DUK WANDA YA SAYI RARIYA

Ina zaton idan na yi ta mahaukaci nace duk duniya babu wata kasa ko al’umma wadda ba ta dauki ran dan adam a bakin komai ba kamar Nigeria za’a iya yarda da ni ko da ban bada wata hujja ba. Amma dai ya kamata komai zaka fada ka kawo hujjoji. A tunani na, babban dalilin da ya sa kasar nan take cikin bala’in da take ciki shine jinin mutane da ake zubdawa ba tare da cewa yan kasar ko hukumominta su damu ba. Duk wata al’umma da ta san abinda ta ke yi hatta dabbobi ta na tashi tsayin daka wajen ganin ta kare rayukansu. Amma mu a Nigeria babu wani rai da yake da cikakken tsaro kuma idan aka kashe shi an kashe banza ko wanene don babu abinda za’a yi. Kwarai kuwa domin a kasar nan ne a bainar jama’a aka yi sanadiyar daya daga cikin gwarazan yan siyasa da basa tsoron kowa, wato Chuba Okadigbo amma babu abinda aka yi. Sannan an kashe ministan shari’a Bola Ige, kuma wanda ake zargi da hannu, Omisore, yana kurkuku aka zabe shi zuwa majilisar dattawa. Don Allah a wace kasar duniya ce za’a zabi wanda...