WATA 8 BAYAN KADDAMAR DA TASHAR RUWA TA BARO
Yau
kimanin watanni takwas kenan (wato tun January 2019) da shugaba Buhari ya
kaddamar da tashar jirgin ruwa ta Baro. Wannan tasha ta samo asali tun lokacin
turawan mulkin mallaka da su ka zabi garin Baro ya zama tashar jirgi saboda
kasancewar ta a tsawon kilomita 650km tun daga bakin teku a kan kogin Kwara, ba
wajen da ke da gabar ruwa mai tsandauri da zata iya jurar shige da fice na
jirage da sauke kaya kamar ta Baro ba. Tun a shekarar 1911, lokacin turawa aka
hada garin Baro da layin jirgin kasa wanda ya taso daga Kano domin jigilar
kayayyaki, musammam amfani gona na auduga da gyada a wancan lokaci. Amma saboda
rashin tsari da hangen nesa irin namu ya kasance sannu a hankali sakamakon
daina noman gyada da auduga a arewa, sai a ka yi watsi da wannan layi na dogo,
kuma ita ma tashar ta mace murus.
Wannan
tasha ta Baro ta na da alaka da shugaba Buhari kasancewar a lokacin da ya ke
rike da hukumar PTF su ne suka tsara yadda za’a sake gina wannan tasha ta zama
ta zamani. Gwamnatoci a baya, musamman ta Abacha da Yar’Adua sun yi yinkurin
yashe kogin kwara tun daga Warri zuwa Baro domin samun damar jiragen daukar
kaya su rika isowa har Baro. Yunkurin bai kai ga nasara ba har lokacin Jonathan
wanda ya ware Naira Biliyan 47 kuma a ka sakar wa ‘yan kwangila hudu kimanin
Biliyan 34 domin aiwatar da wannan aiki. A karshe dai an wayi gari babu kudin
kuma ba’a yi aikin ba. Gwamanatin Buhari ta farfado da maganar yashe kogin da
kuma gina wannan tasha, inda ministan Sufuri, Amaechi, ya rika cika bakin cewa
gwamnatin Jonathan ta wawashe Naira Biliyan 47 kuma ba’a ga komai a kasa ba don
haka su za su yi amfani da hukumar da ke kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA)
wajen yashe kogin a kan Naira Miliyan Dari kacal. Wani bincike da jaridar Daily
Trust ta yi game da wannan aiki ya nuna cewa har yanzu dai ba ta sake zani ba
game da yashe kogin Kwara domin dai a fadar wani injiniya na ruwa Abdullahi
Makujeri cewa ya yi “A ka’ida ana bukatar zurfin da ya kai mita 8.5 zuwa 10.5
yadda manyan jirage za su iya bi yadda za su lodawa kananan jiragen kaya domin
isa gaba” to amma a yau zurfin tashar Baro bai karasa mafi karanci na mita 2.5
da ake bukata ba. Don haka duk wanda ya ce a yau manayan jirage za su iya isa
tashar Baro ya na yin yaudara ce irin ta siyasa. Shekaru takwas ke nan da ake cewa
an yi yasar wajen, wadda a ka’ida ko da an yi, ana bukatar bibiyar yasar duk
bayan shekaru biyu wanda ba’a taba yi ba.
Wani
muhimmin al’amari game da aikin wannan tasha shine na maganar wutar lantarki,
domin babu yadda za’a yi a gudanar da al’amura na wannan tasha idan muka yi
la’akari da manyan injuna na dagawa da daukar kaya da ma’aikata da ofisoshi da
ake bukata idan babu wutar lantarki. Abin mamaki shine har yanzu garin Baro
ba’a hada shi da layin wuta na kasa ba. Tasha ce wadda za ta kunshi kusan ilahirin
bangarorin ma’aikata na tsaro, yan sanda, sojoji, hukumar shige da fice da ta
baki da sauransu domin tasha ce tamkar filin jirgin sama ko ta jirgin ruwa.
Idan ba wutar lantarki ta yaya aiki zai iya wanzuwa a wannan tasha?
A
daya hannun kuma, ita kan ta tashar ta Baro, gwamnatin Jonathan ta bada
kwangilar gina ta a kan Naira Biliyan 5.8 a shekarar 2012, abinda shi ma ya
zama labari. Zuwan Buhari ya farfado da maganar kwangilar gina tashar kuma an
kama aiki domin ganin an samar da gabar tasha mai tsawon mita 150 da kuma wajen
sauke kaya mai fadin murabbain mita 7000 da kuma wajen tsayawar jirage mai
fadin murabba’in mita 3,600. A farkon watan Janairu na wannan shekara shugaba
Buhari da ‘yan tawagarsa sun sauka a garin Baro a jiragen Helikwafta domin kaddamar
da wannan tasha, sakamakon cewa babu wata hanyar mota ko jirgin kasa
ingantacciya da za su iya bi domin isa garin Baro. Hanya mai tsawon kilomita 55
da ta ratsa garuruwan Baro-Katcha-Agaie da kuma ta Baro-Muye wadda ke haduwa da
garin Gegu da ke kan babbar hanyar Abuja-Lokoja, dukkansu ba za su iya biyuwa
ba. Ita hanyar Baro-Katcha-Agaie gwamantin Yar’Adua a kokarinta na farfado da
wannan tasha ta bada aikin gina wannan hanya tun a shekarar 2009 amma daga baya
a shekarar 2012 sai Gwamnatin Jonathan ta soke kwangilar bisa hujjar cewa dan
kwangilar ya kasa yin aikin yadda ya kamata. Amma daf da zaben 2015, sai
gwamnatin ta Jonathan ta sake bada kwangilar wannan titi ga wani kamfanin India
a kan kudi Naira Biliyan 17.5 da yarjejinar za’a kammala aikin a watanni sha
biyu. Da Buhari ya ci zabe, an saki wani kaso na kudin aikin wannan hanya amma
sakamakon kasa ci gaba da bayar da kudaden aikin wannan hanya, har yanzu bai fi
kilomita goma ba cikin abinda aka kammala, dalilin da ya sa tawagar shugaba
Buhari ta sama su ka iya isa Baro a watan Janairu lokacin kaddamar da tashar.
Sassa na wannan hanya, musamman tsakanin Katcha da Baro a lokacin damina ba ya
biyuwa sakamakon cabi da kwazazzabai, sannan su kansu gadojin da ke wannan
hanya sun fara gazawa domin wasu tun na zamanin turawa ne. Haka abin ya ke a
sashen hanyar Baro-Muye-Gegu wadda ke hada garin Baro da sashen kudancin kasar
nan.
Wani
tsohon soja wanda jaridar Daily Trust ta yi hira da shi ya ce “Tsawon watanni
takwas da kaddamar da wannan tasha babu wani jirgi ko da guda da ya iso tashar
Baro” inda ya ci gaba da cewa “Ta yaya jirgi zai zo tunda babu kayan aiki a
wurin wanda zai bada damar hakan?” A tashar kawo yanzu babu wasu jami’an shige
da fice da ke wajen. Wani mai gadi ya ce kafin zuwan shugaban kasa an je an yi
fentin katangar wajen an saka wayoyi masu tsini na tsaro a kai. Shi kan sa
kamfanin First Index Nigeria Limited wanda aka bawa kwangilar kula da manyan
kugiyoyi na daukan kaya sai da ya koka a karshen shekarar 2018 saboda motar da
ta dauko kayan da ake gaggawar su isa garin Baro kafin zuwan shugaban kasa, ta
kafe a kan hanya kafin ta isa, sai da hukumar kula da hanyoyin ruwa NIWA ta sa
aka je a ka yi aikin hanya kafin a samu wannan mota ta isa Baro da karafunan da
aka nuna wa duniya kamar tashar ta kankama.
A bayyane ya ke cewa
wannan gwamnati, ta yi amfani da wannan aikin na Baro domin kamfe na siyasa
kamar yadda sauran gwamnatoci a baya su ke yi. Kuma abin tambaya anan shine
idan wannan gwamnati tsawon shekaru biyar ba ta iya kamala wannan aiki ba, kuma
bayan watanni takwas da kaddamar da tashar da aka yi na yaudara, ba tare da an
ci gaba da maganar hada garin Baro da wutar lantarki ba, ko gyara hanyoyi biyu
da su ka hada arewaci da kudancin kasar nan da tashar ba, sannan shi ma hanyar
jirgin kasan ba’a kammala shi ba ballantana yashe kogin daga matsayinsa na kasa
da mita 2.5 a yanzu ya kai akalla mita 8.5, shin duk wadannan za su iya samuwa
a sauran shekaru uku da su ka rage wa wannan gwamnatin?

Comments
Post a Comment