YADDA MAJALISA TA KASSARA KASAFIN KUDI NA 2018
A tarihin Nigeria ba’a taba samun gwamnati da ta karbi mulki cikin mawuyacin halin tattalin arziki da tsaro irin lokacin da wannan gwamnati ta shigo ba, domin hatta albashin ma’aikata sai an ci bashi ake iya biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya, su kuwa jihohi da damansu ba sa iya biyan albashin tsawon watanni. Kasar ta fada cikin koma bayan tattalin arziki mafi muni a tarihi, amma cikin shekaru biyu gwamnatin Buhari ta juya akalar abubuwa yadda aka fice daga koma bayan tattalin arziki sannan hukumomi irin su kwastam da Jamb su ka kafa tarihin karbar haraji mafi tsoka a tarihinsu.
A wannan shekara ta 2018 an yi kasafin kudi mafi yawa tun da aka kafa Nigeria, domin ya kai kimanin Tirilian 8 da doriya. Dalilin wannan kuwa shine saboda man fetur ya farfado a kasuwar duniya sannan gwamnati ta bude kafofin tattalin arziki kama daga noma, haraji da ma’adinai yadda kudaden shiga su ka habaka fiye da yadda aka taba gani a baya.
Shi kasafin kudi karkashin kundin tsarin mulki, bangaren zartarwa ke da ikon tsara shi da aiwatar da shi, su kuma majalisa na da hakkin duba shi da sahalewa sashen zartarwa domin su aiwatar. Ba’a taba samun lokacin da kasafin kudi ya dade a hannun ‘yan majalisa ba a tarihi irin wannan shekara domin sai da ya dauki tsawon wata bakwai a hannunsu su na jan kafa. Ina dalilin hakan? A bayyane ya ke cewa ‘yan majalisa na kokarin yi wa gwamnati zagon kasa ne saboda irin ayyukan alherin da aka tsara a cikin kasafin, su kuma ganin shekarar zabe ta zo ba sa son gwamnati ta yi nasarar aiwatarwa domin zai ba ta damar cin zabe. A tarihin majalisu a duniya ban taba ganin muguwar majalisa irin wannan majalisa ta 8 a Nigeria ba, amma dai dama kowa ya san cewa kowa ya sayi kwando ya san zai subar da ruwa.
Duk mai bin tarihin majalisa a Nigeria ya kwana da sanin cewa tun daga 1999 zuwa yau, a duk lokacin da ka ga majalisa na tada jijiyar wuya, to ka tabbatar abu ne da ya shafi ‘yan majalisun, idan banda hana rantsuwa yunkurin da su ka yi a 2006 wajen dakile tazarcen Obasanjo. Mun ga yadda su ka rika fada da jami’an gwamnati irinsu Nasiru El-Rufai, Femi Fani Kayode (a lokacin ya na dan gani-kashe-ni na Obasanjo) da Sarkin Kano na yanzu Sunusi Lamido Sunusi, da kuma a baya bayan nan irinsu Hamid Ali, Ibrahim Idris kai har ma da ‘yan uwansu da su ka bijire musu irinsu Ali Ndume. Kwanan nan mun ga yadda su ka yi barazanar tsige Buhari saboda ana zargin Bukola da manyan laifuka.
Kasafin kudi na wannan shekara 2018, ya tabbatar wa duk wani mai hankali cewa ‘yan Nigeria ba su da wani makiyi wanda ya wuce ‘yan majalisar mu. Ga dalilai na; Na farko dai shine cewa Bukola Saraki a matsayin mutum na uku a iko a tsarin tafiyar da mulkin kasar nan, wanda kuma ya fito daga sashen tsakiyar Nigeria, ya shugabanci tantance kasafin kudi wanda ya cutar da al’ummarsa ta tsakiyar Nigeria kai tsaye, domin sun yanke kudin da aka ware na gina titin dogo da ya taso daga Itakpe zuwa Ajaokuta. Wannan aiki na cikin manyan ayyukan da wannan gwamnati ta sa a gaba domin ganin katafariyar ma’aikatar sarrafa karafa ta Ajaokuta ta kama aiki gadan gadan a watan December na wannan shekara. Mun ga yadda gidan talabijin na Aljazeera ya dauko rahoton aikin wannan wuri da nuna cewa komai yana tafiya yadda a karshen shekara za ta fara aiki, amma Bukola ya sa hannu wajen tsaikon wannan aiki. Sannan mataimakinsa, Ekweremadu shi ma ya yi wa ta sa shiyyar ta kudu maso gabas irin wannan manakisa ta hanyar yarda da zaftare kudin karasa ginin filin jirgin sama da ke garin Enugu daga Naira biliyan 2 zuwa Naira miliyan 500 kacal, wato kashi daya cikin 4, abinda zai hana kamala wannan aiki. Sannan kuma aikin mashahuriyar gadar nan ta kasar inyamurai, 2nd Niger Bridge, ganin cewa gwamnatocin baya sun kasa amma wannan gwamnati ta yi nisa da aikin, don haka ba sa son alherin ya sami jama’ar yankin don haka shi ma sun dakile shi. Babbar hanyar da ta hada Lagos da Ibadan wadda an ci karfin aikin ita ma sun dakile ta, hanyar da tun Obasanjo ake fitar da kudin gina ta. Shin wadannan da mu ke dauka shugabanninmu, Buhari su ka cuta ko kuwa al’ummomin da su ka basu damar wakiltar su?
Kwanakin baya mun ga yadda tsagerun Niger Delta su ka fara tada jijiyar wuya game da katafariyar jami’ar harkokin sufurin ruwa, Maritime University, wadda irinta ta ce tilo a nahiyar Afirka kuma shugaban kasa ya ji koken wadannan mutane ya sa ka ta cikin kasafin kudi amma sai gashi da sahalewar ‘yan majalisa na yankin irinsu Ben Bruce sun amince da zaftare kudin daga biliyan 5 zuwa biliyan 3, abinda tabbas zai kawo tsaiko wajen kafa harsashin wannan jami’a. Akasarin ‘yan majalisar nan rayuwarsu a Abuja ta ke amma sai gashi birnin tarayyar bai tsira daga manakisarsu ba wajen ganin sun zaftare Naira biliyan 7 da rabi cikin kudaden da ake son kammala hanyoyin jirgin kasa na cikin garin Abuja, saboda ba su za su amfana ba sai dai talakawa da ke zaune a wuraren.
Tun shigowar wannan gwamnati, ba’a fito da wani aiki mai mahimmanci wanda zai lashe kudi kamar aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila ba, za ta lashe kusan dala biliyan shida kuma idan aka kammala ta, za ta samar da wutar lantarki da ta kai Mega Watta 5000 zuwa 6000. Wannan tasha a arewa ta ke kuma arewacin Nigeria ne zai ci gajiyar ta sama da kowa, amma sai gashi shugabannin wakilanmu irinsu Yakubu Dogara da Alasan Ado Doguwa saboda ba sa kishin mu sun sahale da kawo wa wannan aiki tsaiko ta zaftare kudadensa. Abin ba a nan ya tsaya ba domin sashen lafiya shi ma ba su barshi a baya ba sanin cewa talakawa ke amfanarsa domin su a waje su ke zuwa asibiti. ‘Yan majalisa sun zaftare biliyan 7 da kusan rabi da za’a yi amfani wajen daga darajar wasu asibitoci.
Wani abin mai tsananin muni da tayar da hankali shine zaftare Naira biliyan 3 daga cikin kudaden da aka ware don samar da tsaro a makarantun sakandare 104 na gwamnatin tarayya (Federal Government Colleges) wadanda a kowacce jiha dake fadin kasar nan na da akalla makarantu biyu. Sannan wani rashin Imanin da majalisa ta nuna shine na cire Naira biliyan 5 daga cikin kudaden fansho na ma’aikata. Ya ilahi mutanen nan kuwa na tsoron Allah?
Haka nan sun ki yarda da wasu kudade kusan kimanin biliyan 4 na gina ofishin majalisar dinkin duniya, ofishin da a baya ‘yan Boko Haram su ka wargaza. Sun sahale da kashe Naira miliyan Dari kacal maimakon biliyan 4. A bayyane ya ke cewa yakin da su ke da wannan gwamnati har kimar mu a kasashen waje su ke son rusawa ganin yadda Baba ke da kima a duniya. Babban abin mamaki shine akwai kudade da aka ware na kimanin biliyan 14 da rabi domin gina rukunai na kasuwanci don shige da fice na kayayyaki kasashen waje da kuma kebabbun wuraren kasuwanci wadanda za su tallafawa tattalin arzikin kasar nan, sai gashi sun kwashe wannan kudi kuma su ka mayar da shi cikin asusun majalisa a bisa kari daga abinda aka ware musu. A fili ya ke cewa wadannan mutane yaki su ke da talakawan Nigeria domin ya ya zaka cire kudin raya kasa ka mayar da su aljihunka?
A takaice dai ‘yan majalisar nan sun zaftare kudade kimanin Naira biliyan 347 daga cikin manyan ayyuka da gwamnati ta tanada sun maye gurbinsu da ayyukan boge na kimanin biliyan 578, ayyukan boge ne tunda ba’a tsara su an tantance su ba, kuma bangaren zartawa bai san da su ba ballantana ma ya sahale musu (wato dai cushen da su ka saba sai sun yi shi). A wannan lokaci da wannan gwamnati ke kokarin rage kudaden da ake kashewa na yau da kullum da karkatar da su zuwa manyan ayyuka sai gashi sun kara kimanin biliyan 74 domin ayyukan yau da kullum a cikin kasafin kudi domin ma’aikata da ‘yan siyasa su wawashe su a ci gaba da barin talakawa na hamma.
Hakika lokaci ya yi da duk wani ‘dan Nigeria mai hankali zai farka daga barcinsa ya san cewa ba mu da wasu makiya a kasar nan a yanzu sama da masu wakiltar mu, domin an dade muna zabar su suna mai da mu wawaye su je Abuja su yi ta sharholiyarsu. Dole mu tashi tsaye mu kori ‘yan majalisar mu na yanzu domin ba su da wani amfani, kuma mu lalubo a cikinmu mutane masu kishin jama’a da tsoron Allah. Idan ba haka ba zamu ci gaba da zama a matsayin bayi a cikin kasarmu. Duk yadda Buhari ya kai da gaskiya wallahi ba zai cimma cikakkiyar nasara ba sai ya sami ‘yan majalisa masu kishin jama’ar su. Ya rage namu mu yi aiki da hankalinmu kuma mu yi amfani da makaminmu, wato kuri’armu.
Comments
Post a Comment