje ya gyara mu, wato wajibinmu ne mu tashi tsaye mu gyara da kanmu, idan ba mu yi ba hakika zamu mutu cikin takaici kuma mu bar wa yayanmu tsarin da ba za su iya samun rayuwa mai kyau ba. Ko dai mu tashi tsaye ko kuma mu ci gaba da zama bayi har abada.

 

Comments

Popular posts from this blog

ALAMUN TSINUWA...

LARABAWA: AL’ADA KO ADDINI?

Dabara Ta Rage Wa Mai Shiga Rijiya…